Part 64

289 16 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!

Qaddara ce sila group,Hajow fans group,indabawa group,maidala group da sauran groups ina matuqar jin dad'in yanda yanda kuke comment wa novel dinnan thanks so much Allah yabar zumunci.

P9️⃣8️⃣
Amina Muhammad Basiru shine cikakken sunana Mallam Basiru Mai darasu shine mahaifina kamar yanda kusan gabad'aya wajen nan kuka sani.

Ya samu sunan Mai darasu ne saboda yana da babbar makaranta da yake koyar da manyan mutane da yara da kuma matan aure da daddare makarantar addini da ake koyar da litattafan addini tun daga kan alqur'ani da sauran litattafai.

Iyayena mu hud'u kacal suka haifa wato Sama'ila daya kasance babban mu sai Hamza dake bi masa sai kuma Atiku daga nan Innar mu taita samun b'ari sai da ya zamana an shekara goma sha d'aya kafin aka same ni.

Mahaifiyar mu er asalin Gumel ce bafulatana usul yayin da mahaifin mu ya kasance d'an asalin nan garin GANGARE ne dake qarqashin garin gezawa ya kuma samun auren mahaifiyar mune a wajen kawun ta dake garin gumel wanda kasuwanci ne ya had'a su.

Na taso cikin gata da so tsakanin iyayena da 'yan uwana musamman daya kasance ni kadai ce mace sannan yarinya sosai,wannan yasa Innar mu ta fifita ni sosai.

Shekaru na biyu a duniya mahaifina ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya ta zazzabi da mura.

Haka Innar mu ta cigaba da kula dani tana bani tarbiyya don duk da irin son da take mini bata yi sake wajen tarbiyantar dani da bani ilimi ba don itama hafiza ce sannan tana da karatu mai zurfi a addini hakan yasa nima na zama mai yawan ilimi har mutane na mamakin haka.

Shekaru na hud'u babban yayan mu Sama'ila ya auro Rammah daga qauyen kusa da mu wanda bazan iya d'orar da komai ba akanta saidai nasani er talla ce kuma farkon fara zancen auren mahaifiyar mu ta nuna adawa da auren don tana ganin akasarin en talla basu da tarbiyya balle su tarbiyantar,saidai hakan bai hana shi kafewa ba akan dolen dole sai ya aure ta hakan yasa dole Innah ta haqura ya auro ta.

Zaman Innar mu da Rammah ba wani zama ne da za ace mai dadi ba haka zalika baza a kira shi maras dad'i ba don Rammah macece maras kirki da kawaici da neman fitina haka nan kuma Innar mu ta kasance macece mai kawaici irin na fulani da kunya tunda matar d'ane na fari a wajen ta shiyasa ko fitina ta kwaso Innar bata kulata balle ta nuna tasan tana yi sai ta share ta hakan kuma ba qaramin zaman lafiya ya kawo ba don babu wanda ya isa yace gashi abinda ke faruwa.

Ni ba mutum bace mai kwarafniya tun tasowa ta ko irin qiriniyar yara sam bana ciki da wahala ma a samu anyi wata b'arna dani a ciki.

Wannan halin nawa yasa da yawan mutane ke kirana miskila don ko magana ma bata dame ni ba,haka nan bana fad'a,kullum zaka same ni tare da Innar mu ina taya ta sabgogin ta tunda inada qoqarin nuna son gwanewa a harkokin gida duk da qanqantar shekaruna.

Rayuwa ta riqa tafiya tsakanin mu da Rammah dai babu wani abu mai muhimmanci sai in taga mijin ta,haka tafiya ta tasowa Innah zuwa garinsu wata ta'aziyya a lokacin kuma akwai makaranta haka dole ta barni wajen Rammah don sam ko meye zai faru bata yardar min fashin makaranta ba sai in ya zama dolen dole,ina kuka bana son zama da Rammah duk da ba wani abun take min ba haka kawai dai bana so amma ba yanda zanyi Innah ta tafi Gumel ta barni.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now