BIYAYYAH....

740 29 0
                                    


💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

 

*Story...writing*

By

   *Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃


*page....33-34*


  *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


-------------Sosai sukai ba'kin ciki da hakan, musamman ma Hindatu, tabbas tasan wannan ba 'karamin zaluncine aka musuba, taso su d'aukaka 'kara malam Adam ya hanata, Dan yanajin bazasu samu wata dama ba *" nikam nace da dai ka bari ta gwada"* kuma insha Allahu sai Allah ya bayyana gaskiya.

Haka suka d'au ha'kuri da juriya suka sawa zuciyarsu, amma duk 'karshen sati d'aya zuwa biyu sai sunje duba malam Adam.kuma yana matu'kar farin ciki da hakan.haka rayuwar su ta kasance har tsawon wata uku, yayinda kasuwancin malam Adam ya tsaya, ma'aikatarsu ma ayanzun ta sallameshi domin tace " ba zata zauna da mai ha intar 'kasaba, da kuma safarar muyagun 'kwayoyi, wannan al'amarin da ya faru ya d'ad'a je fasu cikin wani hali, kud'in da ya d'an tara baban Hindatu ya fara musu wata sana'ar dasu, dan provision ya bud'e musu, aka zuba kaya, sosai suke tafiya kuma ba laifi ana samun kaya, Dan har oder yanayi. Ba laifi suna samun ciniki sosai.haka rayuwa tai ta tafiya yau da dad'i gobe babu.

  Kamar ko yaushe ko na yin sabgar gabanshi, masu zaman gida nayi masu fita kasuwa nayi....zaune suke da babanta suna ta'ba hira yayin da mamanta ke samusu baki jefe-jefe, wayar sace ta hau ringing batare da jin kirin komiba ya d'aga tare da sallama.

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shine abinda naji ya ambata. gaba d'aya nsu shi suke kalllo, nunfaahi yaja tare da sharce gumin da ya keto masa.

Hindatu ce tayi 'karfin halin cewa "baba lafiya, meyake faruwa, kasanar samu, koma meye zamuyi ha'kuri n hakan, wannan 'kaddarar mice"

Suke nunfashi yai yace " Hindatu kiyi ha'kuri, tabbas ko wane bawa yana tare da yasa 'kaddararsa, lallai ba makawa kowa akwai yasa jarrabawar,kiyi ha'kuri Hindatu, Allah shiga fimu San kowane bawa, hakan yasa yake da IKON kar'bars aakowane lokaci, yanzunma hakan ce ta kasance domin kwavya amshe bawansa malam Adam, kiyi ha'kuri, Allah zai baki......"

Wata iriyar shid'ewa tai kafin nun faahinta ya tsaya, da gudu sokayo kanta suna jijjagata, "please Hindatu kitashi Dan Allah" fita sukaivda ita zuwa asibiti, suna shiga aka kar'beta zuwa emergency.shikuma baban Nata ya wuce can prison d'in Dan amso gawarsa, tabbas lallai wannan ba'karamin rashin hankali suke cikiba,amma ya zasuyi haka Allah ya hukunta, kodayaje sai da ma'aikatan ma suka shaida mai" lafiya 'kalau ya kwana da safe kawai aka ga yatashi da wani irin train, nan aka garzaya dashi asibiti, amma ko kafin su isa ya mutu" Nan dai aka mai sitira aka kaishi gidan shi na gaskiya.koda Hindatu ta farfado ba abinda take ambata sai malam Adam d'in ta, saida likitan d'aya amsheta ya mata allurar bacci.yayin da can gidansu aka kama zaman makoki.

Bayan sati d'aya da rayuwar, komi ya sauya cike kuwa harda sauyawar Hindatu, Dan bata cewa komi, ko gaisuwa akazo yimata saidai ta kalle mutum kawai, babanta har ya fara tunanin Nidai tayi loosing memory d'inta ne.yayinda su Abdallah ke ta tambayar Abbansu, su akaisu wajensu, saidai maman Hindatu ta musu dabara tace yayi tafiya, shine ake samun Kansu.haka rayuwa tacigaba da tafiya , yayinda babanta ya maida hankali kan kasuwancin daya kafa musu, kuma alhamdulillah ana samu sosai.

.........Bayan wata biyu , Hindatu ce naga ta'ba ta daman had'e-had'en kaya ajaka, " tabbas tasan abinda zatai bai davkyau kuma iyayenta sukaji abinda take shirin aikatawa bazasuji dad'i ba amma ba yadda zatai ,muddin zata cigaba da zama an an garin to bazata ta'ba mantawa da abinda take so arayuwarta ba,ba yadda zatai dolane tayibabinda tayi niyya" ta'ba gama wannan tunanin ta mi'ke tare da sa'ba Auwal a baya ta d'au Abdallah aka fad'arta, taja trolley d'in Nata data Sanya kayan Nata aciki.dayake farin bai gama washe waba, hakan yabata damar fita daga gidan batare da kowa ya gantaba, ahaka har ta isa tashar garin Abuja....."Kano...kano".....shine abinda taji ana fad'a, "Kano " ta maimata a zuciyarta, take taji banason bin ayarin su, " zanje kano d'in nima" ta fad'awa driven, gidan gaba ya bud'emata yashiga, dama mutum d'aya ake jira agama Lodi, Dan haka ta'ba shiga shima driver yashiga ya tada mota...."asauka lafiya"

Can gidan su kuma koda mamanta ta tashi, d'akin ta ta le'ka Dan taji shiru, domin tasan Hindatu da rashin wuri, amma yau tajita shiru. tana shiga taga wayam bakowa a d'akin, toilet ta le'ka nanma wayam, cikin rashin hankali ta fito tare da 'kwalawa mijin nata ta kira.

Fitowa yai yana fad'in " lafiya kuwa, kike ta faman d'aga sauri haka?"

"inafa lafiya malam, naga hindatu ba Sam, bata gidan nan wllh"

"kamar ya baki ganta ba, haba dai kema to ita yarinyacebda zata 'bata?"

"Malam da gaske nakema fa, har su Abdallah Nasa nan fa" ta fad'a cikin rud'ani.

"Innalillahi" ya ambata, kafin su hau bin cike agidan Kodak wani wajen yashiga, har gidan ta suka he batanan, wasa-wasa har gabanin magrib suna Neman Hindatu amma name kama da ita ma.hankalinsu yayi matu'kar tashi sosai, "wannan wace irin rayuwa ce, yavAllah kaki yayemana Hindatu mu aduk inda take, ameen" .


..............'Bagaren Hindatu kuwa koda suka shigo farin kano, sai ido ya raina fata, domin dai gata a kano amma bata San ina zata ba, gashi duk ansauke kowa.

"Rimin gado 'kauyen 'butu-'butu, zaka Kaine" taji wani mutum ya fad'a. Cikin sauri itama tace "nima haka" nan ya fad'a musu kud'in mortar suka hau, koda aka sauke wannan mutumin sai itama tace anan zata sauka, ata'kaica dai duk inda wannan bawan Allahn yasa 'kafa itama sai yasa, batare da tayi tunanin koshi d'in wayeba, ahaka har ya iso 'kofar gidan shi, ganin zai shiga yasa ta yin magana tar da fad'in "bawan Allah Dan Allah ka temakeni"

Juyo wayai ya kalleta yace " muje ciki" yana gama fad'ar haka suka shige cikin gidan, koda suka shiga wata mata ta Tatar zaune kan ta barma tana kad'i.

" ah lake maraba da zuwa, sannnunka, an dawo lafiya" ta fad'a cike da murna.

"lafiya lau sa'ade, bamu tabarma, bani kad'aineba" sai alokacin takai duabnta ga Hindatu, "maraba marabanku, sannunku da zuwa"

Koda suka nutsu ya hau tambyarta daga ina take, me tashigoyi farin kano?"

Nan ta gayamai komi daya faru da ita, harta shawarar data yanke makanta sai suka tausya mata matu'kar, saidai malam Tsallah ya muna mata kuskuren ta nayin hakan, gashi shima daman wata ziyarace ta kaishi can bare yace in ya koma yatafi da ita Koran ta koma wajen iyayenta, nan dai tai ta kuka, tare da nadamar abinda ta aikata, sai dai ta ro'kesu "akan su barta ta zauna tare dasu" " nan sukai na'am da ita, tare da ware mata d'aki guda agidan.

Satin su guda suna cigiyar Hindatu amma basu ganta ba, hakan yabasu tabbacin cewa lallai tayi Mesa dasu, saidai kullum suna tayata da addu'ar fad'awa hannu na gari.




..........Bayan shekara goma sha biyu, komi yana tafiya dai-dai, yayin dasu Abdallah suka dad'a tasawa domin ayanzu shekara Abdallah goma sha hud'u, yayin da Auwal ke da shekara 12 da rabi.nan malam Tsallah yafara fita da Abdallah wajen sana'arsa, kuma sosai yatsaya ya maida hankali akan hakan, suna iyayen sunyi farin ciki da hakan.

Comment and
Share....

*Miss Gentle ta kuce......*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now