QADDARA CE SILA!

512 43 0
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya* 

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel

🅿️3️⃣
A hankali d'alibai suka dinga zuwa suna taruwa har ajin ya cika taf da d'alibai wanda akasarinsu maza ne kowannen su wasa yake da abokinsa banda Ansaar dake can gefe ya raku6e yana kallonsu a haka mallamin ajin nasu ya dawo ya same su.

Tsawa ya buga musu kowannen su ya nutsu ya koma wajen zaman sa banda Ansaar da har wannan lokacin yana kusurwar ajin a zaune.

Cikin taushin murya mallamin yace "Kaii Ansaar baza ka tashi ka koma wajen zaman ka bane?"

Idon sa ne yayi qwal qwal ya juya yana kallon kujerar da nan ne mallamin ya sashi,Awwalu da Hadi sune a kujerar sai shi na uku suna had'a ido da Awwalu ya cije gefen le6ensa alamun zai daku idan ya dawo.

Ganin yanda yake kallon sune ya kasa magana mallamin yace "Tashi ka koma wajen ka."

Jiki a salu6e ya miqe ya koma wajen da suka bashu rata suka matse kansu saboda wai kada su ra6e shi ko su ta6a shi.

Haka yayi kiran suna da yake kuma shine da period na farko sai kawai ya shiga darasi sosai.

Ansaar na d'aya daga cikin d'alibai na gaba gaba da suke gane karatu sosai kuma suke da qoqari da fahimtar karatu sosai wannan dalilin ne yasa mallamai da d'an yawa suke kauda kansu daga aibun sa suke sonsa suna kuma qarfafa masa gwiwa akan karatun sa,don da yawa kayan karatun ma kyauta head master ke bashi dukkan lokacin daya buqata.

Wannan shi ya qara rura wutar tsana da tsangwama ga Ansaar daga da yawa daga cikin d'aliban.

Anyi karatun kuma Ansaar ya gane sosai shi yake ta bada amsar dukkan tambayar da mallamin yayi bayan darasi har kyautar jin dad'i mallamin ya masa ta biscuit da alawa ya kuma tusa shi gaba yace ya cinye kafin ya fita don yasan indai yabar msa baza su barshi ya ci ba qwacewa zasuyi wanann tasa laifukansa suka zama bila adadin ma ga 'yan ajin musamman 'yan kujerar sa Awwalu da Hadi sai cijewa suke suna hararar sa danuna masa lallai zaiji a jikinsa in mallam ya fita.

Yana fita wani mallamin ya shigo don haka abinda sukayi niyya basu yi ba har saida aka tashi suka fito daga aji shi kuma Iyyar sa ta makara saboda wankin da take yi sam bata ma lura lokaci yayi ba saida taga yaran gidan su sun fara shiga gidan sannan da azama tasa hijabin ta ta tafi d'aukar sa.

Tana zuwa ta same shi kashir6an yaci kuka damajina da hawaye har hanci an fasa masa saboda duka.

Da sauri ta qarasa wajensa tana tambayar sa waye yayi masa wannan dukan haka,ta qarasa maganar tare da janyo shi sosai jikinta tana d'aga kansa daya soma d'aukan zafi saboda kuka kuma duk jijiyoyin kan sun tattashi.

Cikin kuka yace "Su Awwalu na gidan M.Ladan ne su Rabe dasu Hadi suka tarar min sukayi min duka d'azu da baki zo ba."

Cikin 6acin rai tace "Me kayi musu?"

Cikin kukan dai yace "Wai akan Mallam Anwaru yace na koma kujerar mu nida Awwalu da Hadin sannan yayi tambayoyi ya bada amsa shine suka tare ni suka min duka."

Kai ta gyad'a abun na cin ranta,ta kalli ofishin shugaban makarantar baya nan don haka kawai sai ta jashi ta goya shi ta d'aure shi da d'ankwalinta da niyyar gobe baza ta qyale ba abun na 'yan garin nan yayi yawa kullum kuma sake gaba yake yi.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now