Part 52

229 26 1
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel

P7️⃣4️⃣-7️⃣5️⃣
Yana tafe yana tunanin abinda Allah kuma ya jarabce shi dashi "Wai Larai." Ya fad'a a karo na ba adadi inya tuna da yanda yaji zancen su jiya da daddare da kuma yanda yau tayi masa.

A haka ya qarasa cikin kano yana zuwa kasuwa ya nemi Baba ya gaya masa bai san gidan alhaji ba ko za a kwatanta masa.

Salim na zaune yace "Aa muje na raka ka ina son tabbatarwa wai shin alhaji da gaske yake taimakon ka zaiyi ko kuwa yana da manufa."

Baba yace a d'an dake duk da shima zuciyar sa nata bashi ba haka kawai alhajin ke son taimakon yaron ba akwai dalili "Wacce irin manufa zaka tsorata shi haka kawai."

Yana dariya yace "Haba Baba don Allah kayi tunani fa tun yaushe Nasiru yake binsa da takardunsa na NCE akan yana so yayi B8 amma ya hana shi ko asi qarshe ma yayi masa kaca kaca yace ba don shi ya tara arziqin sa ba amma dubi fa daga ganin yaro yace zai taimaka masa."

Baba yai murmushi yace "Baku san in Allah yaso tallafin ka ta hannun wani komai wayonsa sai yasa yayi ba,wallahi tunda naga yaron nan naji a raina a babban al'amari a tare dashi saidai yana buqatar addua a rayuwar sa matuqa da gaske shiyasa na qudurce a raina zan dinga yi masa yanzu kasa na fad'a masa don haka kuje ku dawo zanyi magana dakai kai Ansaar."

Da to ya amsa yana mamakin tsohon suka fice,suna tafe suna hira da Salim kamar abokai,Amma a zahiri Salim ya girmewa Ansaar nesa ba kusa ba kuwa don a qallah ya bashi wata shekaru goma a lalace.

Haka suka hau napep ya kaisu har gidan alhaji.

Yana shirin fita don har zai hau mota maigadi yayi hanzarin bud'e musu qofa yace su shiga ga alhajin nan fita zaiyi.

Yana ganin su ya soma fara'a don shi mutum ne mai yawan fara'a ga mutane saidai ba mai yawan bayarwa bane in kaga ya bada to da dalili ne babba sai kuma idan yana sonka a ransa to babu abinda bazai maka ba koda kuwa babu abinda kake masa kuma ko baka da buqata.

Yana son Salim saidai bai cika masa alheri ba kamar yanda ya saba Nasiru d'an uwan Salim ne Allah bai had'a jinin su ba ko misqala zarratin ko shagon yaje ya ganshi zai baiwa kowa alheri amma vanda shi haka nan duk taimakon da zai nema indai bata wajen Salim ko Baba yabi ba bazai masa ba wannan tasa Nasiru ke matuqar qullace da alhajin yawancin yaran shagon ma dake d'ibga sata a koresu dasa hannunsa shine zai d'auki yaro ya bashi kwangilar satar in yayo ya gutsira masa ya kore shi tare da tsorata shi.

Asali yaqi Ansaar ne saboda tunda ya ganshi yaga alamun sanyi da cikakkiyar kamala a tare dashi yako tabbatar ba ta yanda za'ayi mai wannan sifa indai akwai su a halayyar sa ya yarda ayi cuta dashi shiyasa yaso daqile zancen d'aukar sa tun asali don har ya gama had'a harqallar sa da wani yaro d'an dako Ansaar ya bullo kuma akayi sa'a Salim da babansu suka yi na'am dashi shiyasa yake matuqar jin haushin sa balle da zancen taimakon da alhajin yace zaiyi masa yakai gareshi sunsha zagi qunduma qunduma daga shi har alhaji da la'ana kala kala kai kace da kud'in sa Alhaji zai taimaki Ansaar.

Durqusawa suka yi suka gaishe shi yace "Da na yi zaton vaza kazo ba yau?"

Ansaar yana dariya yace "Aa an d'an samu matsalar mota ne a hanya shiyasa."

Ya gyad'a kai yace yana kallon salim "Kun tab'a gwada shi kuwa?"

Salim ya gyad'a kai yana shafa shi yace "In sha Allahu babu wata matsala Alhaji."

QADDARA CE SILA حيث تعيش القصص. اكتشف الآن