Part 19 Qaddara ce sila

327 24 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!

Wato Fans ina matuqar godiya maras adadi a gare ku na addu'o'i da fatan alkhairi da kuka riqa min na samun ingantacciyar lafiya nagode nagode Allah ya qara zumunci nagode sosai musamman masu biyo ni private wallahi banda bakin gode muku Allah ya saka da alkhairi i luv u guys so very much wollah ana tare😍😍😍

_Page 18-19_
•••Haka ta wayi safiya sukuku da ita ga wani zazzabi na musamman na neman lullu6e ta amma duk da haka sai ta daure ta tsananta jikinta ta ja Ansaar suka nufi gonar da ainihi itace gadon ta 'yan uwan nata ke nomawa wanda koda an noma basa bata koda ladan gona kuma bata ta6a d'aga kai ta kalle suba.

Gonar fal take da itatuwa wanda da alamu sassare su akai don wani amfani kuma akwai dogaye a jiki daga gefe kuma akwai wani abu da akayi kamar rumbu duk ciki kararen bara ne basu d'ebe ba daman kuma kusan da iya abinda takan d'an tsira kenan.

A hankali ta had'a kararen masu yawa ta qulle da d'an kwalinta tana niyyar d'orawa Ansaar yace "Iyyah ni baki d'aura min ba bakya so na taya ki?"

A tausaye ta shafa kansa tace "Ansaar kayan nan sun ma nauyi baza ka iya ba kadai ta bina kaji kada kayi nisa dani."

Kansa ya gyad'a mata sannan yace "To in d'ebar miki qirare kiyi girki?"

Tana qoqarin maida qwallar ta tace "d'ebo min yaron kirki Allah yayi maka albarka ya d'aukaka ka ya vaka ilmi mai amfani."

Ya washe baki yana dariya yana fad'in "Amin Iyyahta."

Dariya ya bata don ta fuskanci duk da qanqantar shekarun sa yana matuqar so tace Allah yayi masa albarka ta dinga binsa da kallo yana had'o qiraren qanana har ya had'a da yawa,saita kwance d'ankwalin kanta ta d'aure masa a ciki suka tafi gida.

Babu wanda ya amsa sallamar su bisa ga al'adar tasu ta en gidan haka nan ba wanda ya kalli take harta sauke karan ta bud'e d'akinta ta saka shi a ciki Ansaar ma yasa qiraren kansa akan karan suka sake kulle d'akin don ta tabbatar in har ta barshi a tsakar gidan labudda baza ta dawo ta same shi ba.

Sun juya kenan Hasiya matar Atiiku ta uku tace "Aikin banza mu dai wallahi hankalin mu yanzu bazai ta6a kwanciya ba muna tare da muguwa munafuka irin wannan wacce Allah ya tsinewa nikam abu ya tsaurara fa za a iya nema na a rasa wallahi don bazan zauna wata jakar banza ta illatani ba a wofi."

Iya Salah matar Sama'ilah ta farko tace "Ke mai gatan tafiya gidan kenan muda muka tsofe da zuwa gida ai saidai muyi ta qarar mugun mutum wajen Allah kada ya bashi sa'ar cutar damu."

Alawiyya d'iyar iya Ramma tace "Kuma ya cigaba da tona asirin mugun mutum ba Iyar Salame."

Duk ta fuskanci maganganun nasu sarai koda daman in kaji ana yadda magana a tsakar gidan to tabbas da ita ake,kuma abun sam bai dame taba tsap ta gama abinda zatayi ta fice ta sake tafiya gonar dake da bala'in rata tsakanin ta da ainihin cikin garin.

Suna tafe suna hira da yaron ta wani shirmen tayi dariya in yayi wani abun ya bata tausayi wani abun ta kwa6e shi haka suka yini zarya tsakanin cikin gari da gona da jido qirare da Karan da zata gina danga dashi(kunji fa readers tsabar masifa aikin da yaka kamata ace maza ne zasu yi ita shine take yi Allah ya raba mu da mahassada da maqiya.)

Duk wannan jidon na kara da tayi in zata shigo sai goma sai yada mata magana sau goma ita kuma bata tankawa kowa ba maimakon haka ma sai ta koma shiga da karatun alqur'ani mai sauti itada yaron ta wanda shike d'auke hankalinta daga jin munanan kalamansu akansu.

QADDARA CE SILA Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin