QADDARA CE SILA!

1.7K 65 5
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_

*©ZahraArkel*

*Alhamdulillahi Ala kulli haleen,Allah ya qaddara gamawar littafin ANA BARIN HALAK... yau kuma gani d'auke da sabon littafi wanda nake fatan zaky biyo ni sannu kan hankali don tsintar d'an wa'azin dake cikinsa dafatan kuma Allah ya bani iko da damar kammala shi kamar sauran*

*HAJOW sisters u re the best sisters from diff wombs from diff Mums,i rily do appreciate yanda kuke supporting each oda keep it up sisters Allah ya qara had'a kawunan mu amin.*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar lallai QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya*

Fans luv u lodi lodi A kaftaaaaa......😊😊

*Bismillahir rahmanir raheem.*

🅿️1️⃣
"Shege tsinanne matsiyaci zai fasa min er qwaryar da nake da ita qwalli d'aya jal kamar rai matsiyacin yaro kawai." Iya Ramma kenan data fito daga madafa tana masifa wa wani d'an qanqanin yaro da duka duka bazai haura shekaru hud'u ba.

Duk wannan masifar da take yaron bai fasa yi mata ihu da fad'in "Wooo nadai bugo nadai bugo."

"Yar guntuwar ta6arya ta wawuro kusa da qaton turmin dake tsakar gidan ta bishi tana fad'in "Bari na fasa maka kai shege d'an iska lalatacce kafin ni ka fasa min kai ba uban da zai biya ni gare kaba."

Ganin ta da yayi yasa shi wawurar er ball d'insa ta leda yayi wani d'aki dake can 6angaren kudu yana kiran "Iyyah Iyyah bud'e min qofa."

Kafin ya qarasa qofar ta bud'e wata matashiyar macece ta fizgo yaron cikin zafin nama kuma ta tura qofar katakon mai qwari tare da sa mata sakata ta kulle.

Koda Iya Ramma ta qaraso qofar d'akin bugu take kamar zata karya qofar tana fad'in "D'an zina d'an fasiqai da ki bud'e qofar mana wallahi dana karya ku duk ku biyun don daya fasa min qwaryan nan gwara na karairaya shege na zubar."

Tijara sosai ta zuba a wajen kafin tabar shi matar gidan sunata hada hadar su kowa da abinda yake yi wasu wanki a bakin rijiyar da take tsakar gidan,wasu na daka wasu surfe a turamen tsakar gidan dukkan su ba wadda ta tofa ko qala har saida Iya Ramma ta gama sha'aninta sannan wata dake can gefe bakin qatuwar kwatar su tana zazzage kayan kashin d'anta taja tsaki tace "Banda ma abu irin na Iya Ramma wai menene ma yasa take kula shi wannan d'an iskan yaron tijararre shege daman ina yaga tarbiyya."

Wata daga gefen ta itama wankin take tace "Hmm to wai kema dai ita kanta mai bada tarbiyyar ta ganta ne balle ta bawa shegen d'anta."

Wata daga can qurya tace "Yo banda abun ku wai shege da uwar shege ina suka ga mamora,itan ma gani tai zata iya,ni fa tuntuni na daina shiga sabgar wannan yaron bashi da mutunci."

Duk zantuttukan da suke akan kunnen tane don haka ta kifa kanta a cinyoyinta tana wani irin kuka mai cin rai, inda sabo yaci ace zuwa yanzu shekaru hud'u da watanni ta saba da yanda 'yan gidan dama 'yan gari ke mata akan yaron nan amma har yanzu zuciyar ta ta kasa sabawa da wannan rayuwar ta qunci da baqinciki.

Yaron ta d'aga kai tana kallo lokacin da yake zaqulo kayan kara da shine ya had'a abunsa da kansa daga qasan gadon qarfen dake d'akin a hankali tace "Ansar."

Da sauri ya d'ago kai yana kallonta amma ganin yanda fuskar ta ke jiqe da hawaye jage jage yasa shi saurin shiga taitayinsa sosai ya shiga qifqifta idanuwa ya had'a da jan majina yana kakkaucewa don kada ta dake shi.

A hankali tace "Meya had'a ka da Iya Ramma?"

Cikin rawar murya tason zaiyi kuka yace "Wallahi Iyyah itace jiya ta doke ni ban mata komai ba kuma tace min shege mara uba shine nj kuma na rama akan qwaryarta."

Kai ta kad'a tana qoqarin shanye kukan daya taso mata tace "Amma bana hana ka kome zasuyi maka kace zaka rama akan wani abu nasu ba?" Ta qarasa da shan mur sosai.

Tuni idonsa ya kawo ruwa na tsoron kada ta dake shi yace "Allah Iyyah na daina don Allah kiyi haquri."

Sake had'e rai tayi tace "Idan ka qara fa?"

Yana qoqarin had'iye kukansa amma duk da haka saida hawaye ya biyo kuncin sa yace "Ki zane ni."

Kai ta kad'a tare da miqewa jin an kira sallar magriba tace "Tashi muje muyi alwala."

Da sauri ya miqe ya tattara kayan wasan nasa ya tura su inda ya d'auko su sannan ya bi bayanta.

Alwalar suka d'aura a qofar d'akinsu suka koma ciki don dama iyakacin su kenan babu mai yarda ya matsa kusa dasu balle har a mu'amalance su.

Harira data fito daga band'aki ta dube su lokacin da suka gama d'aura alwalar tayi dariya tare da ta6e baki tace "Kai kace sallar ma kar6ar ta ake an dage da ibadar qarya wadda bata kar6uwa."

Duk yanda taso danne kukan ta ta kasa da sauri ta janye shi suka shige d'aki,tana shimfid'a darduma shima ya tsaya a bayanta saita juyo tace "Aa Ansar na gaya maka maza a masallaci suke sallah a jam'i yafi lada don Allah kaje can."

Ta6e fuska yayi yace "Don Allah Iyyah ki barni nayi anan innaje masallaci kullum sai su Lati sun tare ni a hanya sun min duka suce wai ina shigawa su babansu masallaci ni bani da tsarki wai inji Innarsu."

Kai kawai ta kad'a ta juya ta tada sallar zuciyar ta a matuqar quntace,haka suka yi sallar magribar suna idarwa ya d'auko jakarsa suka soma maraja'a ta qara masa qur'ani,hadith da sauran littafan da take koya masa dukkan lokaci irin wannan kuma da yake yarone mai hazaqa kai sai kayi tsammanin ya ninka shekarunsa ne don yanda yake iya d'auke dukkan karatun datake koya masa don a shekarunsa hud'u ya kusan had'a izu uku.

A haka suka kai sallar isha'i suka sallace ta sannan ya fara neman abinci,sauran data saba rage masa ana ranar ta ta miqa masa yaci amma bai qoshi ba a haka ta dinga lallashin sa har ta samu yayi bacci don tasan yau dai kam basu da tuwon dare tunda Ansar yayi wa Iya Ramma laifi.

Tana jin shigowar yayan ta bai neme suba itama saita share duk da yinwa dake qwaqwalarta da qyar ta samo guntun gari tana da quli wanda tayi da kanta ta hada da gishiri ta kwad'anta taci ta kora da ruwa badon ta qoshi ba ta tashi ta kwantar da Ansar itama ta kwanta tana ta tilawa har bacci ya d'auke ta.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
'Yan yarane identical twins a harabar gidan da yayar su wadda daga gani dai ba wani tazarar shekaru ta basu ba qwallo suke duk su ukun lokacin da wata budurwa ta fito daga falon gidan tace "Toh oya ku wuce muje a shirya islamiyya."

Dire diren qafafu guda daga yaran ya fara amma gudan wucewar sa yayi babu alamun yaji d'an uwan nasa na rigima.

Cak ta d'auke shi suka wuce cikin gidan a falo ta dire shi d'an uwansa har ya fara cire kayan jikinsa yana ganin sa ya zura da gudu yaje ya warto wandon da yake hannun d'an uwan abinda ya sa d'an uwan fusata kenan ya bishi da gudu.

Zagaye falon suka shiga yi yana binsa yana ya bashi wandon sa shi kuma yana wandon sane,basu tsaya a ko'ina ba sai a kitchen,da sauri mahaifiyar su dake had'a salad ta dakatar dasu da fad'in "Kaii meye haka lafiya?"

Cikin 6acin rai wanda aka fizgewa wando yace "Mommah Areep ne ya d'auko min wando na na islamiyyah kice ya bani."

Wanda aka kira Areep yace "Qarya ne Momma wando nane fa."

Cike da takaici tace "Bani dallah nasan halinka yanzu sai tayi nasan ka d'auko." Ta qarasa da duba robar wandon.

Cike da takaici takai masa duka tace "Gashi nan nasa ka d'auko nifa bana son rigima da tsokana ka sani wallahi zan ma dukan tsiya kafin ku bar gidan nan."

Ta6e baki yayi ya juya ita kuma ta miqawa yaron tace "Ungo Aseepin Abbuh jeka saka kaji yaron kirki kazo ka kar6i alawar ka."

Yanayinsa na rashin son magana da ciccin maganu ya kar6a ya juya ba tare daya amsa ba a falon ya tadda anata danbarwa da Areep shi daman kullum sai anyi haka kafin asa uniform kona boko kona islamiyyah shikam gefe ya koma ya saka kayansa ya shirya ya sa hular sa sannan ya goya jakarsa.

Saida suka kwashe mintuna kusan biyar kafin aka gama sawa Areep nasa uniform d'in Mommah ta fito ta basu alawowin suka wuce su ukun aka sasu a mota suka tafi islamiyyar.

*©ZahraArkel ce!* 💝

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now