29 Qaddara ce sila

324 20 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!

*Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!A jiya 16/9/2019 na qara shekara na kuma rage wata shekarar nagodewa Allah da wannan baiwar da yayi min ta ganin wannan shekaru masu albarka ina roqon sa ya qara min qarfin gwiwa da imani da jin tsoron sa da kuma ingantacciyar rayuwa ya bani ikon cinye dukkan jarabawarsa amin....Ina matuqar godiya ga wad'anda suka taya ni murna nagode nagode Allah yabar zumunci amin*








Page 38-39

*BAYAN SHEKARU UKU*
•••Ranar asabar ranar ta kama ranar d'an qwarya qwaryar liyafar da Momma suka shiryawa 'yan biyu ne ta fita daga secondary school da kuma samun sakamako mai kyau 'yan uwa da abokan arziqi duk sun hallara tun daga na gumel har na nan kano da sauran abokan ayyukan Abbu da ma qawayen Hamdiyyah dake a level 400 yanzu micro biology.

Kowa ka ganshi cikin annushuwa yake da farin ciki musamman da ya kasance an hadu ne da 'yan uwa da sauran abokanan wasa ana ta zolayar juna da barkwanci tsakani yau ko Aseep da bashi da sakewa can na hango shi tsakiyar friends yana ta caskalewa da nishad'i nidai harda riqe ha6a ina kallonsa don ban taba zaton yana dariya haka ba.

Sanye suke da wata dakakkiyar shadda Ash colour tasha aiki da irin zaren ta d'inkin zamani na en birni en qwalisa sun sha hulunan su zanna bukar dakakkiya 'yar borno ta asalin qafafuwansu kuwa wasu takalma ne sai uban qyalli suke abun gwanin sha'awa hatta da links d'in su iri d'aya ne sai suka fito manyan matasa majiya qarfi masu kyau na d'aukar hankali duk da qanqantar shekarun su babu abinda zai hana ka zaci shekarun yaran basu wuce ashirin ba saboda cikar zati da kamala don haka duk qwaqwar ka baka isa ka gano banbancin su ba koda kuwa ta wajen sakewar ne don yau Aseep ya bada mamaki sosai.

Qarfe biyu aka fara hidindimu sosai anyi addu'o'i haka zalika aka ci aka sha ba a tashi ba sai gab da magriba inda en uwa na kurkusa suka tai tafiya na nesa kuwa en gumel sai gobe ne zasu wuce don haka gidan ya zama kamar gidan biki saboda cika da hayaniya.

Don koda aka tashin ma wata dabar hirar aka kuma kafawa ana cigaba da zantawa da juna kamar an yi shekaru ba a had'u bane.

*** *** ***
A shekarun sa na haihuwa sha bakwai ya gama secondary a yanzu zaman banza kawai yake yi sai in yamma tayi ya je yayi karatu haka nan da magriba.

Yau ma yana zaune kusan qarfe biyu na rana harda d'oriya yana kallon yanda samari da 'yan mata harda manya keta karakaina suna dosar babbar kasuwar garin kasancewar a ranar take ci.

Kamar kullum Saro er M.Ladan mallaminsa tazo gifta shi da daron funkaso akanta tare da qawayen ta take amma tana hango shi sai ta zame musu ta tsaya a baya don kawai tayi masa magana yanda ta saba kullum.

Shima yana ganin ta ya saki murmushi don itace mace ta farko a tun tasowar sa take kula shi har ma in ta samu d'an sake taga babu wanda ke kallon su sukan d'anyi hira kuma wannan ne ya saka shaquwa da sabo a tsakanin su sosai.

Saida ta bari qawayen ta sun yi nisa sosai har sun sha kwana sannan ta qarasa inda yake tana dariya tace "Mallaam." (sunan sa take kiransa dashi kenan.)

Yana murmushi ya miqe yana fad'in "Hajiya Saro sai kasuwa?"

Duk da da kaya akanta haka ta d'aga masa kai tana murmushin daya lotsa manyan dimples d'inta tace "Taya ni saukewa na baka ka kaiwa Iyyah."

QADDARA CE SILA Onde histórias criam vida. Descubra agora