Part 67

258 16 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!




P1️⃣0️⃣1️⃣
Ayyah,inna Jumah,Iyyah,Hamdiyyah da Maimuna da su Salmah duk d'akin Iyyah suka tafi suka kwanta yayin da mazan dukkan su suka d'uru d'akin su Ansaar da Saratu inda saida Ansaar da sauran samarin suka gyara shi saboda er qurar da yayi.

Hoton Saratu a falon twins da Mahmoud bayan su Baffa sun kwanta sukaje suna kallo.

Areep yayi murmushi yace "She's cute."

Aseep yace "And young,i hope tana raye nasan da kowa zaiji dad'in ta don fuskarta looks very innocent."

Ansaar da qwalla ta ciko masa ido ya zauna gefen kujera yana cigaba da kallon hoton yana tuna abubuwa a kanta da dama basu ankara ba sai ji sukayi ya fashe da wani irin matsanancin kuka.

Da sauri suka dawo kusa dashi suna dafa kafad'ar sa Mahmoud yace "Haba mana Ansaar Saratu fa ba kukan ka take buqata ba adduar ka take buqata ya zaka zama lusari ne?"

Isma'il yace "Indai akan Saratu ne Ansaar yafi qarfin lusari saidai a kira shi fiye da haka ya kasa haquri da ita ya kasa fad'awa zuciyar sa ta rasu baza ta dawo ba ya kasa nutsuwa ya gane annabi ya faku."

Ya miqe yana share hawayen sa ya qarasa gaban hoton yana cewa cikin rawar murya "Baza ku gane ba,ni kadai nasan me nake ji game da ita kuma a wancen lokacin inda za a bani zab'i ace da ta rayu nina mutu kota mutu ni na rayu wallahi zan zab'i ta rayun nina mutu,Saratu mace mai kawaici da sanin ya kamata ga addini ga mutunci ga tarbiyya ta soni sanda nake tsakiyar maqiya babu wanda ke sona ke yake kusantata a lokacin ta jajirce ta miqe a tsakiyar mutane dubunnai tace ni take so taya bazan yi kukan rashin ta ba sai dai nasan Allah ya fini sonta shiyasa ya d'auke min ita har abada bazan iya daina kukan rashin taba rufin asiri na d'aya kafin ta tafi tayi babbar kyautar samun Lil Sarah idan badon haka ba qilan da watarana hauka zanyi." Ya qarashe da sake fashewa da kuka.

Duk ya basu tausayi amma ya za'ayi mutuwa tayi gaggawar d'auke Saratu lokacin da ba a tsammata ba gata 'yar qaramar yarinya saidai ga magajiyar ta nan wato Little kamar yanda Areep ya sa mata,sun jima a haka babu wanda yayi yunqurin hana shi kukan da yake wataqila sun fuskanci qyale shi yayi kukan sa shine mafi a'ala a gareshi don ya fidda azabar da qirjin sa ke masa da kansa yayi shiru ya nemi kan bargon da sukayi shimfid'a a qasa ya kwanta yana sakin ajiyar zuciya.

Duk sai sukayi koyi da shi kamar wadanda dama can jira suke ya nuna musu,suna kwanciya kuwa ba wanda ya wuce mintuna biyar yayi bacci.

Ansaar yaji alamun sun bacci kawai sai ya miqe don shi kam baya jin wani bacci ya dinga kallon su yana ayyanawa a ransa wai shine yau da en uwa da dangin sa a waje guda,kuka ya dinga yi qasa qasa yana share hawayen sa har wajen awa guda kafin yaji an tab'a shi.

Da hanzari ya juya sai yaga Baffa yayi saurin sa masa hannu a baki alamun kada yayi magana ya ja hannunsa suka fice tsakar gidan suka zauna kan tabarmar da aka nad'e ta aka ajiye a gefe Ansaar ya shimfid'a ta suna fuskantar juna Baffa cikin tsokana yace "Meya hana ka bacci."

Murmushi yayi lokaci guda hawaye na shatata yace muryar sa na rawa "Ina tuna duk tsahon wannan shekarun da muka d'auka da Iyyah ta muna fama da qalubale kala kala daga wannan sai wannan ashe ina da gata ni ba shege bane inada iyaye da dangi kamar kowanne d'a?ba mamaki shiyasa Iyyah ta kasa fad'a min waye mahaifina duk sanda zan mata wannan tambayar sai ta fashe da kuka tana cewa ba yanzu ba ba yanzu ba,Saratu da qishir ruwan sanin waye ni ta rasu na so ace tana raye ta san mijin ta nada iyaye da dangi kamar kowa." Ya qarashe da goge hawayen sa wanda hakan bawai ya hana su zuba bane.

Cikin tausayi ya dafa shi yace "Ita mutuwa ai bata barin wani don wani da ana haka mu kanmu da mun roqi a bar mana iyayen mu saidai babu wannan,Saratu kuma tabar magajiyar ta ai tunda ga mai sunan ta nan kuma mai kamannin ta tunda ga hoton ta nan banbancin su kawai shekaru ne amma inta kai kamar ya iya itama lallai zata zama irin ta saidai Allah yayi mata rahma."

Ansaar ya amsa da Amin.

Shiru ya d'an gifta kafin su qara magana sai ganin Mommah sukai ta fito itama tana share hawaye tazo ta zauna tare da jan hannun Ansaar tace "Nafi kowa farin ciki da wannan ranar Ansaar don itace burina da fatana ina tsananin qishin ruwan ganin ta sai gashi Allah ya nuna min babu abinda zancewa Iyyahr ka sai addua domin da wahala asamu mace irinta a wannan zamanin mai hali irin nata gashi bata haife kaba amma ta tsaya tsayin daka irin tsaiwar da ba kowacce uwa bace bama zata iya don gashi nan yaran ko ina yar dasu ake yi saboda iyayen su suna tsoron shiga hali irin wanda ta shiga sai gashi ita bata ma haifa ba amma ta cinye duk wannan bala'in kuma da badon Allah ya kawo sanadi ba da haka zata qare rayuwarta a wannan bala'in."

Ansaar yayi murmushi yana jin qarin qaunar Iyyar sa yace "Lallai babu abinda zakuyi mata daya wuce addua sai kuma ina roqon ku da ku d'auke ta daga qauyen nan inda hali ko sau daya ne tabar qasar nan duk da inada burin nine zan fara fitar da ita amma don Allah kuyi mana wannan alfarmar zanji dad'i."

Abbuh dake fitowa yace "babu wani abu da zaku nema mu hanaku nifa nan ma wani tunani nakeyi."

Duk suka zuba masa ido suna kallon sa sannan yace "Ai Iyyar ka tayi primary ko?"

Kai ya d'aga masa alamun eh.

Sai ya cigaba "Gemu baya hana ilmi idan dai har tana son karatun ta har yanzu ni kuma zan shige mata gaba tayi shi har sai tayi masters."

Ansaar yayi dariya kan yayi magana kuma Iyyah ta fito tana kallon su cike da mamaki tace "Wannan qus qus d'in meye aka had'a ana hana mu bacci?"

Duk dariya sukayi mara sauti kafin Mommah tace "Fad'i gaskiya qus qus d'in kema kika fito ji kenan."

Dariya tayi tana zama kusa da ita tace "Aa yaya kun dai hanani bacci shiyasa na fito kinga sai ayi tuntub'e dad'in gushi inji me ake cewa."

Dariya suka sake yi sannan Ansaar ya zame hannun sadake cikin na Mommah ya koma wajen Iyyah yana cewa cikin murna "Iyyah Abbuh ne yace zai biya miki karatun ki har masters nasan kina so don Allah ki karba kice zakiyi ina son kiyi ilimin da shine burin ki tuntuni."

Hawaye ne taji sun ciko mata ido tace "Na yarda wallahi ni ko iya secondary na tsaya Alhamdulillahi nadai yaqi jahilci ba kamar da ba."

Cikin murna Abbuh da Mommah suka had'a baki da "Yawwa Alhamdulillahi."

Hira sosai ta b'alle tsakanin su duk da qus qus ce amma sosai sukeyin ta kowa yana fad'in albarkacin bakinsa har wajen qarfe uku Ansaar da bacci ya dame shi ya d'an jingina kansa kan cinyar Iyyah sai juyowa sukayi sukaga yayi bacci tana ta shafa kansa suna hira Mommah ta bisu da kallon sha'awa kawai abun har mamaki ya bata wai wannan ace ba itace ta haife shi ba dubi fa wai yayi aure ya haihu amma bai daina saka kansa a cinyar ta yana bacci ba hawaye ya shiga taruwa a idon ta saita miqe ta shige tana cewa nidai sai anjiman ku.

A hankali suka miqe Abbuh yace "Tashe shi muje mu kwanta kan asuba."

A hankali ta tashe shi kamar wani jariri saida taga shigar su sannan ta nad'e tabarmar ta shiga daki itama ta kwanta tana jin wani irin dad'i na musamman a ranta yaudai Allah ya nunawa duniya Ansaar d'in ta ba shege bane kuma Allah ya toni asirin Rammah shikenan ita bata da sauran damuwa a duniyar ta ko yanzu tabar duniya tasan lallai bata da danasani a cikinta.


Afuwan am kinda busy this days ayi haquri da wannan.

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now