Part 16 Qaddara ce sila

325 22 2
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

'''Tk Maid AKA Husbyn Meenal AKA Besty this is yours wallahi ina matuqar jin dad'in yanda kake nuna qaunar ka ga wannan novel dama sauran novels d'ina Allah yabar qauna besty Allah ya nuna min ranar abun muyi shaku shaku da kwaso shoki son ran mu much much luv Besty.'''

_Page16_
●●●●Haka ta tashi cikin dare tana ta addu'a da neman za6in Allah akan ta tafi tabar garin ne ko kuwa ta cigaba da zama a cikinsa har Allah yayi ikon sa akansu ita da yaron ta?.

Haka har aka kira asuba ta sallace ta bata koma ba saida ta kai Ansaar makaranta duk da baccin dake damun idon ta gashi garin ya gingimo hadari sosai har tana tunanin ta kaishi kota qyale shi amma ganin kamar hadarin yamma yake yi yana zama iska yasa tasa a ranta bazai yi ruwa ba don haka ta kaishi tana shiga tsakar gidan kamar jiran ta ake ruwa ya goce ko yayyafi babu.

Da gudu ta shige d'akinta ta d'ebo kwanukan da take tara ruwa ta tattara ta koma ta cire kayan jikin ta ta shanya sannan ta kwanta ta shige mayafi aiko wani irin bacci mai nauyi da dad'i yayi awon gaba da ita.

Shiko ga Ansaar Allah ya taimaka M.Marwaan na ajin yazo musu kiran suna kuma ruwan ya tsuge don haka ya zauna yana musu bitar abubuwan daya koya musu tunda yasan ba mallamin da zai shigo ajin a lokacin,ruwan bai tsagaita ba har aka kusa tashi don anyi awa da awanni ana yin sa mai yawa kuwa.

Yana tsagaitawa aka kad'a qararrawa akan kowanne d'alibi ya tafi gida don hadarin kamar ma sake gangamowa yake ta gabas.

Aiko babu jira d'alibai suka fito yuuuuuu akayi hanyar gida ana sowa da murnan yau an tashi da wurwuri za a samu wasa kenan.

Caraf Kamilu abokin Lado ya cafke Ansaar lokacin da suka fito daga cikin harabar makarantar sannan yace "Don uwar ka karuwa wana kama."

Da gudu Lado ya qaraso wajen cikin dariyar qeta yace "Yawwa Kamilu Allah kuwa yau dole na baka alawar d'inya in baban mu ya dawo daga kasuwa janyo shi nan."

Kiiiiii suka soma jansa yana turjewa tare da fasa kuka don yasan in sun kai shi inda suke niyya zai daku ne iyakacin dakuwa.

Da gudu sauran yaran dake abokan su Ladon ne kuma sune sukayi musu ihu a jiya suka dafo bayan su suna ihu suna dariyar jin dad'in kama Ansaar d'in da akayi.

Shikam da yaga ba sarki sai Allah sai ya fara ihu sosai aiko kamar wad'anda ya bawa iznin su duke shi da ihun suka rufe shi da duka kamar Allah ne ya aiko su suka shiga cud'a shi cikin ta6o yana birgima yana ihun kuka saida suka yi masa ligib shima gudun da suka yi M.Marwaan da M.Abdulhadi suka hango sun nufo su shine suka gudu.

Yana kwance linkif cikin ta6o yana kuka kamar ransa zai fita ya d'ago shi cikin tausayawa yace "Mallam jeka ni bari zanje na kai yaron nan wajen mahaifiyar sa."

M.Abdulhadi yace "Aa muje mana."

Cike da takaici ya d'aga yaron yace yana kallon M.Abdulhadi "Don Allah ga jakar sa can d'auko masa mana mallam."

Ba musu ya d'auko suka nufi hanyar gidan su Iyyaah kowanne a ransa akwai abinda yake saqawa har suka isa ba wanda ya iya tankawa d'an uwansa.

M.Marwaan ya bud'e murya ya kwad'a sallama a qofar gidan,daga ciki Asabe d'iyar iya Rammah ta amsa sannan tayo waje tana tambayar waye.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now