Part 20 Qaddara ce sila

317 21 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!



_Page 20-21_
Da asuba data tashi bata koma ba ta shiga aikin dangace kanta duk da Ansaar na taimaka mata hakan bai sa aikin ya mata sauri ba har magriba tana abu d'aya Allah dai ya taimake ta ta gama a magribar amma matuqar jigatuwa tayi ta zazzabi ne sosai a jikinta don haka tan yin wanka da qyar a daddafe tayi sallar magriba ko cikakkiyar addu'a bata samu tayi ba ta kwanta saboda azababben ciwon da kanta ke mata da gajiya ga zazzabi dake cinta ga wata kwantacciyar yunwa.

🦋🦋🦋
Ga su Iya Rammah kuwa tunda asussubar fari suka doka sammako suka fice don Iya Rammah ma gani tayi daren ba qaramin tsaho yayi mata ba.

Suna zuwa suka tadda Hama a shirye don haka fita kawai sukayi Hama na bawa kishiyar ta umarnin abubuwan da zata yi mata kan ta dawo ita ko cikin biyayya take amsawa harta gama suka fice.

Abin fa ya masifar burge Iya Rammah don haka tasa a ranta wannan aikin ma zata yiwa kishiyoyin ta amma a yanzu dai so take yi ta fara da Aminatu don ita ta ke gabanta yanzu.

Suna tafe Hama na kuzanta yanda bokan nata yake ita kuma Iya Rammah na ta yabawa yanda taga yin aikin nasa.

Qauyuka kamar biyu ne tsakanin su sannan suka isa ainihin qauyen da bokan yake wanda ba a cikin gari yake ba don baya son a sa masa ido shima.

A qofar gidan sa suka tsaya ganin jibga jibgan motoci da alamu yana da manyan baqi ne don haka dole aka tsayar dasu a waje kusan rabin awa Iya Rammah ta gama qosawa su fito ta isa gareshi.

To sun qara mintuna wajen goma sannan suka fito,manyan alhazawa ne masu ji da kud'i da izza daga nan wata hajiya ta shiga itama ta d'an jima sannan su Iya Rammah suka shiga.

Yana ganin Hama ya sheqe da dariya yana fad'in "Hama kenan ai na gaya miki aikina sai kin kawo wasu."

Zama tayi tana murmushi tace "Wallahi kuwa Mallam ai na gama sallama maka yanzu kaga yanda nake damawa a gidana kai baka ce nice ba."

Dariya ya sake sakawa yace "Ahap ai gashi nan ko a jikin ki ya nuna hankalin ki yanzu ya kwanta."

Ta gyara zaman ta tace "Wallahi kuwa."

Saida ya d'an ci serious sannan yace "Ina jin ki yau kuma dame kika zo na ganki da baqin fuska."

Zungurar Iya Rammah tayi tace "Daman qanwar mijina ce kawai ke shige min hanci da qudundune duk abinda zanyi Mallam don na samu yarinyar nan ta fita daga sabgata na daina ganin ta nayi amma abu yaci tura shiyasa nake son a fitar da ita daga garin ta shiga duniya ta tambad'e ta balbalce kawai kowa ya huta kuma kada yan uwan ta su nema ta daga nan har tashin alqiyama."

Kai ya jinjina ya jawo wani faranti daya sha tankadaddiyar qasa a ciki ya soma wasu zane zane a jiki zuwa can jimawa ya d'ago yana kallonta yana girgiza kai.

A d'an tsorace tace "Mallam me kenan?"

Kai ya sake girgizawa yace "Akwai lokacin barin ta garin na dindindin saidai ba yanzu bane fitar ta a yanzu bazai ta6a yuwuwa ba koda kuwa gawar tace baza ta fita daga garin nan ba domin yaron da take tare dashi yana da wani babban rabo wanda sai ya same shi sannan zai fice daga garin wanda fitar sa shine silar warwarewar duk abinda kika qulla ni da a shawarce ce miki zanyi kada koda wasa kiso fitar su musamman shi wannan yaron domin akwai babban lamari a had'e da fitar tasa."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now