Part 69

242 19 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!





P1️⃣0️⃣3️⃣
A ranar suka tattara suka koma dukan su don dole dai aka yiwa Mommah saida ta tafi da ta kafe sai taga anyi auren nan saida Iyya ta rantse mata akan ta yarda zata auri Abbuh sannan ta haqura ta tafi.

Triplet kawai aka bari a wajen Iyyah don sunce indai Ansaar bai tafi ba suma baza su tafi ba hadin kan ya motsa,shi kuma yace bazai tafi yabar Iyyar saba har sai ranar da aka d'aura auren ta sannan zasu tafi tare.

Gida yai tsit duk matan gidan jikin a bala'in sanyaye yake kowacce saita juya ta juya sai ta antayowa Iya Rammah zagi da tsinuwa don itace silar komai ita ta asassa komai duk da mazajen su ba wai sun yi musu hukunci bane saidai guilty tada tabaibaye su.

Larai ta shiga sashen Iyyah suna zaune da Little tana mata tsifa tana ta kuka don yawan gashinta bata kuma son a tab'a mata shi,da farko rab'e rab'e ta dinga yi saida Iyyah tace ta shiga mana sannan ta iya shiga.

Ansaar baya nan sai su Aseep dake can d'ayan gefen suna ludo ta saci kallon su sannan ta zauna kusa da Iyyah a ladabce ta shiga gaishe ta.

Ba wani mamaki ta amsa don zuwa yanzu ta lura girma na musamman ake bata a gidan tun daga manya har yaran su banda yaran d'akin Iya Rammah wadanda su gani suke kamar abinda ya samu mahaifiyar su kwana da kwana a tsakiyar gari itace sila don haka suka tsane bama kamar Auwalu da shi ya cigaba da cin alwashin ko uwarsa bata ga bayan su ba shi zaiga bayan su.

Sukayi gum daga ita har Laran don ita Iyyah ba sabawa tayi da magana dasu ba tun suna qananun su haka zalika ba abinda ke shiga tsakanin su inba rashin kunyar su ce ta motsa ba sukayi mata don haka yanzu ma sai take ji ba abinda zata ce da ita kuma.

Little nata kuka hakan yasa Larai miqa hannu tana cewa cikin lallashi "Zo Saratu na goya ki rabu da Iyyah kinji."

Cikin zabura kamar wanda aka tsikara yayo kansu yana cewa cikin tsawa "Karki tab'a ta karki yarda ki d'auke ta."

Da sauri ta janye hannun ta jikin ta na rawa idon ta har ya tara ruwa bai kula ba ya nuna ta da yatsa yace "Na rantse da Allah da wasa kika sake kika tab'a min d'iya saina balla ki ba abinda ya had'a ku karki yarda ba wai kinga na barki kin shigo ba hakan ba yana nufin zan yarda da duk wani shashanci ba kuma.."

Da sauri Iyyah tace "Ya isa mana Ansaar wanda ya kula naka ai yana son ka ne."

Da sauri cikin zafin rai yace "Duk wanda yace baya son ka ko daga baya ya dawo yace yana sonka qarya yake ki tuna Larai da uwarta sunfi kowa qinmu a gidan nan taya zamu yarda da ita yanzu muji a ranmu ba cutar damu tazo yi ba."

Kuka sosai ta fashe dashi tana girgiza kanta tana cewa "Wallahi ba cutar ku zanyi ba wallahi da gske nake wallahi..."

Wata uwar tsawa Aseep ya buga mata yana cewa "Ke dalla get out kin cikama mutane kunne da wata banzar muryar ki er qauye kawai qazama get out."

Ba qaramin tsorata tayi da yanayin Aseep ba don shi dama haka kurum ma mai shan mur ne balle kuma an tab'o shi da gudu ta fice daga sashen tana kuka tayi waje.

Kamar had'in baki duk su ukun suka ja tsaki Aseep ya qara da "Useless girl kawai."

Iyyah kallon su kawai take cike da takaici za ace ko mamaki har suka gama tsakin da maganar,duk sun wani kimshe sun sha mur in badon banbancin kayan jikin su bama da da qyar ta gane Ansaar a cikinsu  tace "Kun gama?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now