Part 73

312 17 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!


P1️⃣0️⃣7️⃣
Gyad'a kai yayi yace "Shikenan Allah ya taimaka ya baka sa'ar gyaratan."

Duk suka amsa da amin sannan suka wuce gida kai tsaye yayin da su Mahmoud da Isma'il suma suka wuce nasu gidajen.

A falo suka tadda su Mommah suna hira suka zauna suna maida yanda lamura suka kasance musu a yau anan ne kuma suka basu labarin Lubnah da amincewar da Areep yayi zai aure ta.

Mommah tace "Yarinyar nan mai mutunci ce ne?"

Had'a ido sukayi duk su ukun sannan suka maida hankalin su kan Mommah Ansaar ya bude baki zaiyi magana Areep ya riga shi "Mai mutunci ce Mommah in sha Allah babu wata matsala don koda na zauna a gidan su ma ban samu matsala da ita ba."

Sakin baki kawai Ansaar yayi yana kallon sa yanda ya rainawa Mommahn hankali ya canza kansa kuma alamu sun nuna ta yarda yana ta qoqarin yayi magana amma Areep yayi kicin kicin ya hana shi cewa komai dole ya qyale shi yasan ba gane su ake ba tsoro yake ji kada Lubna ta tafka wata ta'asar Mommah tace shine ya bada shaida akanta amma dolen sa yayi shiru kawai.

Iyyah ce tace tana kallon Ansaar "Yaushe zamu je gezawa ne?"

Gyara zaman sa yayi yana kallon ta yace "Next week ko?"

Kai ta gyad'a tace "Allah ya kaimu nima abinda ke raina kenan."

Ansaar ya amsa da "Allah ya nuna mana da rai da lafiya."

Ta amsa da amin sannan ta miqe tana ce musu bari ta shiga d'aki akwai abinda zatayi,harta wuce ta dawo ta kira Ansaar suka shige d'aki,abinda kullum ke bawa Mommah mamaki ko komai iri d'aya suka saka bata kasa gane waye Ansaar d'in don akwai sanda hatta agogon su iri d'aya ne ta kira Ansaar Aseep ya amsa ya bita tana juyowa ta zuba masa ido na en sekwanni kafin tayi murmushi tace "Ansaar na kira ba kai ba."

A ranar kowa ya dinga mamaki Mommah tai ta mata nacin kan ta gaya mata yanda take iya banbance yaron ta da su Aseep saidai tayi dariya tace "Ansaar ko inuwar sa na gani nasan tasa ce bazai b'ace min ba ko a cikin irin sa dubu yake."

Ta dai haqiqance qaunar ce da take masa ta daban yasa komai nasa ya zame mata jiki tasan waye shi ciki d bai.

Suna nan zaune Abbuh ya dawo bayan magriba,hira ta sake b'arkewa anan kuma Mommah tace suma zasu je gumel satin da su Iyyah zasu tafi gezawa nan yace saidai in gabad'aya suje gangare sannan su tafi gumel daga baya,duk suka amince da hakan wajen qarfe tara kowa ya dare mazan suka tafi d'akin su,Salmah da little suka tafi nasu d'akin Iyyah ma ta tafi Abbuh da Mommah dake dakin sa wannan ranar suma suka tafi nasu d'akin.

Wanka ta fara shiga tayo sannan ta fito yana zaune gefen gadon yana danne danne a laptop dinsa da alamu dai aiki yake yi ta zauna gaban madubi tana kallon sa ta ciki tace "Abbuh."

"Uhmm." Ya amsa ba tare da ya kalle taba.

Ta sake cewa "Wata shawara ce dani Allah yasa zata karb'u."

Dariya yayi ya ture laptop d'in tare da maida hankalin sa kanta yace "Shawarar ki bata kwantai Mommahn yara."

Murmushi tayi wanda ya masa kyau sosai tace "Inaga tunda Iyyan Ansaar ta samu abinda ta samu fiye da abinda muke tsammanin zata samu a qasar nan me zai hana a maido ta nan tayi waec in taci sai kawai a maidata can tayi Msc d'inta idan kuma bata ci ba saita koma can ta cigaba wata shekarar ta sake yi tunda kaga girma take sake yi ko ya ka gani?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now