biyayya....81

903 44 18
                                    

      *BIYAYYA*


  By
      *Maryam Abduul*

Wattpad@maryamad856.


💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫


Aunty Maimoonah ina matuqar tayaki murnar kamma littafinki mai taken *'YAR GADARA* Allah yabada ladan fad'akarwa......ameen.


*Page.....81*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

-----------------Suna fita Ashraf ya miqe daga inda yake tare da matsowa kusa da ita, hannunsa yasa tare da kama nata kana yace" meyasa kika taho batare da izininaba?"

Dije ta bud'e baki galala tana kallomsa kan tace" ai dai da izinin mom nataho ko kaga magana taqare"

Ashraf yai murmushi kana yace" tukunna dai, ko kin manta ni d'in mijinki ne komi zakiyi sai da izinina?"

Dije ta murguda baki kan tace" miji, a ina mijin yake, ai ni har abada bani da wani mutum mai suna miji, domin bana zama da wanda baisona wanda bai qaunata ko kad'an, mezai sama nakirashi da suna miji, kar kamantafa wannan auren da akai biyayya ce kawai kuma na gama yinta"

Ashraf ya gyara zamansa tare da qara matse hannunta kan yace" wa yace miki mijin naki bai sonki, dan haka kisa aranki shi d'in naki ne har abada kuma zai soki har qarshen rayuwarsa"

Cikin zafin nama dije ta miqe tare da qwace hannunta daga nashi kan tace" qaryane wannan kuma duk shirmenkane bazai ta'ba yiwuba har abada ni ni kad'aice batare da kowaba, dan haka inma zaka farka daga dogon baccin da kake to tun wuri ka farka na gayama"

Ashraf ya miqe tare da matsawa daf da ita kan yace" kema qarya kike duk abinda kikace qaryane ni nan na qaryatake, ki nutsu ki dawo muyi rayuwar mu cikin farin ciki dan Allah khadija"

Dije ta d'ago idonta sunyi jajawur kan tace" khadija bazata ta'ba dawowa gidanka ba, kar kamanta ni d'in baiwace wacce tarasa 'yanci arayuwarta, wayasata acikin wannan wahalar? amsar kaine, koba haka bane?" ta tambayeshi tare da kafeshi da idanuwanta.

Ashraf ya sunkui da kai kan yace" naji duk nasan nazama mai laifi amma dan Allah ki dawo kudan wannan abincin naki da kikeyi"

Dije tai dariya kan tace" na dawo na ma me, bari kaje abinda baka saniba nasha kamaka kana min d'auken abinci amma sabida ance nabi miji namasa biyayya ban ta'ba cemaka ka d'aukar min ba, mekace cakai kar na sake dafawa dakai to meyasa kake d'auka, wannan kasan halin suwaye? Halin masu satane wannan kuma abinda kai yazama sata tunda bada saninabane, na ta'ba gayama a'a amma duk da girkin dakake ci innayi na ajjiye hakan baisa ka tausaya minba, sai yanzu da kaga kayi rashi zaka zo kace na dawo, har da wani wai kana sona wannan maganar ma kasan qaryace, dan haka daga yau kada ka qara kuskuren tun karata balle ma kamin wannan qazamin zancen naka, in bahaka wllh sai rayuka sun 'baci"

Tana gama fadar haka tai ficewarta daga d'akin, zuciyarta namata suya, wani 'barin kuma tanajin wani irin dad'i, amma meyasa sai yanzu zai san dacewa itama mutum ce"

Ashraf kwa wata zuface ke ketomai, gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa, daman qwarin gwiwar yasamone daga wajen dr.Saleem shi yabashi wannan shawarar akan yazo ya sameta ya lalla'bata, to sai gashi kuma haqansa bai cinma ruwa ba"

"Tabbas bazaiwa kansa qarya ba yana jin felling akanta, amma meyasa bazata fahimce shiba?" nan yaji zuciyarsa tamai baqirqirin, ko abincin da aka kawo musu ma jiyai yafice mai arai.

Koda zasu tafi Dije ko inda suke bata jeba qarshema barin layin tai gaba d'aya, dan tasan ko taje gidan su jummai zai Iya biyota, ko bama shiba dole za'ace tazo suyi sallama.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now