biyayya.....78

794 43 26
                                    

*BIYAYYA*


Writing by
        *Maryam Abduul*

Wattpad@maryamad856.


💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

*Page......78*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

---------------------Shirye-shirye ake sosai yayinda kwanaki nata matsowa dan yanzu ya rage sauran wata guda yayinda su dije ke qoqarin zana jarrabawar zangon karatu na farko.



Ashraf kam duk yabi yashiga damuwa dan sosai yake jinsa wani iri ya kuma rasa dalili, wanda har yanzu yaqi yadda dacewar wai yana missing din abincinta.sau tari yakanyi qoqarin san yaga yaci wani abun amma ko kadan bai jin dad'in sa.wannan yasa ya yada duk wata cima.



A 'bangaren Imran ma har yanzu baisa ka bi takansaba dan yanaso yaga yagano gaskiyar al'amuran, yanaso ace shima yakoma hanya ta gaskiya, wannan dalilin ne yasa shi kauda idinsa daga kan duk wani al'amari nasa.

Duk dacewa yaga kusan wata guda bai ganim shi a office amma hakan bai damu idanma wani abun ne inya kirashi yaji, amma shikam bazai kiraba yaje can ya qarata.







........Su Dije an fara jarrabawa, yayinda bikin auta ya rage saura sati guda, nan fa aka qara bada wuta wajen gyare-gyaren da zasuyi, duk wani gyaran amarya da za'ai sai anyiwa dije itama, hakan baqaramin da fito da kyanta yai ba.

Itama Jummai ba'a barta abaya ba, dan itama sosai ta dage wajen gyara jikinta dan fito danata kyan da Allah ya bata.






*********

Biki bidiri bured'e, yaune aka soma shagalin bikin auta, duk da bawani abubuwa za'ai da yawaba dan event uku kawai akace za'ayi.

Su dije, Jummai da kuma fiddausee sune amara qirjin biki, kai sai rawa yake.

Yau za'ai dinner, wanka sosai suka d'auka, wanda Hafsy ce taja ragamar kwalliyar ita tai musu, masha Allah dukkanau sunyi kyau.yayinda sukai anko iri daya, duk dogwayen riguna.abin gwanin sha'awa.


Imran dai dayaga shiru ba labarin Ashraf shine yaje dakansa har gidan danjin lafiya, dan ko mom bata bi takansa shiyasa batama son wai yana zuwaba ko a'a, ga kuma hidindimun biki.

Auta kam duk tabi tadamu na rashin ganin yayanta wannan yasa ta kira Imran ta tambayeshi ko lafiya?"

Sine ma yake cemata" suna tare zasu zo wajen ai" sosai taji dad'in hakan.


Imran kam koda yaje wajen Ashraf d'in lafiya lau ya tadda shi saidai duk yabi ya rame yayi baqi dashi, kallonsa yai kana yace" yadai malam baganka soo cool koda wani abunda ya farune?"

Ashraf ya galla mai harara kan yace" bansaniba, inma mutuwane ina ruwanka"

Imran yace" yanzu dai duk ba wannan ba kataso muje nace da mom zamuje wajen dinner d'in "

Ashraf yace" ba inda zani karabu dani dan Allah"

Imran yai murmushi kan yace" na rantse da Allah sai kaje, ka tashi ka shirya malam, ko kanaso ka dad'a bata ran su mom din ne bayan abinda ka aikata"

Jin hakan yasashi yin tsaki tare da miqewa ya fad'a toilet, Imran yace" oho dai sai kaje"

Wayar shi ya d'auka tare da tura saqo, sannan ya miqe ya dauka mai kayan da zai sanya.yana fitowa ya fara shiryawa, sai da yabata lokaci sosai wajen shirin kan yagama.sannan suka nufi wajen dinner d'in.








BIYAYYAHWhere stories live. Discover now