31 Qaddara ce sila

279 17 2
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!




*My cwt Besty Oum Bae this is yours,kiyi yanda kike so dashi Allah ya raya mana khadija ya kawo mana triplet soooooon in kinga dama kada kiba Nabeeha (My troublemaker) ta karanta sai ta biya 1k🤓😂 luv u lodi lodi and thanks for everything*

Page 42-43
Kasancewar Saratu kyakkyawa data zarce da yawa daga sa'annin ta dad'in dad'awa ta fito daga babban gida ya sanya ta zamo tarauruwa tsakanin matasan garin kowa so yake ace shine nata wannan tasa kowa ma zuwa yake wajen ta saidai kaf d'insu tana kulasu ne bisa tilashin mahaifiyar ta dake nuna mata lokaci ne a gareta da zata za6a ta darje a cikin 'ya 'yan manyan garin dake ta bibiyarta kamar Lado daya kasance guda daga yaran manyan mutane a garin mai sarautar mai unguwa sannan babban manomi da kowa yasan da zaman sa har a maqotan qauyensu.

Tun tana noqewa da nuna mata itafa babu wanda yayi mata musamman Lado da tun tasowar sa dama taqadari ne mara jin magana mara kirki kuma mai shaye shaye harda sara suka da sunan farauta.

Mahaifiyar ta kan nuna mata duk zai daina dga zarar ta aure shi wannan ba matsala bace ita kam tayi aure a babban gida tayi babban gado shine babban burin ta.

Wannan abun yasa Hansai ta qulla qawance da mahaifiyar Lado wanda wannan qawance yasa aka kori kowa ma sai shi dai Ladon shi kad'ai ne idan yazo wajen Saro take tilasta mata saita fita wataran sai tayi kamar ta dake ta.

Koda ta fita kullum ya6a masa magana take zuwa tayi ta dawo amma dake qwayar bata gaya masa daidai shi a kalaman soyayya ya d'auke su.

Tsahon wannan lokaci kuma Saro na maqale da soyayyar Ansaar tana neman damar dazata bayyana kanta kasancewar ta bafulatana ta kasa tunkarar sa kuma cikin qawayen ta babu wanda zata iya tunkarar da maganar sa musamman da yake kowa ma qyamar yake duk da yafi akasarin mazan garin komai amma kam abun bazai zo da sauqi ba indai wani yaji zancen don haka ta danne abinta a ranta har suka kawo wannan mataki da suke kai a yanzu.

*Cigaban labarin*
M.Ladan na shiga gida yasa aka kira masa Saro suka shige d'akinsa saida ya zauna ya daidaita sosai sannan cikin taushin murya yace "Saratu."

A hankali ta d'ago kanta tana kallon sa sannan tace "Na'am baba."

Ya gyara murya sannan yace "Shin yaron nan Ansaar da kike tsayawa dashi kina son shi kuma shi kika tsayar a wanda zaki aura?"

Shiru tayi kanta a qasa amma fuskar ta fal da murmushi tana ta wasa da santala santalan yatsun ta da suka qunshin dungulmi sukayi d'au dasu gwanin sha'awa.

Hakan da tayi ya bashi tabbacin lallai tana son shi kenan kuma amsar tambayar sa Eh ce don haka yace mata "Tashi kije Allah ya zab'a abinda yafi zama alkhairi."

A ranta ta amsa da amin amma a fili miqewa kawai tayi cike da kunya da nauyin mahaifin nata ta fice ran ta qal da farin ciki.

Mahaifiyar ta na tsakar d'akinsu da qannenta suna zaune suna hira gefe Bukar ne keta faman zuba da bawa mahaifiyar tasu labarin wani abun da ita bata gane zancen ba ta nemi waje ta zauna tare da jawo littafin ta na hadith tana dubawa.

Hansai ta kalle ta tana fad'in "Naji ance baban ku na kiran ki daga ina kike?"

Sai da ta d'anyi guntun murmushi sannan tace "Daga wajen sa nake tambaya ta yayi abu."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now