30 Qaddara ce sila

302 24 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!





*Jummai ta group d'in Khairun Nisaa wannan page d'in naki ne nagode sosai da qauna saqon ki kuma ya tadda ni ina matuqar godiya lots of luv*

Page 40-41
•••Tun daga ranar wata irin shaquwa ta sake shiga tsakanin su abin kamar almara duk da mahaifin ta yasha ganin su amma sai ya nuna sam bai san meke faruwa ba tun in ya gansu yana cewa ta tafi shi yazo suyi karatu har ya koma saidai yace musu su bari su gama karatu tukunna shida kansa yake tura ta bayan sun gama d'in.

Wannan damar da suka samu ita ta fayyace irin soyayyar da sukewa juna Ansaar kuma ya dinga jin shid'in mai sa'a ne duk da kasancewar yanda ya taso da qyama ta al'umma amma da ke Allah na sonshi sai ya azurta shi da soyayyar kyakkyawar mace mai kyawawan d'abi'u kuma a kodayaushe wannan ke sashi tsananin farin ciki.

A 6angaren Iyyar sa kam duk da ya gaya mata M.Ladan bai ta6a hana shi tsayawa da Saro ba amma hankalin ta bai gama kwanciya ba tasan lallai akwai babban al'amarin da zai biyo baya idan maganar ta fasu kowa yaji don haka kulluk cikin ja masa kunne take da kashedin yayi a hankali yabi komai sannu.

A wajen sa jin ta kawai yake don yanda yake jin son Saratunsa ya shirya tunkarar kowanne irin qalubale matuqar zai same tan.

Watanni suka gangara ganin suna sake shaquwa yasa da daddare bayan sun kammala karatun dare M.Ladan ya gyara zama yace "Ansaar dama akwai maganar da nake son muyi dakai a 'yan kwanakin nan saidai ana ta samun matsala uzururruka na hanani yin ta dakai."

Ansaar ya nutsu yana jin sa shi kuma ya d'ora "Na lura watannin nan kaine kad'ai Saro ta za6a take kulawa ba kamar baya ba da take da yawan manema don haka idan har da gaske son ta kake kuma neman auren ta kake ina buqatar ganin manyan ka."

Da matuqar farin ciki ya amsa da "Toh Baba zan fad'awa Iyyah in shaa Allahu zasu zo."

D'an guntun murmushi yayi sannan yace "Amma ina son ka gaya mata kafin ta turo kowa tazo muyi magana nida ita akwai muhimmiyar maganar da zamuyi da itan."

Da to ya amsa shi cike da tsantsar farin ciki kuma yana miqewa kan sa tsaye gidan Hinde ya fara nufa don gani yake ita tafi kowa cancanta ta soma jin wannan kyakkyawan labarin.

Yaci sa'a yana zuwa mijin Hinden na niyyar shiga gidan don haka bai bari kowa ya gansu ba ya shigar dashi 6angaren nasu sannan ya dawo ainihin cikin gidan don zuwa wajen mahaifiyar sa kuma ya basu damar zantawa da juna.

Tana zaune tana bawa Hadiza koko suka shiga yanda taga Ansaar d'in cikin tsananin farinciki yasa ta itama washe baki tana fad'in "Hala autan Iyyah ta samu ne irin wannan farin ciki haka?."

Dariya yayi yana zama yace "Kedai bari ai babbar samuwa ce."

Tana jin hakan ta saba Hadiza a baya wadda ta gama shan kokon tace "Bani nasha d'an tilon qanina."

Nan ya labarta mata abinda ya faru ai tama fishi farin ciki kuma take ta d'auko mayafi tana fad'in "Aa wannan albishir dani za'ayiwa Iyyah shi bazai wuce niba."

Suna fitowa sukayi kaci6is da mijin nata yana niyyar shiga cikin d'oki tace "Mun tafi wajen Iyyah sai mun dawo."

Da kallo kawai ya bita da mamakin farin cikin su haka zalika ita kanta Matar tasa wadda zuwa yanzu ya gama sanin irin qaunar da takewa goggon nata da d'anta mamaki take bashi amma sai ya shanye abinsa ya shige yana fatan dawowar su lafiya.

Ba wanda yasan da shigar su gidan don duk sun shige d'aki don haka salin alin suka shiga sashen Iyyar.

Tana zaune tsakar d'akin da rogo gabanta tana fere shi suka shiga murya qasa sosai suke magana don kar wani ma yaji Ansaar na daga bakin qofar yana kallon duk abinda zai wakana daga bakin qofar zuwa jikin dangar tasu wanda a wannan lokacin baya tsammanin kowa a wajen ko don macizan dake yawo a tsakanin nan kamar kiyasai saboda damina.

Iyyar Ansaar dai tunda taji batun ta fashe da kuka sosai wanda daga Hinde har Ansaar mamaki ya hana su magana sai kallo kawai.

Ta jima tana yin sa kafin ta samu da qyar ta d'ago tana kallon sa tace "Tabbas nafi kowa farin ciki Ansaar da wannan daddad'an labarin domin kuwa ko babu komai nasan kai baza kayi rayuwar qunci da rashin 'yancin aure ba irina zahiri zan ji matuqar dad'i naga ranar auren ka kuma wannan shine cikar buri na Allah na gode maka." Ta qarasa da sharar hawaye.

Duk sai ta karyar musu da zuciya suka tsaya suna kallon ta cike da tausayi Ansaar kam wani irin abubuwa ne suka dinga cakud'uwa a zuciyar sa ya rasa tausayin ne yafi rinjaye ko farin ciki.

Bayan shiru na wani lokaci Hinde tace "Iyyah yanzu yaushe zakije?"

Shiru ta d'anyi sannan tace "Nan da gobe ma da magriba sai inje."

Da murna duk suka amsa "Allah ya kaimu."

Haka suka d'an ta6a hira duk akan lamarin auren ne kafin daga bisani Hinde tayi musu sallama ta fice ba tare data bari koda mahaifiyar ta tasan da zuwan ta gidan ba.

*ASALIN MALLAM LADAN*
Muhammad Bashir Ado shine asalin sunan haifaffen qauyen nasu Ansaar ne qarqashin qaramar hukumar gezawa asalin mahaifinsa M.Ado kenan.

Mahaifinsa M.Ado shine ladani a wannan lokacin kuma kamar shima a zamanin sa Mallam Ladan ake kiransa wanda kamar gadon gidan sune ladancin duk wanda ya taso babban d'a shine ke gadon mahaifinsa haka abin ya gangaro har kan Muhammad Bashir wanda yake babban d'a ga Mallam Ladan.

Tun yana yaro yayi karatu mai zurfi na addini haka nan Bashir nagartaccen yarone mai haquri da sanin ya kamata.

Mahaifiyarsa Saratu shi kad'ai ta haifa ta rasu don haka a hannun kishiyarta ya taso saidai kara da tsananin zaman lafiya irin na mutanen da saida ya girma sosai sannan ya gane ba itace ta haife shiba.

Ya auri matar sa ta farko Hansatu yanada shekaru sha bakwai a duniya wanda shekarar su uku kafin suka samu haihuwa inda ta haifi d'anta na fari Anas daga nan haihuwar ta bud'e sosai duk shekara bayan Anas ta haifi Nafi sai Bukar sai Saratu wadda suke kira da saro sai kuwa autan su Imamu.

Sai matar sa ta biyu Karime itama ta haifi yaranta hud'u Ada'u,Ashiru,Azima da Jafaru.

Zaman gidan M.Ladan Bashir zamane kadaran kadahan kasancewar sa tsayayye a gidansa don haka bai bada qofar da za'ayi masa shiririta ba saidai suyi bai sani ba.

Tsakanin su dai ta ciki na ciki ne don haka zaman gashi nan dai saidai a cakud'a kawai.

Haka nan ya auro matarsa ta uku Indo wadda ita bata jima ba sanadin haihuwa Allah yayi mata rasuwa itada abinda ta haifa tun daga nan kuma bai sake aure va sai ya maida hankalin sa kan iyalansa mazan da matan kowannen su yana bashi kyakkyawar kulawa musamman kan harkar karatunsu.

Wannan dalilin yasa kaf yaransa babu wanda baiyi sauka ba a shekara goma goma kad'an ne suke haura goman kafin suyi ta.

Saidai 6angaren matan Hansai Allah yayi ta azababbiya duk da kasantuwar ta cikakkiyar bafulatana ta ruga saidai sam babu kara ko sassauci a sabgar ta in badon jajircewar mijin ta ba da zata iya addabar kowa a garin baka gidan su kad'ai ba.

Karime kam kadaran kadahan ce bata cika masifa ba amma in ka ta6o ta babu sauki don tabbas zaka ji a jikinka fad'anta kamar fad'an kurma baya qarewa har sai hukuma wataran ta shiga ciki ake samun salama.

     Wannan kenan!!!

Ga yaran suma kowannen su akwai inda ya d'iba kuma kowannen su akwai sabgar d yake yi saidai dukkan yaran babu wanda ya kwashi uwar sa zam kamar Bukar marabar sa da Hansai dai ita mace ce shi ko namiji amma wannan halin nata na zafi da azaba ya kwashe shi tsab harda dad'i akai.




I hope y'all enjoy this page and please a qara yawan comments hakan zai qara mini qwarin gwiwar rubutun sosai thanks y'all lots of love.

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now