Part 78

562 31 1
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!



P1️⃣1️⃣2️⃣
Ansaar ne ya soma qarfin halin qarasawa inda babies d'in suke a jere reras yana kallon su cike da wani irin annashuwa da jin dad'i yakai hannu ya d'auko ta kusa dashi yana kallon ta ya soma mata addua yana tofa mata.

Haka sauran sukayi koyi dashi suka qarasa gaban gadon harda Hamdiyyah ta d'auki ragowar d'ayan itama tana kallo tana hawaye.

Mommah ce ta qaraso ta zauna tace "Ku had'a min su don Allah na dauke su naji dadi."

Duk suka had'a mata jariran hud'u reras gwanin ban sha'awa Abbuh ya fiddo camera ya d'auke ta hoto dasu sai baccin su suke kamar yanda itama mahaifiyar tasu keta nata baccin na huce wahalar data sha.

Haka suka wanzu cikin farinciki don sam babu wanda ya iya matsawa daga kusa da ita da jariranta harta farka wajen bayan la'asar dake allurar bacci sukayi mata.

A hankali ta bud'e ido tana qarewa wajen kallo can kuma ta juya tana kallon Mommah da Maimunatu suna cin abinci a plate d'aya,Hamdiyyah na gefe da d'iyarta tana bata itama.

Can gefe kuma su Safiyyah ne da Lubna da Asiyah suna hira qasa qasa,sai su Ansaar dake gefensu suma abincin suke ciki saidai kowa nasa daban ba kamar su Mommah ba.

A hankali tace "Mommah."

Da sauri ta miqe don bata lura da ta tashi ba ta ajiye spoon d'in hannunta tace tana qarasa "Ashe kin farka sannu."

Kai ta d'aga mata kafin a hankalin ta sake cewa "Zanje toilet."

Gyad'a mata kai tayi ta kama ta sai Hamdiyyah ta taso ta taya ta suka kama ta suka kaita toilet Mommah ce ta tsaya Hamdiyyah ta dawo ita ta taya ta yi brush ta wanke fuskar ta sannan ta dawo da ita d'akin,ta zaunar da ita sannan ta had'a mata tea a cup mai kauri ta miqe mata.

Ganin tana noqewa yasa ta zauna ta fara bata tana cewa "Idan baki ci abinci ba taya zaki shayar da babies d'inmu."

Daidai lokacin da su Abbuh,Sabeer,Sameen,da Aseep suka shigo d'akin kuma yayi daidai da farkawar namiji d'aya a cikin jariran ya tsanyare da kuka kuwa mai sauti da alama yana da murya sosai,ita sai a sannan takai duban ta wajen jariran.

Zaro ido tayi tana kallon Mommah tace "Wannan yaran wacece ta sake haihuwa aka hada min dasu?"

Murmushi tayi tana cewa Hamdiyyah "Dauko shi mana."

Sannan ta maida hankalin ta kan Iyyah tace "Kece kika haihu dai ba wata ba kece Allah ya azurta mana da yara har hud'u reras kinga dadi da ribar haquri kenan."

Kawai sai ta hau hawaye tana girgiza kanta haka aka bata baby d'in dake kukan har wata er uwar tasa ta farka don haka aka had'a mata su ta fara shayar dasu a haka doctor ya shigo ya same su yana murmushi ya sake congratulating su Abbuh sannan ya sake gaya musu qa'idojin wanda aka yima Cs duk sukace sun kiyaye sai kuma shan magunguna akan lokaci.

Kwanakinta hud'u suka sallame ta suka koma gida nan kuma aka fara shirye shiryen tafiya nigeria don dai Iyyan da kanta tace gara su tafi ayi suna acan.

Visa bata samu ba saida sukayi kwana biyar lokacin kwanan babies tara kenan har an rad'a musu sunayensu.

Matan sukaci sunan Ayyah wato Khadija,sai sunan Mahaifiyar Iyyah Maryama sai kuma mazan sukaci sunan Muhammad Basheer da kuma Muhammad Salees ana kiran su da Ashnaah,Ashfah,Ashfaq, da Ashraph.

Suna dawowa nigeria kai tsaye aka wuce da ita Gangare wanda gabadaya gidan suka wuce can.

Sun samu an gyare sashen su tsap harda turaren wuta tun kafin su isa aka dora ruwan wanka saida suka ce akace baza a iya yi mata wanka ba saboda aikine aka mata dole haka aka haqura sai jariran aka yiwa.

MashaAllah tubarakallah shine abinda kowa ke fada idan yaga jariran don girman su sai kace kowanne shi daya aka haifa.

Sai da sukayi arbain a gangare bisa ga al'ada sannan suka wuce gumel can ma satin su biyu suna zaga dangi sannan suka wuce kano inda suka soma shirye shiryen komawa don gab su Hinde suke da komawa school.

A lokacin kuma Asiya ta haifi nata babyn namiji santalele mai kama da mahaifinsa sak kwana biyu tsakani Lubna ta haifo tata d'iya mace mai kyau haka kwana hud'u tsakani Hamdiyyah ta haifi tata mace itama ta biyu kenan qatuwa.

Dole suka dakatar da komawa aka tsaya akayi suna,yaran mata sukaci sunan Mommah da Iyyah Asma'u da Aminatu ake kiran su da Nasreen da Nasmah namijin yaci sunan kakansa na wajen uwa suke kiransa da Noor.

Dole yabar Asiyan anan saboda wankan jego sai tayi arba'in ta koma.

Suka tattara suka koma ya cigaba da aikin sa Iyyah ma ta koma makaranta ta dinga barwa Inna Atika da suka tafi da ita yaran idan sun dawo kuma suke kula dasu tare.

Asiya nayin arba'in itama aka had'a ta da wata er dattijuwa suka koma tare saboda rainon Noor baza ta iya ba ita kad'ai ga makarantar ta.

*BAYAN SHEKARU HUDU*
Iyyah ta kammala degree d'inta kuma ta dawo nigeria tayi service d'inta ta nemi aiki a gidan wani radio mai zaman kansa inda ta soma aikin ta cikin nasara.

Nan kuma ta qaddamar da wani programme da ta sawa suna *QADDARA CE SILA* wanda ke fad'akar da al'umma akan yarda da qaddara da kuma kallon ta ta kyakkyawar fuska koda kuwa ba kyakkyawar qaddara bace,kuma sosai yake magana akan yara marayu na gidan marayun dake nassarawa da sauran gidajen marayu dake nigeria tana ta wayar dakan al'umma akan su da ma d'aukar su kuma Alhamdulillahi kwalliya na biyan kud'in sabulu don har ta hanyar ta ansha bi ana daukar yaran daga gidaje da dama.

Fauziyya itama ta haifi twins d'inta duk maza wadanda aka sawa suna Ajmal da Akmal.

Iya Rammah dai damuwa da tsananin tashin hankali yasa kwalkwalwarta gocewa tana bi gari tana ta fama har dai abu ya zama tuburan tabar garin ta fantsama duniya aka rasa inda ta shiga.

Hinde ma ta had'u da wani d'an minister a Uk kuma ya nemi auren ta Abbuh ya aurar da ita dangin mijinta sai hamdala don suna matuqar sonta da kulawa da ita kamar ita ce er dangin ba mijin taba har ta haifi babyn ta namiji yaci sunan minister Ibrahim Khaleel Nuhu suke kiransa da Akram.

Larai anga uwar bari Ansaar ya mata nisa dole ta haqura ta auri wani dan kusa da qauyen su mai mata biyu taje a ta uku babban gida irin nasu.

Tammat bi hamdulillah iyakacin abinda ya samu kenan dafatan inda nayi daidai Allah ya sada mu aladan inda na kuskure kuma Allah yayi mani afuwa dafatan zaku biyo ni a littafi na gaba acikin sabuwar shekara in sha Allahu.

Nagode sosai da qauna musamman masoya wannan littafi ina qara godiya Allah yabar zumunci.

Darussan dake cikin sa kuma dafatan za ayi masa kyakkyawan fahimta a kalle shi ta fuska mai kyau a kuma yi amfani dashi.

*Alhamdulillahi Ala kulli Haal.*

Much much love 💖🥰

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now