part.....67

794 38 30
                                    

💎💎💎💎
💎💎💎💎
💎💎💎
💎💎

*BIYAYYA*

*Story...writing*
By
*Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

Masoyana ina matuqar alfahari daku....masu comment, vote, like and share duk inatare daku...wad'anda banasamun damar mayar musu da amsa kuyi haquri kunji...amma kuna raina sosai.

Wannan shafin nakine, gaba d'aya littafin sadaukarwane gareki *Nana Khadija* ina alfahri dake sosai.

My mom kema ina alfahri dake arayuwata kin min komi inason ki sosai over.

*page....67*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

---------Hakan yayi dai-dai da shigowar Fiddausee ajin, ganin abinda ke faruwane yasanyata matsawa inda Dijen take tare da sa hannu dan 'ban'bare hannunta akan wuyan zuby d'in amma hakan ya faskara. Duk da tason tabbas sune basu da gaskiya sune suka takaleta dan tasan halin 'yar uwartata sosai.

Da qyar tasamu ta 'ban'bare hannun nata daga kan wuyan zuby, zuby wacce tasha shaqa sosai take zazzare da idanuwanta waje dan tashaqu ba qarya, kallon Dije take ciki da borin kunya tana wani karkad'a jiki tace" wllh kinci albarkacin wannan yarinyar amma da saina......" bata qarasaba Dije tayo kanta ai habawa qafa menaci banbakiba takye ta zura da gudu sai waje.

Habawa mai 'yan aji zasuyi inba dariyaba.Fiddausee ce ta kallesu tace" wai meyafaru ne?"

Yarinyar da d'azu tai magana itace yanxunma ta bud'e baki tace" yaya , yaya zuby ce da tsokana wllh muna zaune qalau tazo tafara gayamata magana, harda zagin babanta, shine ita kuma taga bazata iyaba ta rama"

Fiddausee ta kalli yarinyar tare da kallon Dije tace" yayi kyau, ai nasan yanzu bata qaraba ko"

Yarinyar datai magana tace" wllh kam yaya"

Fiddausee ce ta juya tana mai fuskantar Dije tace" kiyi haquri halin zubaida kenan, rashin girmama d'an Adam, muma haka muke fama da ita dan ta d'au qarya ta d'orawa kanta"

Dije tace" kiyi haquri nibanma san cewa 'yar uwarki bace da hakan bata faruba"

Fiddausee tace" no kada ki dubi wannan, ai nasan itace da laifi, qanwatace amma uba d'aya muke uwa kowa da tasa, mu bakwai ne a gidanmu, nice ta biyar sai ita sai wannan kausar kenan" ta qarasa tana nuna yarinyar datai magana d'azu.

Dije tace " lallai ashe kuna da yawa"

Fiddausee ta murmusa kana tace" ehh amma ai bawani sosai ba, kufa ko nawane?"

Dije tace" ni kad'aice agidan mu babana da mamata sun rasu, sai kakata da qanin babana"

Fiddausee ta rausayar dakai kana tace" ayya sorry sister, Allah ya jiqansu da gafara ya musu rahma"

Dije ta amsa da " ameen"

..........
Alhj.Shamsudden shine mahaifinsu Fiddausee shahararran d'an siyaysane sosai dan yanzu shine ke riqe da muqamin deputy governor, ayanzu yana saran zai zama governor nan gaba, wannan yasa zubaida da 'yar uwarta mai suna Rahma suke tata rashin mutuncinsu basso san harka da 'ya'yan talakawa ko kad'an sunqi jininsa sa'banin su Fiddausee da ragowar 'ya'yan.

Hajiya Mariya itace mahaifiyarsu Fiddausee 'ya'yanta biyar Hisham shine babban d'anta kuma shine na fari akaf gidan, sai Auwal, Mariya mai sunanta amma suna cemata momi, Fiddausee sannan Asma'u wacca itace auta a d'akinsu.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now