Biyayyah.....!

678 16 0
                                    

💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
💎💎💎
💎💎
*BIYYYAH*

*Story...writing*
By
*Maryam Abdul*

Wattpad:@maryamad856

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃

Da bazarmu writers ass. Fatan alkhairi ga kowa da kowa.... Ku kasance cikin farin ciki da annushuwa na har abada.

Masu comment and Vote ina matu'kar godiya gareku...Allah i bar zumunci...ameen.

*page...53-54*

Bismillahir Rahmanir Raheem.

--------Dije ta kalli Imran tace" amma ya Imran kana ganin ba matsala inaso zan koya amma inaga kamar mom da wannan mutumin bazasu amince ba?"

Imran yai murmushi kana yace" waye haka kuma 'kanwata?"

Turo baki tai tace" mugun nan mana haba ya Imran ai yakamata acema ka gane basai nayi dalla-dalla ba"

Imran yace" to to ni taya zan gane da wa kike alhalin bansan waye shi d'in haka ba"

Ta 'Kara turo baki tace" Wanda ya ran'kwashi d'azu fa"

Habawa me Imran zaiyi inba dariya ba ya kalleta yace" wai da Ashraf kike? tab lallai kamar akunnensa kamar yaji shi kike cewa mugu?"

Marairai cewa tai tace" haba yayana kar muyi haka dakai fa, ni da wasa nakefa"

Imran yace" oho dai amma kin fad'a ai ko?"

" To kayi ha'kuri bazan 'karaba" Dije ta fad'a.

Imran yace" shikkenan naji bazan fad'a ba, maganar bari kuma indai zaki maida hankali akai kada ki damu baki da matsala ni zanyi magana da mom"

" Shikkenan na gode ya Imran" Dije ta fad'a .

Imran yasa kya cewa" d'azu naga kamar kinason keyi magana ko? Ashraf ya katseki, me zaki ce?"

"Lah bakomi fa yaya na" ta ''karasa cike da washe baki.

Imran ya girgiza kai yace" kin tabba ta ba wata matsalar inda akwai ki gayan 'kanwata kar ki 'boyen komi kinji"

"Allah babu , inda akwai ma ai zan fad'a maka" ta fad'a.

" Tam shikkenan, ni zan gudu"

" Kai da wuri yaya kofa 10:00pm batai ba"

" Habawa ai na dad'e ke kuwa, nasan mom nacan tana jirana Dan ban gaya mata ba"

" Shikkenan ka gaida gida da mom, zanzo ai"

Imran yace" zasu ji, sai na ganki to inda gaske"

"Allah da gaske nake zamu zo nida auta, zan tambaye mom kuma nasan bazata hanaba"

"To ai shikkenan ba damuwa ni na wuce"

Sai da yaiwa mom sallama sannan ya fad'a motarsa tare da bata wuta.ita kam Dije part d'inta ta koma ta hau shirin kwanciya Dan jinta take duk a gajiye. *(N ikam nace" ba dole ba kin shiga kitchen")*



Ashraf kwa ba shi ya dawo gidan ba sai wajen sha d'aya, direct d'akin ta ya wuce tana kwance tana ta sharar baccinta, gefan filon da take kai ya shiga bubbugawa.firgit ta farka da yake Dijen dama ba mai nauyin bacci ceba.

Kallon ta yai yace" oya tasu kisaman a d'akina" yana gama fad'a ya juya.

Mi'ka tai kafin tace" nidai kam na shiga uku wllh"

BIYAYYAHजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें