Part 17 Qaddara ce sila

335 18 0
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.



_Page 17_

●●●Bata kulata ba kawai ta juya ta shige d'aki don ta lura sam Iyaa Rammah hankalin ta ba irin na manya bane kamar yanda jikin ta yake na dattijai tana jin ta tana ta hayaniya bata sake bi ta kanta ba jimawa kad'an kuma saita jiyo su ita da mamar Hinde a tsakar gidan tunda rigimar data faro ita bata nan ta fita.

Kamar daga sama ta jiyo Iyaa Rammah na ce mata "Kinsan Allah indai har kika bari wannan tabbatacciyar yarinyar da shegen d'anta suka taka gidan er ki shikenan ta kaso mata aure an gama auren da gashi nan ko sati bai rufa ba."

A qufule tace "Wallahi bata isa ba tabdijan ai ko saidai ayita ta qare akan dai ta kaso min auren d'iyar da akayi shi bisa rashin son maqiya ga auren da tarin maqiya."

Iya Rammah ta amsa "Ah to ai kece da sanya da shashanci tun asali waye yace ki bari ta ma fara kula d'iyar ki ni kinga duk kaf cikin yarana akwai wanda na bari Amina take kula su ai bada ni ba."

Cike da 6acin rai tace "Barni da ita kinibabba mai neman jawa mutane jafa'i wallahi saidai ya qare mata akanta."

Iya Rammah cikin sake so zuga ta sosai tace "Ah to ai gara kije kija mata kunne sosai in ba haka ba kinsan ta da shegen taurin kan masifa saifa taje."

Har ta tafi Iya Rammah ta sake kiranta tace "Saura kuma mijin ki ya tambaye ki kice nice na fada girmana ya fad'i."

Tana murmushi tace "Inaa bazai jiba wallahi ai taimako na kikayi."

"Saiki hanzarta zuwa kafin ita ta riga ki zua ta kaso miki auren d'iya ba gaira ba dalili." Ta qarashe zancen da jajantawa kamar ma taje ne.

Tana jin haka ta miqe tsam ta je ta tura qofar su tun ma kafin Hasiya ta qaraso.

Tana zuwa ta ta6a qofar ta jita a kulle sai kawai ta soma zuba ruwan bala'i kamar zata cinye qofar ta shiga ta cinye su d'anyu harda Ansaar da baisan komai ba shima saida ya samu rabon sa sosai sannan tabar wajen ta tafi tana ta mita.

Duk matan gidan na ji don da yawan su sun fito jujjuye ruwan da suka tattara na sama a makayen su don haka da yawan su dariyar abun suke 'yan baruwan mu kuma a cikin su sabgogin gaban su kurum sukeyi.

Haka ta qarar da ragowar yinin ranar cike da qunci da 6acin rai ta kuma sa a ranta gidan Hinde dole ne taje koda tana sallama mijin zai had'o Hinden da sakin ta idan yaso sai su dawo tare kuma taga abinda zai biyo baya.

¶¶¶¶¶¶¶¶
Suna tafe shiru kowannen su akwai abinda yake saqawa a ransa har suka isa gidan su dake staff quarters na makarantar mai d'auke da d'akunan bacci biyu da kitchen da falo d'an matsagaici mai kyau dashi.

Yaraf suka zube cikin qananun kujerun falon M.Marwaan ya runtse idanunsa yana jan iska cikin huhun sa tsahon lokaci kafin ya furzo ta waje gabad'ayan ta yaja ajiyar zuciya mai tsayi ya ajiye kana ya d'ago yana kallon M.Abdulhadi da shima ya nutsa cikin tunanin sosai yace "Mallam."

M.Abdulhadi ya kalle shi yace "Na'am."

M.Marwaan ya sake shaqar iska sannan yace "Lamarin nan na d'aure min kai da mamaki fa abin yayi yawa fa."

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Wallahi Mallam nima tunani nake akansu wai meye silar wannan tsanar da tsangwamar haka?"

D'an d'aga kafad'a yayi sannan yace "Nidai daga abinda naji shine Mahaifiyar Ansaar bata ta6a aure ba ta haife shi."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now