Part 43

253 19 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel



P5️⃣8️⃣-5️⃣9️⃣
Haka rayuwar su ta cigaba da gangarawa har sukayi hutun first semester d'insu wanda Abbuh yace kada suzo su zasu je musu.

Gabad'aya gidan aka had'u harda su Hajaaratu en abuja da yaransu Nusaiba,Hamida da Ayyan suka d'unguma suka tafi.

Aiko sun sha hutu sun kuma ji dad'in hutun su.

A wannan hutun ne Hajaaratu da Maimuna da Hamdiyyah suka fita don yin siyayya a wani super market dake kusa da masaukin su.

Suna zagayawa Hajaarah da Maimuna na hira ita ko Hamdiyyah tura keken kawai take tana duba list d'in da sukayo tana zuba kayan a ciki bata ankara ba taji gwarab tayi karo da mutum da sauri ta dafa goshin ta tana fad'in "Wash."

Da sauri shi kuma ya juyo yana fad'in "Oh my God am so..."

Da sauri kuma a fusace ta d'ago kanta tana kallon sa tace "Meye haka?nan d'in ma biyo ni kayi."

Maimakon ya qarasa maganar sa sai ya had'iye yana dariya yace "Ko dai kika biyo ni."

Yanda yayi maganar da d'an rainin wayo harda kama qugu ya qara bata haushi a fusace tace "Stalker."

Zaro ido yayi yana kallonta ta wuce ya maimaita "Stalker?Ni?" Ya fad'a kamar tana gabansa ita yake tambaya harda nuna kansa.

Taji abinda yace don haka ta juyo harda murgud'a baki tace "Yes you."

Murmushi yayi don ta masa bala'in kyau yace "Bakomai zan kama ki ne zaki zo hannuna."

Sake murgud'a masa baki tayi ta tura keken zuwa wajen masu biya,saida aka gama lissafawa tana niyyar miqa card d'inta y miqa nasa yace a cira harda na kayan daya siya.

A fusace ta juyo tace "Bama buqata."

Bai ko kalli inda take ba ya karbi card dinsa ya wuce abinsa,a hasale ta bishi tana miqa masa kud'i tana fad'in "Nace maka bama buqata ungo kud'inka."

Saida suka kusan fita Maimuna dake biye da ita ta janyo ta tana fad'in "Meye haka Diyyah."

Da sauri ya juyo yana wani murmushi yace "Ba don ke na biya ba don wannan kyakkyawar fulawar mai yawan murmushi da kyau na biya." Ya qarasa yana kallon Maimuna dake murmushin ta mai kyau.

Cikin bazata taji wani irin abu ya tokare mata maqogaro tace lokacin da ya juya ya soma tafiya "Sai ka bari inta siya nata sai ka biya wannan namu ne."

Yana dariyar sa mai kyau ya juyo yace "In queen ta amince da hakan zan karbi kud'in hannun ki in bata amince ba kuma shikenan." Ya juya ga Maimuna duk da suna nesa da juna yayi motsi da lebensa kamar yana tambayar ta ita kuma cikin murmushi ta girgiza kanta tana masa alamu da ido kan ya kalli Hamdiyyah.

Yanda yaga ta sake qufula ya sai ya qara himma harda wani kashe ido yace yana wani shagwab'ewa tare da tab'e baki "Ohhhn queen bata yarda ba sorry."

Ya juya ya cigaba da tafiyarsa,ita kuma Maimunan tabi bayansa da murmushi cike da wani irin mugun haushin su gabad'aya ta fizge kafad'ar ta da Maimuna ta kama ta fice daga wajen gabad'aya.

Hajaarah da Maimuna suka kwashe da dariya sannan Hajaarah tace "Kinyi qoqari wajen taya shi tunzura ta koda bai gaya miki komai ba."

Dariya tayi tace "Nasan Hamdiyyah sosai inda ace bata jin sa a ranta to da ko kula shi baza tayi ba duk kuwa da yanda zai riqa binta qila ta kasa fahimtar da kanta ne akwai birbishin sonsa a ranta yanzu kalli yanda tayi fa da alamun kishi da jin haushi to bari muje mu tadda ta zakiji ta musa abinda na gaya miki."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now