QADDARA CE SILA!

570 58 4
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya* 

🅿️2️⃣
Da asuba ta farka tayi alwala tayi sallah sannan ta soma karatun alqur'ani har wajen qarfe bakwai ta tashi Ansar dake ta bacci ta sashi yayo alwala yayi sallah sannan tayi masa wanka ta sanya masa uniform d'insa ta goya masa jakarsa taja hannunsa suka fito ta kulle qofar d'akin nasu kowa na ta sha'aninsa suka fice Ansar nata rigimar yunwar da yakeji don daman bai qoshi da dare ba.

Kai tsaye wajen wata 'yar kasuwa suka nufa inda dandazon mutane ke taruwa ana siye da siyarwa da safiya na kayan karin kumallo haka nan da yamma ma kayan kwad'ayi da d'an tab'a ka lashe.

Mata da yara da samari sunfi yawa a wajen haka taja Ansar suka tsaya a gefen mai saida qosai haka a gefe itace ke saida koko amma yaranta ke zubawa.

Saida aka rarragu sosai kafin ta miqa kud'in ta a hankali tace "Bamu koko na ashirin qosan talatin."

Da qarfi ta fizgi kud'in ba tare da ta kalli inda take ba tace "A ina za a zuba muku?"

A hankali tace "Zuba msa mana don Allah a kwanon ki Ansaar ne zaisha kinga makaranta zan kai shi."

A wani irin hanzarce ta juyo a masifance tace "Ashe Amina baqin cikin naki da hassadar da kike min har ta kai haka?"

Cikin rashin fahimta tace "Ban gane ba me nayi na hassada Ramatu?"

Cike da takaici tace "Inba hassada da baqin ciki ba  ta yayane zaki ce na zubawa shege mara tsarki a kwanona na sana'a mai tsarki?siyar mikin da nake ina cakud'a kud'ina ma dana hannun ki bai ishe niba sai na zuba muku to wallahi saidai ya mutu da yunwa kuwa,ke ungo ma kud'in ki bana siyarwa." Ta qarasa tana miqa mata hamsin d'in data bata.

Cikin marairaicewa tace "Don Allah yi haquri yunwa yake ji bari in samo leda saiki zuba masa."

Maida hamsin d'in tayi cikin bokitin da take tara kud'in cinikin tana fad'in "Saboda baqar zuciya da hassada d'an abinda nake samu na ci da iyalai na shine zakice na bawa shegen d'anki don kawai ki ja min masifa na rasa d'an cinikin da nake yi na daina."

Itadai bata kula ba ta nemo ledar ta miqa mata ta zuba musu kokon da qosan amma duk da haka vata daina mitar da take ba,itadai kar6a tayi taja Hannun Ansar suka wuce amma suna bada baya wata dake tsaye bayan su tace "Kema dai Ramatu jarabar son kud'ine ya miki yawa wallahi,in ba haka ba menene na kar6an kud'inta har kina saida mata da abun ki sai kinje kin kwashi zunubin da ba naki ba."

Zaro ido Ramatu tayi tace "Zunubi kuma ni Ramatu na meye?"

Wata acan gefe tace "Eh fad'i da kyau don ni naji wani mutumi ma yace ko magana ce ta had'a ka da shege sai an masa dukan zunubin kula shin da kayi."

Ramatu ta sake zaro ido tace "Wai Allah na ni daman bana kula shegen ita uwar dai nake kulawa."

Kai d'ayar ta gyad'a "To ke banda shirmen ki akace shi d'an ma balle uwar data haife shi."

Ramatu ta kama ha6a tace "Ahh ai kuwa dai na daina haka kawai banji ba ban gani ba ban aikata laifi ba walakiri ya narke ni."

Ladidi tace "Ai kuwa."

Duk suka fashe da dariya sannan Ramatu tace "Ai kuwa tayi kai don ba zan jawa kaina ba dukan walakiri ba hannuna a alfasha...."

Aminatu dake janye da hannun Ansaar sun riga da sunyi musu nisan da baza taji qarashen maganar ba sai tashin dariyar su taji harda masu qyaqyatawa,kamar an 6alle fanfo haka hawaye ya shiga kwararo mata tasa bayan hannunta ta goge Ansaar ya d'ago kai lokacin da ta jashi zauren wani gida yace "Iyyaah menene?meyasa ki kuka?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now