Part 10 of Qaddara ce sila

347 25 0
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

_Page 10..._
*Sorry zaku ga page 8 guda biyu nice nayi mistake nayi su guda biyun d'ayan page 9 ne*

●●●"Hajaarah duk fa abinda mahaifiyar ki tayi itace ta haife ki ba kece kika haife taba in gyara zakiyi mata bata haka zaki gyara mata ki vita da lallami da lallashi sai ma tafi fahimtar ki su iyaye 'yan lallashi ne duk irin halin su kuwa."

Kanta a qasa tace "Wallahi Baffah bansan sanda nake harzuqa ba idan Innah tayi wani abun nakan ji ciwo mai yawa a zuciyata ace wai Aunty Asama d'iyar tace fa itama meyasa zata dinga yi mata haka d'in kamar basu had'a jini ba."

Kai ya jinjina yace "Duk na gane halin da kike shiga amma ki sani duk irin ciwon da zuciyar taki take miki dolen ki ki qasqantar da kanki a wajen ta domin kuwa haifar ki tayi Annabin rahma (saw) cewa yayi iyaye koda ba musulmai bane kada ka kuskura kayi musu ihu ko tsawa ka lallashe su ka lallame su kayi musu biyayya balle ke taki mahaifiyar musulma mai bin umarnin ubangiji kawai wani son zuciya ne ke damun ta wanda addua ya kamata muyi mata ba wannan halin ba."

Kai ta gyad'a tace "In shaa Allahu zan kula Baffah nagode."

Dariya yayi yace "Hajaaratu ayar Allah ke kam bakin ki baya gajiya da godiya tashi kije ki bata haquri Allah yayi miki albarka."

"Amin." Suka had'a baki wajen amsawa sannan tamiqe ta fice.

Tana fita Mommah tace "Baffah nifa cewa nayi inda Innahma zata amince dana tafi da Hajaarah nafi son tayi aure kusa dani nima ace ina da 'yar uwa dai a kusa dani kuma tunda bata samu mijin ba ta koma makaranta kawai zuwa sanda Allah zai fito mata da mijin."

Murmushi yayi yace "Gaskiya shawara ce mai kyau wannan amma nifa Innar ku nake ji kinsan halin ta kuma zata ga Hajaarah ba tawa bace balle nace zan mata iko da ita ga kuma yanda kuke amma dai bari Abdulhameed yazo shi ya iya da ita wataqila idan yayi mata magana ta haqura ta baku ita."

Ajiyar zuciya tayi tace "Toh Allah yasa ta amince d'in."

Da amin ya amsa suka cigaba da tattaunawa abinsu cikin raha da jin dad'in yanayin.

6angaren Innah Jumah da Hajaarah kuwa tana fita tayi d'akinta,tana zaune gefe gadon ta mai lumtsumemiyar katifa wadda duk aikin Asama ne wadda tasa Basheer yayi musu itama Hajaaran sai taje ta zauna gefen ta tana murmushi ganin yanda take ta wani kauda kai da murtuke fuska wai ita a dole fushi take.

A hankali ta dafa cinyar ta tana sake fad'ad'a murmushin ta tace "Haba Innah ta yau kuma dani ayan ki kike fushi haba Innata na tuba nabi Allah na biki na daina Allah kiyi haquri."

A fusace ta juyo tace "Qarya kike inda ace baza kiyi ba da baki yi amma wai akan Asama kike min wannan halin ko Aya?" Ta qarashe maganar da nuna jin zafin abun har tana nuna kanta da hannunta.

Kai Hajaarah ta girgiza sannan cikin kwantar da murya tace "Aa Innah ba akanta nake miki ba akan zumuncin Allah nake miki Allah shi yace ayi zumunci wallahi raina na 6aci a duk sanda naga kina tozarta Aunty Asma'u da yaranta ko Yaya Abdulhameed domin basu cancanci haka d'in daga gareki in aka duba irin tsantsar so dakulawar dakika samu daga mahaifiyar su,Innah ki tuna fa Innah Habi harta koma ga mahaliccinta irin son da take miki saboda son da take miki nema tace ki auri mijin ta a lokacin da ta tabbatar da ita tata ta qare kuma na tabbatar koda tana da lafiyar ma da ace tana da yanda zata yi wallahi sai ta kawhe auren ta ta baki mijin don kawai ki samu kwanciyar hankali amma meyasa Innah 'ya 'yan ta baza su samu farin ciki da nutsuwa daga gareki ba irin yanda mahaifiyar su tayi miki?" Tayi shiru tana kallon ta yanda jikinta yayi sanyi alamun nasihar na shigar ta.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now