biyayya......

832 37 5
                                    

*BIYAYYA*

       Writing by
       *Maryam Abduul*

  Wattpad@
  Maryamad856


*Page...71*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

-----------Auta kam ba ita tabar gidanba sai wajen magrib dan saida tatsaya ta dad'a tayata suka gyara gidan, tare da kunna mai turaren wuta masu qamshi.

Auta na fita dije ta fad'a tiolet nan tai wanka, tana fitowa ta shiga feshe jikinta da wasu dad'ad'an turaruka tare dayin wanka da humra da kwalakca.

Wata dogowar riga tasa ta atamfa tai hayewarta kan gado tare da jawo wani littafi tashiga karantawa.

Ashraf kam bashi yashigo gidanba sai wajen goma na dare lokacin kam dije ta dad'e dayin bacci.

Saida ya shiga d'akin nata, kwance ya taddata qarasawa yai tare da bugun gefen filonta.

Cikin bacci dije taji kamar ana dukan wani abu dake kusa da ita hakan yasa ta bud'e idanuwanta take kwa ta saukeau kansa yana tsaye ya sa hannayensa cikin aljihun wandansa, tare da kafeta da ido.

Mitsttsike idanuwan nata tai kan ta yinqura ta miqe zaune, cikin ranta fad'i take" ko meyazo yi kuma oho"

Kallonta yai tare da gyara tsayuwarsa kan yace" waya baki izinin kwanciya?"

Jin tambayartai wata iri, take tashiga maimaitata acikin zuciyarta kan tace" baccinma bada izininsa akeyi?, to Allah ne yaban iko da izini har nasami yi"

Ashraf ya juyar dakai gefe cike da cize lebe kan yace" wow yayi, amma duk da hakan saina bada izini  to kunna, dan haka kisameni a falo bakuma nason jira" yana gama fad'a yai waje.

Dije dyage kafad'a tai kan ta miqe tare da jan hijab dinta tai waje.

Yana falon azaune, kusa dashi tasamu tazauna, tana zama yakalleta tare da fad'in " bawai nakiraki ne ko dan inason ganinkiba a'a sabida inaso kisan sharad'an zaman gidanne dan haka ki bud'e kunnuwanki dakyau kiji mezance"

Batare da yajira amsawartaba ya d'ora da fad'in " abu nafarko shine bance miki ina buqatar wani cima daga wajenkiba, dan haka in zaki jagwalgwalon ki to kiyi ke d'aya. Abu na biyu shine kullum ki tabbatar kin rigani tashi, da zarar kin tashi kuma duk fad'in gidan yazamana lallai kin sharesa tare dayin mofin d'in sa. Sannam ina so ki tabbatar kin wanke min motata sabida bana fita da mota ba'awankeba.

Abu na biyun qarshe kuma shine, ke zaki dinga budan gate idan zan fita da kuma bayan nadawo and lastly kuma kada ki kuskura ko dawasa muna ido biyu dake dan bansan ganinki ko kad'an, dan haka ki kiyaye, ban kumace ki riqe karki fadawa kowaba wannan yarage yanaki, amma ki sani matakin dazan dauka bazai miki dad'i ba"

Yana gama fad'a ya miqe tare da barin wajen.

Dije kam jinjina wannan baqin hali nasa kawai take meyasa baya da zuciyar kirkine, bakomi insha Allahu zanyi biyayya agareka ya Ashraf, kamar yadda nayiwa iyayena biyayya na aureka, zan maka duk abinda kakeso da yardar Allah"

Da wannan tunanin ta miqe takoma d'akin ta sai dai sam takasa baccin tunanin halayen kawai Ashraf takeyi meyasa hakane, shi zuciyarsa bata da sanyine?, batason sanda bacci yai awon gaba da itaba.



.....Washe gari kamar jiya haka ta tashi da wuri qasa ta sauka nan tahau aikin da yasanyata, saidai tamatuqar wahala sosai sabida suk sharar da take bata taba irintaba dan gidan da girma yake sosai, amma dan tasamu tacimma manufarta saita kasa gajiyawa haka ta daure ta gama aikin.

Nan tadawo falo shima haka tayi, tana kammala tsaftace gidan ta fad'a kitchen duk da yace baison abincinta amma battajin zata iya qinyi dashi, dan Hanne sosai tamata fada akan hakan, koda yace" kartayi" to tayi amma kad'an kuda baiciba ta bayarga mai gadi ko almajiri.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now