Part 14 Of Qaddara ce sila

300 22 0
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

*'''Duba kuma da wata mai alfarma da muke shirin shiga na Ramadan zan dakatar da typing har sai bayan sallah idan Allah ya kaimu da rai da lafiya dafatan Allah yasa muyi ibada kar6a66iya ya samu cikin entattun bayi ya ara mana rayukan muga na bad'in badada'''*

'''Ku sani ZahraArkel nayin ku irin sosai d'innan yanda ya kamata fa ana mugun Manne fans.'''

_Page 14_








●●●●Sannu kan hankali damina ta fara sauka sanyi da ni'imar damina kuma ta mamaye ko'ina a cikin duniya.

Safiyar litinin ce wadda a daren ta an maka ruwa kusan an kwana ne ana yinsa,Iyyaah riqe da hannun Ansaar suna tafe yana ta mata shirmen labarin daya saba bata har suka isa makarantar ta miqa shi aji ta kuma ja masa kunne da kada ya yarda ya fito sai tazo d'aukar sa.

Da to ya amsa mata ya zauna inda ya saba zama can kusurwa qarshen aji don fafur fa 'yan bencin su sun hanashi zaman kujerar duk randa ya zauna kuwa sai ya daku a wajen su.

A hankali en ajin suka dinga taruwa kowa da abokinsa wasu ma gang guda ne suke shigowa sunata wasanninsu.

Qarfe takwas saura aka tafi assembly aka hau layi kowanne aji bisa ga al'ada saidai Ansaar nacan baya don ba wanda yake qaunar ya ganshi a gabansa bayan ma can yake ya rabu da d'ali6an don duk wanda ya kuskure ya ta6a shi sai yaji ba dadi tun a filin balle kuma yace zai jingina dasu.

Haka aka gama assembly kowanne d'alibi ya wuce ajinsu ga Ansaar ma hakane ya kama hanyar aji shi d'aya yana tafe yana kallon yanda 'yan ajinsu keta kokoye kokoye wanda a son ranshi irin na yaro shima ayi dashi amma koda basa d'in dashi kallon su na sashi nishad'i wani abun har dariya zaka ga yayi don yanda ya burge shi wanda su sam yaran basu lura ma da shi ba har suka shiga aji.

Suna shiga mallamin ajinsu M.Marwaan ya shigo shima yana hangar Ansaar a lungun daya saba zama ya doka masa tsawar data firgita shi ya miqe yana karkarwa idon sa har ya tara ruwa.

A fuska d'aure yace "Bana hana ka zaman wajen nan ba?bance ka dinga zama a kujerar kaba?"

Cikin rawar murya Ansaar yace "Mallam sun hanani zama ne."

A fusace yace su fito en teburin,ba musu suka fito suna zabgawa Ansaar harara da qunqunin zai sani ne,ai ko suna isa gaban aji ya shiga laftar su da tambayar su me yace dasu rannan ba yace su dinga zama dashi ba?Lado cikin kuka yace "Nifa Innata ce tace kada na yarda na zauna kusa da *SHEGE* domin Allah zai qonani a wuta tunda shi najasa ne kuma Allah baya son najasa."

Ran M.Marwaan ya sake 6aci a fusace ya zabga masa bulalar hannun sa yace "A wanne hadisin ko ayar hakan d'in yazo ashe baka da mutunci bansani ba."

Yana soshe soshe yana kuka yace "Wallahi haka tace min."

Sosi yayi musu lilis ya kuma gargad'i sauran 'yan ajin akan Ansaar da dukansa ko tsangwamar sa da kakkausar murya yace su su zauna a qasa na yau shi kuma ya koma kan kujerar,haka suka je suka zauna suna tashan kuka abinsu suko ya d'ane kujera.

Shikam Ansaar ya gama tsurewa yasan wannan dukan da Mallam ya musu yasan duk da gargad'in da yamusu bazai hana su jibgar sa ba idan an tashi yasan akansa abin zai qare amma dai ana tashi zai gudu bama zasu ganshi ba ko kuma Innar sa tazo ta d'auke shi da wuri.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now