Part 13 Qaddara ce sila

288 20 0
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

*Yan uwa ina godiya bisa ga addu'o'i da muka samu na rashin da mukayi na Baby Nabeel nagode Allah ya bar zumunci.*

*'''Duba kuma da wata mai alfarma da muke shirin shiga na Ramadan zan dakatar da typing har sai bayan sallah idan Allah ya kaimu da rai da lafiya dafatan Allah yasa muyi ibada kar6a66iya ya samu cikin entattun bayi ya ara mana rayukan muga na bad'in badada'''*

'''Ku sani ZahraArkel nayin ku irin sosai d'innan yanda ya kamata fa ana mugun Manne fans.'''

                     _Page 13_

●●●●Ta fito tana ta haskawa amma bata ga kowa ba ciki ciki take magana don kar 'yan sauran d'akunan musamman na kishiyarta su ji tana qunduma ashariya tare da tsinewa mai musu la6en da son jin abinda zasu tattauna.

Haka ta shige d'aki suka sake danno qofa suka rufe amma duk yanda Sadiya taso su cigaba da zancen Iya Rammah fafur taqi dole ita ma ta qyale ta suka shiga wata hirar ta daban.

Washegari dai aka d'aure aure aka zarce da yinin biki zuwa yamma biki ya qare aka miqa amarya gidan mijinta wanda aka za6i mutum bibiyu daga 6angaren iyayenta hud'u kenan amma a lissafin babu Iyyaah,daman ita bata sa rai ba ta dai sa a ranta zata je taga d'akin amarya bayan an kaita.

Daidai za a tafi da Hinde ta fito tana kallon su aka fito da ita daga d'akin Iya Rammah tunda itace babba a kaf gidan anan akewa duk yarinyar da aka yiwa aure fad'a nan iyaye maza suke shiga haka zalika da sun gama iyaye mata su shiga ita kam uwa kallo ne nata.

Da da farko taso yin gardama tace a akaita d'akin uwar ta ko d'akin Aminatu Iya Larai tace tana riqe ha6a "Yanzu ke don Allah Rammah wanda yake yi ne zai hana wani ai wallahi Amina saidai ta tunzura yarinyar nan ta kaso mata aure tun ba'a kaita ba."

Baba Ladi wadda itama qanwa gmce ga mahaifin su Amina tace "Hnm itama dai Rammar fad'e take yo mu mahaukatan ina ne ma da zamu kai yarinya mai auren sunnah d'akin wannan mai yawon ta zubar d'in."

Asabaru matar Sama'ila ta kar6e "Ai tana sani itama iya Rammar fa tsokana ce ta sata fad'in haka."

Duk maganganun nan da ake yi Aminatu baiwar Allah bata san me ake ciki ba haka nan wannan maganganun sune suka farantawa Iya Rammah rai harta yarda aka shigar da Hinde d'akinta duk da yanda take turjewa itama tana nuna bata so shiga itama amma haka dai suka tura ta aka zaunar da ita badon taso ba sai don dole.

Ana fitowa da ita ta hangi tsayuwarsu a qofar d'akinsu don haka ta fizge daga wajen yayar mahaifiyar ta ta tafi da sauri ta rumgume ta tana kuka sosai irin na al'adar hausa fulani.

Salatin da suka had'a baki wajen yi ne gabad'aya matan dake wajen ya tsorata Hinde da Amina sukayi saurin sakin juna suna kallon matan da tsananin mamakin menene ya sanya su salati haka?.

A fusace qanwar mahaifiyar Hinde taje ta janye ta tare da d'aga hannu da niyyar kwad'a mata mari amma saita fasa ta zundumo wata ashariya ta auna mata sannan tace "Saboda ke dabba ce mahaukaciya baki san inda yake miki ciwo ba shine zaki je ki had'a jikin ki mai daraja wanda bai ta6a gogar namiji ba kuma wanda yanzu aka d'aura miki aure da jikin fasiqa mazinaciya harda wannan d'an iskan shegen yaron?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now