Part 40

279 18 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel






P5️⃣2️⃣-5️⃣3️⃣
Jin tayi shiru ne ya sashi sake tausasa muryar sa yace "Don Allah Hafsatu kiyi wa kanki fad'a duk fa wanda rai yaiwa dad'i baya mai shi ba kuma kowa yasha inuwar gemu to bazai kai maqogaro va yaushe ne akan zancen mutane zaki cuci kanki ki lahanta rayuwar d'iyar ki gara tun wuri ki farka kisan halin da kike ciki tun kafin kizo kina dana sani."

Jinjina kai kawai take badon lallai maganar ta shige ta gabadaya ba saidai tabbas ta daki fiye da kaso tamanin na qudururrukan data d'auka akan wannan auren don haka ta kasa qwaqqwaran motsi.

Jin shirun ta yayi yawa ya sashi miqewa yana fad'in "Kiyi tunani mai zurfi kuma ki yiwa kanki da ita yarinyar nan adalci ki sani nidai bazan fasa auren nan dana d'aura ba shawara ta rage ga mai shiga rijiya."

Yana maganar ya juya ya bar d'akin ya barta a zaune kamar gunki ita d'aya ta dinga cud'a maganar tana juyawa ta a ranta da tunaninnika barkatai wad'anda tabbas nasara ce kawai taqi yarda mijin nata yayi a kanta amma ita kanta yanzu haushin abubuwan data yi take yi a hankali ta dinga warwarewa kanta komai tun sanin da tayiwa Aminatu tuntuni da nutsuwar ta da kamewar ta har kawo halin da take ciki yanzun da kanta ta dinga furta "Ban kyauta ba tabbas ban kyauta ba."

A haka ta raba dare tana faman tufka da warwara qarshe dai ta yanke shawarar ta kore komai a ranta kuma zata rumgumi wannan auren da hannu bibiyu ta sa masa albarka kamar yanda mijinta yayi bata san me Allah ya b'oye a cikin sa da har ya qadarce shi akayi bakatatan.

Da wannan ta samu nutsuwa ta kwanta d'in akan gobe da kanta zata je ta taho da Saro daga inda ya kaita ta kuma kula da ita kamar yanda kowacce uwa tagari takewa 'yarta.

************
Su Sama'ila kuwa na dawowa suka zauna a zauren gidan su don tattauna yanda lamurra zasu kasance idan su Ansaar sun dawo don suna buqatar tabbatar musu da cewar a yanzu suna tare dasu d'ari bisa d'ari wannan ne kuma yasa Hamza yace "Inaga zan soma zuwa dashi kasuwa a gwada sa'ar sa a nan duk da ba abinda ya sani amma indai yana da fahimta zai gane komai cikin sauqi."

Iya Rammah data zo fitowa ta tsinci maganar Hamza sai ta lafe jikin danga tana sauraren su Atiku yace "Wannan tunani ne me kyau amma in kasuwar bata kar6e shiba sai a juya wani abun ko."

"Hakane." Duk suka amsa sannan suka cigaba da tattaunawa akan sauran al'amuran harda na aurensa.

Iya Rammah fa ai sai taji kanta ya soma juya masa saboda tsabar hassada da baqin cikin daya ciyo da baya da baya ta dinga ja a hankali don kar su jita har ta isa tsakiyar gidan ta taqarqare ta qunduma wata qatuwar ashar wadda ta ja hankalin matan gidan dake tsakar gidan suka soma tambayar ta lafiya?

Duk wanda ya tambaye ta sai ya samu nasa rabon har ta shige d'akinta ta zauna bakin gadon bunun ta tana maida numfashi kamar wadda tayi gudun kilometres masu yawa zuciyar ta kuwa har wani fat fat fat take saboda azaba a fili ta dinga furta "Ladan Ladan Ladan Ladan...." kira kawai take ba adadi don maganar a bazata tazo mata ta kuma kad'a ta matuqa da gaske ace da ranta da lafiyar ta Amina da d'anta su samu farinciki da qarfi ta furta "Inaaaaa wallahi bazai yuwu ko za a mutu."

Zumbur ta miqe ta soma safa da marwa tana tunanin abinda ya kamata tayi domin bokan nata tayi zarya takai hud'u ana ce mata ya tafi nijar wajen wani mallamin sa wanda ya koyar dashi har wannan lokacin bai dawo ba,baqin ciki yasa ta sake qundomo wata ashar d'in tana kaiwa bango naushi da iya qarfin ta a zafafe kamar namiji sai huci take kamar kumurci.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now