Part 45

285 19 2
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel

P6️⃣2️⃣-6️⃣3️⃣
Lafiya lau suka sauka a abuja saida suka d'an huta kwana biyu suka zagaya cikin gari sosai sannan suka wuce kano saboda komawar Salmaah school.

'Yan abujan ma su Hameed suma suka bisu suka wuce gumel gaishe da 'yan uwa kafin komawar yaran su makaranta suma.

Harda su Mommah aka wuce gumel d'in,randa suka je sai dare sosai don haka gidajen su suka wuce sai washegari suka samu fita zaga dangi.

Maimuna gida ta wuce itama don yin kwana biyun tare da iyayen ta.

Qarfe biyu na rana suka shiga gidan su Hajaarah da Mommah ne a gaba sai yaran su na biye dasu sai su Hameed da Abbuh.

Innah Jumah na zaune tsakar gidan da wata 'yar yarinya suna ta gyaran zogale gefe guda kuma murhu ne an d'ora madambaci da alamu dambu take yi.

Yaran da gudu suka qarasa wajen Innar suna ihu suna fad'in "Our lovely granny."

Salmaah data fisu wayau tana dariya tace "Hajiya Granny mai ran qarfe,kabarin ki da Ac aljanna d'iban fari."

Da sauri Mommah ta kai mata duka tana fad'in "Ke! Ina kika ji wannan maganar."

Dariya tayi tana gocewa,Innah itama dariyar tayi tana cewa "Rabu da ita wai ita taji zancen en qauye ne sosai to Allah yasa abinda kikace amma ki riqa kirana da Innah ba wannan rani d'in ba."

Duk suka kwashe da dariya yaron Hajaarah yace "Bafa rani ake cewa ba Granny."

Tab'e baki tayi tace "Koma me ake cewa nidai bani so ku kirani da sunan da 'ya 'ya na suke kirana dashi."

Suna dariya duk suka zauna suka shiga gaggaisawa da juna Innah Jumah tace "Ku shiga Baffan ku na ciki bai d'an ji dad'i bama jiya da yau mura ta kama shi sosai."

Duk suka miqe banda Mommah saida suka shige sannan ta miqe jiki a sanyaye ta shiga ita ta zauna bayan su.

Baffan na kwance saman qatuwar katifar dake tsakar d'akin ya d'an lullu6e da bargo dake garin kuma ya d'an busa sanyi kad'an kuma shi dake ba lafiya ce dashi sosai ba sanyin yake ji sosai.

Suka shiga gaida shi da jiki suka gama suka mimmiqe duk suka fice ya rage Mommah da yara ne kad'ai a d'akin.

A hankali yace "Asma matso mana."

Jiki a matuqar salu6e ta matsa kusa dashi sosai tana ta qoqarin riqe kukanta don yanda ta ganshi duk da bawai jiki yake jiba sam ga wanda baisani bama zaice kawai sanyin garine ke damunsa kawai amma ita tasan yanayin Baffan ta abinda zai sa shi zaman d'aki ba kad'an bane a hankali ya shafa kanta yace "Allah yayi miki albarka Asma'u Allah ya raya zuri'ar ki kan hanya madaidaiciya ku cigaba da addua wa yaran ku Allah ya kare su ya raya muku su."

Tana goge qwalla tace "To baffa."

Murmushi yayi yace "To kuma menene abun kuka Asma'u me kike jin tsoro?kar na mutu ko?to ai nayi ma tsahon rai dubeni fa ki kalli tsufana ai yanzu mutuwar nafi buqata kedai kiyi min addu'a Allah yasa na cika da imani da kalmatishahada."

Wannan karan kukan ne ya taho sosai tana girgiza kai tace "Don Allah baffa ka daina wannan maganar."

Murmushi yayi yace "Mutuwa Asma'u dole ce don haka kiyi mana fatan cikawa da imani kinji idan da sauran kwanana a gaba da shekaru masu yawa sai kiga nakai ai."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now