Part 63

251 16 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!

P9️⃣6️⃣
Duk da irin gajiyar da suka kwaso hakan bai sa yayi bacci lakadan ba sai yayi sai kawai ya farka kamar wanda aka tasa.

Shi kansa abin ya bashi mamaki amma sai ya alaqanta hakan da qila gajiyace tayi masa yawa take sashi kasa baccin.

Bai samu cikakken bacci ba saida aka yi sallar asuba ya samu ya runtsa bacci ko mai dad'in gaske ne ya d'auke shi harda mafarkan da ya saba na Saratun sa.

Har wajen sha biyu da rabi suna bacci dake lahadi ce,wajen qarfe d'aya Qanwar Isma'il ta shiga qwanqwasa musu tana kiran "Ya Isma'il wai inji Hajiya ku tashi haka nan."

Dake baida nauyin bacci shi ya fara jinta ya miqe da sunan da Allah yana cewa "Jeki kice mun tashi."

Har ta juya sai kuma ta sake cewa "Tace ku fito gasu Yaya babba sunzo."

To kawai ya iya ce mata ya soma tashin Isma'il da har yanzu sharara bacci yake cikin magagi yace "Meye wai."

Ansaar yace "Ka tashi wai su Yaya Babba sunzo."

Da sauri ya miqe yana cewa "Yay."

Dariya yaba shi ma shi don haka yayi dariya yana miqewa ya shige toilet yayo wanka da brush ya dawo Isma'il kam saida yaje ya dawo sannan yayi nasa wankan yana shiryawa yana ce masa "Yaya ya matsu ya ganka fa muje don Allah."

Da sauri ya zura riga da wando na English wears sun masa kyau kuwa suka fita kawai sai yaji qirjinsa na wani irin bugawa da sauri da sauri kamar wanda ke gudu ya tsaya.

A haka suka shiga falon kansa a qasa Hajiya suka soma gaisarwa dake itace a bakin qofa ita ke fuskantar su kafin suka juya wajen su Yaya babba kamar yanda suke kiran sa.

Kafin suyi magana Hamdiyyah da qarfi tace "Ansaar."

Da mugun sauri ya d'ago yana kallon ta da mamaki don bai gane wacece ita ba amma ko makaho ya shafa fuskokin su yasan suna kama,cikin wani irin yanayi ta taso ita da sabreena data qwace daga hannun Sabeer tana cewa "Uncle." 

Da mamaki yabi yarinyar da bai tab'a gani ba da ido sannan ya sake kallon Hamdiyyah data qaraso gabansa tana hawaye tare da shafa fuskar sa.

A hankali ya riqe hannun ta ya kasa magana sai kawai Sabeer shima daya qame yana kallon Ansaar ya taso ya ruqo ta yana cewa Isma'il "Junior waye wannan?"

Isma'il yace "Shine abokina Ansaar da kuke ta sab'ani baku hadu ba."

Gyad'a kai kawai ya iya yi sannan ya ciro wayar sa yayi qarfin halin kiran Abbuh ya masa maganar da bawanda yaji,Hajiya kam da mamaki take binsu da kallo tana cewa "Meke faruwa ne kai Sabeer?"

Kasa magana yayi shi da kansa abun ya d'aure masa kai ya kasa wassafa yanda zaiyi da lamari ma a ransa,ganin duk sun mata shiru sai Hamdiyyah dake ta kuka yasa ta zubawa sarautar Allah ido taga me zai faru.

Wajen mintuna talatin sukaji shigowar ahlil Abbuh Muhammad Basheer gidan kai tsaye kuma yau babu surkuntaka.

Duk suka miqe suna jiran qarasowar su Ansaar qirjin sa sai dukan tara tara yake yana son ganin su waye zasu shigo.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now