biyayya....62-63

820 43 1
                                    

💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
💎💎💎
💎💎

*BIYAYYA*

*Story...writing*
By
*Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

Masoyana banson dame zan sakamukuba saidai nace" ubangiji ya biyaku da gidan aljanna...yabar ZUMUNCI"

*page....62-63*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

--------Jummai ta kalli Dije tace" qawalli naga kin qara kyau alqur'an kamar bakeba"

Dije ta harareta tace" ko kuma abinda yafi kyau d'inba, ke wllh kin fiya shirme"

Jummai tace" au nice mai shirman, yanzu ba wannan ba wai nikam ina ya Imran d'in ki? "

Dije ta murmusa tace" yananan lafiya jiyama sukazo shida mommy d'insa, ai yakan zuwa balaifi"

Jummai tace" lallai kam Allah yasa muhad'u koma gaisa ai"

Dije tace" ehh zaku iya had'uwa dashi, inma baizoba zansa auta takirashi sai yazo"

Jummai ta wangale baki tace" kai amma da kin kyauta wllh"

Nan Dije tashiga bata labarin makarantar da yace zaisanyata"

Aikam Jummai baqaramin dad'i tajiba, sai taji inama harda ita itama taqaru da wani abin, sosai ta tayata murna akan hakan.

Nan itama take gayamata yadda sukai da Ramai.

Falsh back

Sanda Dije zasu rabu da Jummai tabar mata saqon takaiwa Ramai kud'inta, takuma riqar mata ita akan tafayemata itama badason ranta tamata hakaba, wai dan ta koyamata hankaline"

Koda Jummai ta kaiwa Rama kud'in baqaramin artabu sukaiba, dan harda su kawu saida suka shiga zancan, tare da neman afuwarta akan yadda abun yafaru.

Jummai nagayamata artabun da akai Dije tai salle tace" shegiya aida nasanima ban maida mata da kud'inba"

Jummai tace" ah gwaradai da aka maida kinsanfa tana da haqqi dai tubda natane banamu baneba"

Dije tace" hakane ai shikkenan"

Sai wajen azahar suka sakko qasa nan suka tadda auta tadawo dan taje wajen saloon agyaramata kai.nanfa auta akasami abinyi duk su ukun suka zauna afalon aka dasa sabuwar hira.

Saida mom tamusu dagaske sannan suka tashi sukai sallah, koda suka idarma kimawa sukai kan hirartasu.sai da aka gama abinci sannan suka zauna ci.

Kawu kam dad yaiwa bayanin komi na tafiyarsu da Dije, sosai dad yaji dad'i koba komibai danginta zataje gani, nan shima yake shaidamai" ai Ashraf d'inma tafiya zaiyi ta tsawon wata shida"

Nan kawu yamasa addu'a tare da fatan samun nasara, koda dad yaiwa Ashraf magana bai ce komiba saidai yai musu fatan addu'ar dawowa lafiya" dad kam yaji dad'i sosai hakama kawu.

Mom kwa dataji labarin hakan itama taji dad'i amma sai ta roqi subarsu suyi kwana biyu Ashraf zai kawusu.

Bayadda Kawu ya iya haka yabarsu dan yanajin kunyar yawatsawa mom qasa a ido game da roqon datamai.sabda zaitafi dije jitai kamar tavishi taga Iyan ta.su dad kam sun hadamai goma ta arziqi, danma da qyar ya amsa.

Bayan tafiyar kawune dad yakira Dije yake mata bayanin komi, habawa zokaga murna wajen Dije saidai ba'abinda yafi farantamata rai irin yadda taji Ashraf zaiyi tafiya jitake inama yatafi gaba daya.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now