biyayya....77

767 42 18
                                    

*BIYAYYA*


Writing by
       *Maryam Abduul*

Wattpad@maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

*Page......77*

---------------Wani kallo Imran yamasa kan yace" koma dai menene to bazaka ciba, na fahimce duk randa kai ido hud'u da abincinta sai ka zuzuce, wai meye sirrin ne?"

Ashraf yace" nidai dan Allah kabani baza ka gane duk abinda zan fad'a maka bane"

Imran ya tura mai da flask din gabansa kan yace" yo to ni ina zan fahimta, ai banaaon ma na fahimta d'in, kai dai ci abincinka"

Batare da ya kulashiba ya hau cin kayansa, tas ya cinyeshi batare daya rage ko kad'an ba.

Imran ya kalleshi yace" amma kaban mamaki fa wannan abincin duk kai kad'ai ka cinyeshi?"

Ashraf yai mutmushi kan yace" kai kasan yaushe rabona danaci abincima wllh duk abinda zanci sai naji sam bai kai dad'in wanda takeyiba na kuma rasa menene dalilin hakan, dan Allah ka dinga amso min kana kawon, dan kaga bana samu yanzu inaci"

Imran yace" wa ni ba daniba, salon mom takamani ina d'an waken zagaye, wannama canai tamin zanzo nace anan ban karyaba, kuma gashi kacinye yanzu ni yazanyi?"

Ashraf yace" ka bada asiya ma awaje"

Imran yace" lallai sabida kai ka cika cikin ka ko, yanzu dai meyasa baka iya cin abincin kowa?"

Ashraf ya dan shafa cikinsa kan yace" wllh ni kaina ban saniba, amma banajin ko wanne dandano in ba nataba, wai ma daman haka ta iya girki?"

Imran yace" daman ai kai kake mata kallon haka-haka amma wllh yarinyar nan ba nan badai, yakamata ka nutsu kai nazari ka amshe matarka hannu bibbiyu dan Allah Ashraf ka zubda makaman yaqinka na tabbata su dad zasu ji dad'in hakan"

Ashraf yace" inason yin hakan amma abu daya zai sani yin haka abincinta, wllh badan shiba da banga abinda zaisa na yarda ma ta dawo gidanaba, dan banajin sonta ko kadan bakuma zan sotaba"

Imran yace" qarya kake, kana sonta"

Ashraf yace" qaryane ni ba macen da nakeso har yanzu nasha gayama ba'a haifetaba"

Imran yace" wllh ko kaso ko kaqi kanason khadija, duk mutumin da zaice yana son wani abu na wani ko yana jin dadinsa to lalli ba shakka shima wannan mutumin anasonshi kuma ana jin dadin zama dashi"

"Yanzu inaso ka gaya min abinda khadija take dashi wanda bai cancanci a zauna da itaba, kar kamanta ta jure duk wata wahalarka, wata ta'ba gayawa? babu, wllh itace kad'ai macen dazata iya zama dakai da halayenka bawai dan bazata iya ramawaba a'a sai dan kawai tana ma biyayya amatsayinka na wanda akace mijinta ne, Ashraf dan Allah ka yarda kasota koda sau d'aya ne ka aminci kayi zama da ita na har abada"

Ashraf yace" nifa bazan ta'ba yarda da son taba, ina son abincin tane kawai"

Imran yace" shikkenan indai in har bazaka so wanda ke dafa ma abincin ba ti daga yau kadaina son abincin, kadaina ci"

Ashraf yace" ti in banciba mutuwa zanyi, aikin banza kawai"

Imran yaja qwafa kan yace" well done yayi kayi duk abinda ranka yakesi, amma kasani wata rana ko ance kayi bazakai ba, na barka lafiya"

Yana gama fad'in haka yafita tare da flask d'in abincin.

Ashraf kam baiso hakan ta kasanceba, amma yazaiyi dan kawai yana nuna soyiwar abincinta sai ace wani sonta yakeyi, ba komi zai daina cin abincin yaga zai mutune ko kuwa zai rayu, zai fita daga cikin sabgarta gaba d'aya ma.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now