biyayya....73

639 26 4
                                    

*BIYAYYA*


Wtiting by
*Maryam Abduul*

Wattpad@Maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫


---------Ina bawa dukkan masoya karatun littattafaina haquri akan rashin jina da kukai kwana biyu.

Hakan yafaru bisa dalilin tsaida duk wani typing damukai sabida 'bullowar wannan annoba.

Zamu dakata har zuwa wani lokaci domin duqufa da addu'a da neman tsari bisa wannan cuta da take yawo.

*Muna roqon ubangiji subhanahu wata'ala dayai mana maganin wannan musiba data afkomana, da duk wani abu dayakasance bana alkhairi agaremuba.....Allah kasa damu da alkhairan dake cikin wannan duniyar baki d'aya... Ameeeeeen*

Inaso 'yan uwa ku gane wani abu wllh yakamata mukoma ga Allah mutuba mudaina aikata abinda mukeyi.mutuna cewa" zamu koma gareshi fa kuma zamu karbi sakamako" kunsan wani sakamako zaku karba? awanne hannune zamu kar'ba? duk bamu saniba sai munje can alqiyama....munafata Allah yasa mu amshe sakamakonmu a hannun dama...ameen.

Ina kira ga 'yan uwana marubuta masu rubuta batsa wad'anda sukeson su 'batamana suna dasu dubi girman Allah da Manzansa dan Allah sudaina aikata abinda sukeyi.

Wllh Allah duk wani abu dake faruwa da kamashenku dan duk abinda za'a aikata na sabon Allah to ba shakka zaiyi hukunci akansa.

Dan Allah kuji tsoron Allah kudaina bata 'ya'yan mutane da sauran jama'a kudaina jamana bala'i muna zaune lafiya.

Kusani wanda yai nagarifa kansa, dan Allah kudaina ku dawo kan hanya ta gaskiya.

Allah yasa ku anfana da abinda muketason mu fahimtar daku.

Abinda nai kuskure acikinsa Allah yagafartamin.

Wanda naiwa ba dai-dai ba dan Allah ya yimin afuwa domin duk d'an Adam tara yake bai cika goma ba.

*A qarshe inawa masoyana fatan alkhairi aduk inda suke*

Nagode.......

*Mrs.Abduul ce*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now