QADDARA CE SILA!

457 26 2
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya* 

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel



P4...
Da sasaafe yanda ta saba tashi taje tayi sallah ta cigaba da karatun data saba yi kullum har qarfe bakwai saura ta tashi Ansaar tayi masa wankan data saba ta saka masa uniform d'insa sannan ta umarce shi da yin sallah kamar yanda suka saba.

Yana idarwa Sabitu d'aya daga yaran yayan Aminatu yazo ta miqo musu kwanon su na tuwo na kari wanda kullum a shi a ke zuba musu nasu.

Wata langa ce duk tayi tsatsa ta tsufa sosai amma a haka Iya Ramma ke zuba musu kuma koda Amina ta canza takai mata wani kwanon saita 6oye wancen a dai wannan d'in zata zuba mata tun tana kaiwa kwanukan mahaifiyarsu saidau taga Iya Ramma ta zubawa 'yan uwan ta ko qawayen ta baqinta in sunzo abinci a ciki har ta daina saidai in an kawo ta juye musu.

Yauma kamar kullum saida ya qandare ya huce sannan aka miqo musu,da yake dai sun saba ci haka kuma duk lalacewar sa a safiyar aka d'umama haka taja musu ta juye a silver babba ta saka musu shi a gaba suka soma ci.

Gishiri ne ya soma yiwa bakunan su sallama daman kuma abinda akeyi musu kenan,sau tari da kuka Ansaar ke qarasa cin abincin don indai tuwo ne sai an gambad'a musu gishiri wataran kuma yajin da babu sirki ko d'aya sannan ake turo musu dashi dole kullum sai tayi dabarar ragewa ta hanyar zabgawa miyar ruwa ta koma tsululu daman gata ga yanda take to yau ma dole haka tayi sannan suka iya cin abincin suka kwanta.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
Tun ran alhamis ake ta shiri a gidan wanda na lura kamar na tafiya ne.

A babban falon gidan a qasa Alh.Basheer ne da iyalansa baki d'aya Aseep da Areep sai yayarsu Hamdiyyah gefe can kuma Mommah ce da Baby Salmah tana shayar da ita sai Maimunatu da take shirya dinning table.

Alh.Basheer ne ya kalli Haj Asma'u(Mommah) yace "Mommah ya kamata fa a soya kajin nan zuwa yau da daddare don komai yazo da sauqi kuma mu tafi da wuri."

Jiki ba qwari da alamun sanyi sosai a tare da ita tace "Abbuh in shaa Allah za'ayi nima bani so gobe ace mun kai qarfe tara ma a kano,so nake Baby Salmah ta sake ni naje na taya Maimuna mu gama don ahad'a da wuri,ni da har na ragon nan nace a soye mata shi kawai idan yaso muna dawowa sai a sai sabo mu taho dashi."

Kai ya gyad'a cike da murmushin jin dad'in yanda Mommah ke kyautatawa mahaifiyarsa duk da kasancewar ta er uwar sa amma ta dangin mahaifinsa suka had'u wato er qanin baban sa ce ita yace "A yi haka d'in."

Miqewa tayi ta sa6a Baby Salmah data soma bacci a baya sannan suka bar falon itada Maimunatu suka shiga aikin soye soyen,ita na soya naman kaji da Doughnut yayin da Maimunatu ke soya na rago wanda tunda yamma sun riga da sun dafe su duka sai cincin suna yi suna d'an ta6a hira saidai kana kallon Momman kasan qarfin hali kawai takeyi.

Sai bayan isha'i suka gama don da yawa ayyukan sun shirya komai tsaf duka an zuba kayyakin da suka tabbatar da zasu buqata a mota wanka ta shiga Maimunatu tayiwa Baby Salmah itama ta kawo mata ita lokacin da take shiryawa Abbuh ya kar6e ta ita taje tayi wanka taci abincin dare ta kwanta da murnar itama gobe zata ga nata iyayen.

Can d'akin kuwa saida ta gama shafe shafen ta ta koma gefen gado ta zauna tana kallon sa yanda yake lalla6a Salmah don ta soma bacci har ya gama bata motsa ba,tsam ya taso daga inda yake ya dawo gefenta ya zauna tare da zagayeta da hannunsa ya zura kansa ta wuyanta yana shaqar qamshin ta yace "Baby Love Hubby ya akayi ne?na lura tuntuni jikin ki a sanyaye yake kodai akwai damuwa ne."

Kanta ta girgiza idon ta na neman zubda qwallah tace "Kullum in zamu gida fitinar Innar Hamid nake gudu wallahi,kullum ita akwai sabon qorafi a wajen ta baza tabar babana ya zauna lafiya ba."

Cike da tausayawa yace yana shafa gefen fuskarta "Innar Hamid bayan matar mahaifin ki kuma qanwar mahaifiyar kice ita,don haka tana matuqar buqatar addu'ar ki Allah yasa ta gane gaskiya."

Kai ta gyad'a kawai sannan ya cigaba "Kiyi bakin qoqarin ki a yanzun ma idan munje kamar yanda kika saba kada maganganun ta su dame ki kinji?"

Kai ta sake gyad'awa tana share hawayenta tace "Toh Abbuh nagode."

Kai ya gyad'a don shi a wajensa tuni labari yasha banban ya soma birkicewa,bata da za6i sai biyewa mijinta don faranta masa rai haka salon ya canza nikam sad'ab sad'ab na arce don bazan iya ganin wagga babban aiki ba.

Washegari tun wajen takwas na safiya suka d'auki hanyar Gumel asalin garin su kenan basu wani jima ba don shad'aya ma a cikin garin tayi musu suna tsakar gidan Ayyah mahaifiyar Alh.Basheer kenan.

Hira sosai ake an gama sauke kayan da suka taho dasu Mommah ta shige part d'insu bayan sun gama cin abinci wanka ta sake yi sannan aka sake shirya twins don zuwa sallar juma'a da mahaifin su itama Maimunatu tayi musu sallama ta tafi gidan su.

Alh.Basheer kam yana manne da Mahaifiyar sa wadda suke kira Ayyaah suna ta hira har Baffansa ya dawo daga d'aurin aure daya tafi a qauyen gumel d'in shima ya zauna aka cigaba da hirar dashi har aka yi kiran sallah na farko suka kwashi yaran suka tafi masallaci dasu su kuma su Mommah sai a lokacin suka shiga tasu hirar ita da Ayyaah don ita sam bata surukantaka da ita mahaifiya ta d'auke ta duk wata matsalar ta ita take gayawa kuma su kashe su binne ko Baffan su baya jin me suka tattauna balle fa Basheer.

√√√√√√√√√√√√√√
Iya Ramma da d'iyar ta Hafiza a tsakar gidan su suna surfe suna yi suna hira tsakanin su lokacin Iyyah ta fito da Ansaar goye a bayan ta cikin damuwa tace "Iya don Allah ina Yaya Madu yake?"

Ko kallon tsiya bata ishe ta ba balle na arziqi,hakan baisa ta damu ba sai ta sake maimaita tambayar tata a karo na biyu nan ma shiru taqi amsa mata sai ma zaqulo zancen da Hafizan zata sake taya ta take.

A karo na ba adadi cike da damuwa tana shirin saka kuka tace "Iya Ramma magana fa nake Ansaar baida lafiya zanje kaishi gezawa na kaishi wajen babban likita."

Wani banzan kallo ta watsa mata kan tace "Yana cikin riga ta ko zani na Madun kinji ko?er marasa kunya er mai baki ni kikewa gayawa shegen d'anki baida lafiya zaki tafi ki kaishi babban asibiti,ki zarce kano ba gezawa ba qarshen tama wajen ubansa zaki yanda aka saba rabo wanduna ko kuwa wata sabuwar harkar karuwancin  ce ta bud'e."

Cike da takaici ta share hawayen ta tace "Kinfi kowa sanin niba karuwa bace ban ta6a karuwanci ba qaddara ce a gareni wadda na kar6a da hannu bibiyu kuma ina roqon Allah daya yi min sakayya mafi alkhairi akan abinda nayi amma bakomai akwai lokacin da kowa zai shaida hakan lokacin da nadama da danasani baza suyi miki amfani ba."

Harta juya zata bar wajen Iya Ramma tayi shewa mai qarfi tare da fad'in "Lallai yarinya wai qaddara an gaida limamiya masaniyar qaddara mai kar6e da hannu biyu Allah nuna min sanda kike fad'en da raina da lafiya ta na gani."

Murmushin takaici tayi ta juya ta fice daga gidan kawai zuciyar ta cunkushe da qunci da baqincikin hali irin na Iya Ramma da bata tsoron Allah,tafi kowa sanin gaskiyar lamarin abinda ya faru amma itace ta soma kwazawa ta soma chanzawa dukkan abinda ya faru hanya ta canza masa manufa.

Haka ta qarasa bakin kwalta ta tsaida mai machine sukayi ciniki da yake kuma masu wucewa ne wad'anda suke haya daga qauyuka na kurkusa ya d'auke ta ya kaita har asibitin gezawa sannan ta shiga ta yanki kati ta je kuma Allah ya taimake ta taga likita da wuri ya duba su nan da nan suka siyi dukkan magungunan suka dawo gida.

*©ZahraArkel ce !* 💝

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now