Part 77

269 17 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!



P1️⃣1️⃣1️⃣
A hankali take zuwa makarantar ta kuma tana samun cigaba saidai cikin daya takura mata duk da bawai laulayi take yi ba amma yana girma fiye da qima kusan yana cikin watannin sa na hud'u amma inka kalle shi saika rantse ta shiga watan haihuwar tane,likitoci suna bakin qoqarin su wajen ganin sun duba meye matsalar saidai suce mata ta kwantar da hankalin ta komai na tafiya daidai.

Tun tana iya jurewa har abun ya fara bawa su Ansaar da ita kanta tsoro don haka ranan da sukaje awo Ansaar yasa likitan a gaba a kan lallai sai ya gaya masa meye matsalar da cikin keda girma haka.

Likitan ya kalle shi jiki a sanyaye yace "Kaine mijinta?"

Girgiza kai yayi yace "Ni d'an ta ne."

Gyad'a kai yayi yace "To gaskiya kayi haquri baza mu iya fad'a maka komai ba saidai muna tabbatar maka ita da abinda ke cikinta lafiya suke babu wata matsala tattare da ita."

Ansaar yayi shiru cike da takaici ya kasa cewa komai can dai ya miqe kawai ya fice yaje yaja hannun Iyyah tana tambayar sa me sukace masa ya cije gefen lower lip d'insa yace "Yaqi fad'a min komai yace sai dai in Abbuh yazo."

Gyad'a kai tayi cikin dauriya don da wahala kaga tana raki tace "Amma ya tabbatar maka komai lafiya?"

Kai ya jinjina yana bud'e mata qofar mota yace "Yace komai lafiya lau."

Ya sake gyad'a kai tace "Shikenan karka damu in sha Allahu koma menene zaizo da sauqi tunda ya fad'i haka."

Shidai jinta kawai yake amma ya za'ace komai lafiya alhali shi baiga lafiyar ba anan.

Haka suka isa gida su Hinde suka cigaba da hidima da ita.

Koda cikin ya shiga watanni shida,dole ta ajiye semester saboda bama ta iya doguwar tafiya balle har ta iya shiga lectures Ansaar fa ya shiga damuwa matuqa da gaske kuma adaidai lokacin Asiya itama ta soma laulayi mai azabar wahala don ita saida ta koma kullum saidai a samata drip.

Abu fa ya taru ya cakud'e masa ga ayyuka a office don dole daya ga Abbuh yana neman kaiwa watanni uku bai zo ba ya neme shi a waya.

Ya tabbatar masa ayyuka ne suka cakud'e masa shima amma hankalinsa na kansu kuma wani satin in sha Allahu yana hanya.

Ansaar yace "Don Allah su taho gabad'aya don Allah."

Abbuh yayi murmushi yace "Tahowa gabad'aya bazai yuwu ba don su Little na school basuyi hutu ba saidai ko iya Mommah."

"Dasu Aseep don Allah."

Dariya yayi yace "Zan fad'a musu naji ko zasu zo."

Ansaar ya sake cewa "Harda su Aunty Hamdiyyah fa."

Abbuh yace "Aa rigima kake ji Ansaar su wad'annan suka gidajen su ya zanje nace a bani su."

Murmushi yayi shima yayi yace "Don Allah Abbuh suzo Iyyah ta haihu a gaban su."

Abbuh yace "Toh zan fad'a musu suma idan mazajen su sun amince zamu taho."

"Toh su Uncle Hameed fa?"

Cikin mamaki Abbuh yace "Ha'a Ansaar wanne gayya kakeyi haka ne lafiya?"

Dariya yayi yace"Lafiya lau kawai ina son wannnan karon naga gidan mu ya cika ya batse ana ta hira kamar koda yaushe."

Dariya Abbuh yayi yace "Toh karka damu Allah ya bamu iko."

"Amin."

Daga haka suka yi sallama,ya nemi num Sabeer ya dinga roqon sa ya amince zasu zo da su Hamdiyyahn haka ma Sameen shi ko roqon nasa ma baiyi ba ya amince yace suna hanya.

***
Abbuh dai dagewa yayi ya yakice komai ya tattaro kan iyalan sa sukayo Uk don tunda Ansaar ya kira shi yasan lallai da matsala ne kuma daga yanda yake masa magana ma da damuwa a cikin ta saidai yana ta qoqarin dannewa ne.

Yanayin da suka same ta ya basu mamaki da tsoro Mommah harda kukanta tana cewa gaskiya aje a cire abinda ke cikin inya so a sa a incubator tunda ta shiga watanta na bakwai.

Washegari suka je asibitin wanda ita sai wheelchair suka bayar aka dora ta.

Likitan suka gaisa da Abbuh ya tabbatar shine mijinta nan ya tabbatar musu saidai ayi mata aiki don cikin na girma fiye da yanda ake zato fa.

Haka akayi Abbuh ya sa hannu akan za ayi mata aiki washegari a cire abinda ke cikin.

A daren babu wanda ya runtsa daga cikin su kowa da fargabar yanda gobe zata kasance yake amma dai haka suka wayi gari a asibitin kuma qarfe hud'u na asuba aka shigar da ita theatre room harda Abbuh.

Duk a reception aka barsu suna ta zirya da kai kawo kowa da abinda ke ransa.

Sun jima sosai don sun kam sun gama qosawa a fito suji me ake ciki,bayan tsahon lokacin dai likitocin da suka jagoranci tiyatar suka fito daga bayan su nurses suka gangaro gadon Iyyah tana kwanta tana bacci abinta.

A bayan su gadon jarirai ne da aka zubo jariran da aka cirowa Iyyah.

Bayan su Abbuh ne cike da farinciki suka bi bayan su ne Mommah tana shiga d'akin ta nemi kusurwa ta durqusa tayi sujudul shukhri ta d'ago tana goge hawaye tana maimaita "Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahi."

Su kam yan ukun Abbuh ba bakin magana kowa mamakine fal fuskar sa sai raba kallon su suke tsakanin Iyyah dake bacci da kuma yaran da suma baccin suke.

"MashaAllah tubarkalla." Shine abinda lubna ke ta faman fad'a itama da take da nata cikin na watanni biyar har ya turo riga abun sha'awa.

Shiko Abbuh tsabar murna da farin ciki kewaya yaran yake ya dauki wannan ya ajiye ya d'auki wancen ya ajiye ya kasa riqe daya takamaimai sai zagasu yake yana tofa musu addua har da hawaye a fuskar sa kai kace wannan ce haihuwa ta farko da akayi masa.

Well fans ayi guessing wai yara nawa Iyyah ta haifa ne??

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now