Part 51

248 23 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel


P7️⃣2️⃣-7️⃣3️⃣
Da sauri ya juyo yana mamakin jin kamar fa muryar Ansaar yaji.

Aiko dai shi ya gani da sauri ya juyo sosai ya taho wajen sa shima a kunyace ya qarasa inda yake ya durqusa ya soma gaishe shi sai kawai ya miqo masa hannu yana cewa "Mu gaisa mana Ansaar bismillah."

Qin kama hannun yayi cike da girmamawa,sai ya maida yana amsa gaisuwarsa,ya zauna a gefen dakalin qofar gidan yana tambayar sa ya yake kuma ya birnin ya abubuwa suka tafi.

Nan ya bashi labarin abinda ya faru a gurguje dama abinda ya dawo dashi yanzu.

Kai ya gyad'a yace "Gaskiya ne Allah yayi maka albarka yanzu kuma zan baka addu'o'i saboda maqiya da mahassada Allah ya qara kare ka kaji."

Da amin ya amsa sannan M Ladan yace yana zuwa,ya shiga cikin gida bai jima ba ya dawo da wasu takardu ya miqa masa yana cewa "In ka riqe wad'annan addu'o'in da iznin Allah ba mutum ba ko aljan bai isa cutar dakai ba."

Jinjina kai yayi yace "Nagode Baba Allah ya saka da alkhairi ya qara girma."

Da amin ya amsa masa ya sake masa nasiha akan zama lafiya da kowa da girman haquri sannan duk Ansaar naji da zai tafi ya bashi tsarabar daya kawo masa aiko yaji dad'i sosai don tabbas yana da buqatar duk abinda ya kawo masa d'in nan yana ta murna ya tafi ya barshi shi kansa yaji dad'in yanda yaga M Ladan d'in yaji dad'i ko ba komai burin Saratu kenan kullum mahaifinta ya zama cikin farin ciki shiko yayi alqawarin duk yanda zaiyi zaiyi qoqarin sashi farinciki ko yaya yake.

Haka ya koma ya tadda Iyyah zaune tana jiran dawowar sa amma Saratu tuni tayi bacci, ya zauna suka cigaba da hirar su abin gwanin sha'awa.

Iya Rammah kuwa tana dawowa Larai ta fesa mata Ansaar ya dawo da kuma irin yanda yayi kyau da kayan da ya zo da su ta qare da "Wai Rammah dama haka Ansaar yake da kyau."

Qirjin tane ya bada damm don tunda har Larai ta fad'i wannan maganar akwai dalili meyasa zuciyar ta zata saqa mata har taga kyansa dole tayi wa tufkar hanci tun kafin abun ya damalmale mata don haka a fusace tace "Uban kyau yake dashi ba kyau ba ashe baki da hankali vansani va shegen kike cewa yana da kyau?"

Kame kame ta fara da farko amma sai da taga babu amfani sai kawai ta fito a mutum tace "Nifa gaskiya tun kan ya auri Saro daman naji ina sonsa kawai yanda aketa aibata shine ya sa nima na dinga dannewa amma gaskiya yanzu nakai geji."

Hannu Iya Rammah ta shiga tafawa tana salallami kan ta fashe da kuka tana fad'in "Na shiga uku,Larai kece kike furta kina son shege mara asali?ashe kema mutuwar kike son yi kenan innalillashi haba Larai ki rasa wanda zaki d'auko kice kina so sai wannan shegen d'an fasiqa?"

Larai ta turo baki gaba tana cewa "Nifa fad'a miki kawai nayi kisan abun yi."

Gyad'a kai tayi tana cewa "Ah dole ne wallahi na nema miki magani ba banza ba haka kawai rana tsaka kice kina son shegen can na rantse da Allah saidai asiri ko ma tsafi."

Murgud'a baki tayi tace "In ma asirin ne dai ke kika sani nidai ga abinda nace dake." Tana gama maganar ta miqe tabar wajen.

Iya Rammah da daman kukan munfurcine sai ta goge idonta tana fad'in "na shiga uku ni Rammah ya komai yake neman dagule min ne?Hama zan komawa goben nan kafin a samu babbar matsala kuwa."

Haka ta dinga safa da marwa a d'akinta ta saqa ta kwance har dare ya raba bata samu mafitar data wuce da sassafe ta komawa Hama da matsalar taba ita sai a yanzun ma ta tuna sanda suka ce bokan yace mata akwai abinda zata yi wanda in bata yi shiba asirin bazai kama su Iyyah ba kuma bai fad'a mata menene shi ba bai gaya mata yanda zata yi ba gashi har Allah ya rage mata wahala ya d'auke Saratu sauran wannan tsinanniyar,haka ta qudurcewa ranta tabbas abinda zata fara tambayar shi kenan idan sunje.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now