QADDARA CE SILA!

485 33 7
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya* 

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel

P5...
Suna dawowa ta sauka bakin kwaltar ta ganganro da qafa amma maimakon tayi gida sai kawai tayi wani d'an duhuwa ta zauna ta kwanto Ansaar dake ta bacci ta ajje ledar magungunan da kuma ledar data siyo d'an biredi da funkaso da yake kasuwar gezawa naci ranar kawai tayi jugun tana kallon zagayen wajen kamar mai nazarin wani abu kafin ta rushe da wani irin mahaukacin kuka kamar wata aka tsulalawa bulalar qarfe.

Sosai tayi shi don da alama babu yawan jama'a masu wucewa ta wajen,har yamma liqis tana zaune a wajen har Ansaar ya tashi ta bashi funkason yaci da yawa sannan ta bashi maganin duk a wajen sai kuma ya ware ya dinga wasansa a wajen tana kallonsa.

Saida taga duhu ya soma d'an soma shiga alamun magriba ta kawo jiki sannan ta jashi ta goya shi suka tafi gida.

Kamar koda yaushe dukkan matan gidan suna tsakar gidan suna sana'ar su tayi da mutane da shewace shewace kamar 'ya 'yan dila ta shiga daa sallamar ta babu wanda ya amsa kamar yanda ta zata sai kawai ta zagaye su tana nazarin irin murna da farin cikin da suke ciki yau.

Harta kusa shiga d'aki Ramatu tace "To tsigalalliya Allah dai ya qara rufa asiri Hinde da kika asirce yau dai an kawo kayanta kuma nan da watan bawa zamu sha shagalin biki saiki shirya tar6ar sabon gori idan tabar gidan..."

Bata qarasa ba Hinde ta kar6e cike da masifa tace "Idan nabar gidan nan Allah yana nan tare da su kuma wallahi ku kiyayi randa Allah zai kama ku da haqqin bayin Allahn nan."

Hafiza da Karima ne sukayi shewa a tare sannan Karima tace "Ahayye wai ma,wai bayin Allah."

Cike da bala'i Hinde tayi wajen ta batayi wata wata ba kuma ta zabge ta da mari ta nuna ta da yatsa tana huci tana fad'in "Wallahi Tallahi ubanki zanci inyi qasa qasa dake a wajen nan don kinsan uwar data haife kima tai min kad'an balle kuma ke karan kad'a miya,da kike wani ahayye bayin ubanki ne da to ko yaya?"

Muqus Karima tayi don tabbas tasani Hinde zata aikata abinda ta fad'a muddin ta tanka amma tabbas bazata bari marin ta ya tafi a banza va sai ta rama akan wannan shegen d'an mai kama da mayu dole ne.

Juyawa Iyyah tayi kawai ta shige d'aki ta sauke Ansaar dake ta zillo ta sauke shi don ya takura da yawa ya wuce goyon a wajenta don dai tana yi ne don ta sauqaqa masa wata tsiyar ta mutan gidan.

Tana sauke shi ta samu gefen gadon su ta zauna ta had'a tagumi kawai tana tunanin barin Hinde gidan nan a garesu kam tasan mugun bala'i ne ke tunkaro su,tasani Hinde ce tasa ake saurara musu a gidan nan in ba don ita ba abinda ake musu sai ya ninka hakan to yanzu ita kam ya zata yi idan Hinde tayi aure?wacce madafa kuma zata dafa bayan auren ta?.

Bata kai ga samawa kanta mafita ba Hinde ta shiga d'akin da sallamar ta,Iyyah ta kalle ta da alamun fara'a a fuskar ta saidai duk wanda ya kalla yasan ta dole ce tace "Amarya ce da kanta."

Da alamun kunya ta zauna tana fad'in "Iyyah kenan wai Amarya."

Dariya tayi tace "Eh mana,ashe auren ya matso babu labari."

Hinde ta sake yin dare tace "To ni goro suka ce zasu kawo kuma sai naji harda sa rana."

Kai ta gyad'a tace "Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now