Part 74

273 11 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!



P1️⃣0️⃣8️⃣
Ta jima don ta kusan awa guda bata fito ba har ya gaji da zaman bakin gadon ya tashi ya qwanqwasa mata toilet d'in yana cewa "Kizo ki tashi su Salmah su tafi wajen Mommah."

"Quuuuuu." Cikinta ya sake bada wani sauti a karo na ba adadi tun shigar ta kamar mai shirin yin zawo tayi dira dira ta juya ta sake juyawa tama rasa me zata yi takamaimai saida saida ya sake qwanqwasawa sannan tayi qarfin halin fitowa amma jikin ta kana kallon ta kasan rawa yake yi.

Da kallon mamaki da tausayi ya bita a ransa yana ji lallai dole ne koda baiyi wa Mommah alqawari ba ya maida ita cikakkiyar mace kamar kowacce macen aure.

Kai tsaye wajen Little ta nufa ta sunkuce ta cikin qarfin hali sannan ta kalle shi muryar ta nad'an rawa tace "Don Allah to ka taso Salman."

Miqewa yayi ya tashe ta dake bata da magagi sai ta miqe yaja hannun ta suka kaisu wajen Mommah.

Har sun fita ta kwalawa Iyyah kira kamar me jiran kad'an ta juya ta sauri shi saima ta bashi dariya ya bita da kallo ya kula a masifar tsorace take.

Tana shiga Mommah ta kama hannunta ta jata waje yana tsaye inda yake sai kawai tace "Muje d'akin su Ansaar."

Suna zazzaune a falon suna ta ludo tace su tashi su koma d'akinta zasu yi magana duk suka miqe suka fice sai ta zaunar da ita kan kujera 2seater tana fuskantar ta ta kwantar da murya tana kallon ta tace "Kiyi haquri bawai zan shiga tsakanin ki da mijin ki bane a'a saidai shawara da nake son baki,don Allah kiyi haquri ki karb'i mijin ki hannu bibiyu ki kwantar da hankalin ki ke ba kamar budurwa er shekara sha bace yanzu kinga dole kuna da banbanci nasan tilas akwai wannan tsoron na farko duk shekarun mace bazai barta ba amma ki daure ki zama jaruma karki gaza wajen bawa mijin ki gudunmawa don Allah."

Kai kawai ta iya d'agawa idonta ya cicciko da qwalla amma bata yarda Mommah ta gani ba ta share da dabara sannan tayi saurin dakewa duk da muryar ta na rawa tace "In sha Allahu bazan baki kunya ba."

Jinjina kai tayi tace "Kar a manta da a nemi agajin ubangiji kuma dai mijina a gidan surukai yake a dinga tunawa." Ta qarasa da zolaya.

Yaqe ta qaqalo tayi tace "Karki damu."

Jinjina kai tayi ta miqe tana cewa "Tashi na kaiki wajen angon ki tun kafin ya qosa ya biyo mu."

Jiki ba qwari ta miqe tana binta haka suka shiga d'akin ta Mommah tace "Abbuh ga amanar qanwata nan a riqe ta da kyau."

Jinjina kai yayi yana hadiyar yawu da qyar yace "Na karb'a."

Ta juya tana murmushi tace "Saida safen ku."

Iyyah kamar ta riqe ta haka ta riqa ji ko ta bita amma hakan bazai yuwu ba dole ta juya ta kalle shi shima ita yake kallo duk sukai duru duru kamar wasu baqin juna shine ya daure ya tsinka shirun da cewa "Je kiyo alwala kizo muyi sallah."

A hankali tace "Ina da alwala."

Sallaya ya janyo ya shimfid'a musu yaja su sallar har suka idar a fargaba take haka nan suka yi addua suka shafa sannan ya gabatar mata da madara da naman taci kad'an tace ta qoshi shima da ke yaci abinci bai wani ci ba ya ajiye.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now