Part 9 Of Qaddara ce Sila

322 23 1
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

                         _Page 9..._

●●●Basu suka dawo daga gaishe gaishen da suke ba sai gab da magriba a gajiye suke liqis tace su wuce gidan su saboda twins da kuma Baffan ta da bata gani ba tsahon yinin.

Innah Jumah na wajen tumakinta tana basu dusa suka shiga da sallama,daga inda take ta amsa ba tare data d'ago ba,Hajaarah dake rubutu a littafin ta na islamiyya da alamu assignment take yi ta d'ago cike da fara'a tana fad'in "Aa Momman Hamdy sai yanzu?"

Tana dariya tace "Eh wallahi Ayar Allah sai yanzu,ai kin ganmu a gajiye muke tulis damu."

Innah Jumah dake ta ta6e baki tana qarewa Kubrah kallo tace "Uhyum kuma gajiyar anan ake huce ta ko?"

Da yaqe cike da tsoron karta dizga ta duk da kasancewar Kubrah er gida amma dai dangin mijin tace ita ai tace "Innah ai dama shirin mu kenan muzo muga Baffah."

Sake ta6e baki tayi tana zama tace "Uhmm yayi masu Baffah,to baya nan da kunje da daddare kwa dawo."

Duk da a gajiye take hakan bai sa ta kasa yunqurawa ba ta miqe tare da sunkutar Baby Salmah da Hajaarah ta kar6e ta tace "Kubrah muje da daddare ma dawo."

Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta kalli Innah Jumah dake ta yatsine yatsine tace "Sai anjima Innah."

Ta gefen ido ta kalle ta tace "Toh mu jima da yawa."

Itako Momman ko tari batai ba tayi gaba don ranta yayi masifar 6aci da d'acin zuciya ta tafi gidan Ayyah don ko a hanya bata kula zancen Kubrah dole ita kanta taja bakinta tayi shiru ta qyale ta don ta fuskanci irin cikin mummanan 6acin ran da take.

Suna isa ta bawa Kubrah Baby Salmah tace ta wuce da ita wajen Ayyah zata d'an kwanta ta huta,ta wuce d'akinta kai tsaye saida ta turo qofar ta fad'a gadon ta sannan ta fashe da wani irin kuka mai ciwo ita 6acin ranta bai wuce yanda itada gidan uban ta ya gagare ta tana budurwa yanzu ma da zuwa kawai zatai fisha ta tafi gagarar ta yake neman yi a dalilin Innah Jumah itada mahaifinta babu halin su yini tare indai ba bata nan ba.

Sosai taci kukan ta har kanta ya soma ciwo a haka Basheer ya shigo ya sameta kwance cikin bargo bata daina hawayen ba har a lokacin zama yayi bakin gadon yana kallon ta tsahon lokaci kafin yace "Tashi zaune."

Ba musu ta miqe ta zauna tana sharce hawayen ta tare da goge su da tissue.

Saida ya sake kallon ta na wasu daqiqu sannan ya soma magana cikin taushin murya "Menene kuma yanzu meya faru?"

Kuka ta sake fashewa dashi tana girgiza kai alamun abun na mata ciwo sosai a rai.

Maimakon magana sai ya haye gadon ya shiga bargon shima tare da janta jikinsa sosai yana shafa bayanta alamun lallashi,a hankali yanayin ya dinga yi mata sauqi zuwa wani lokaci ta daina kukan sai ajiyar zuciya akai akai ganin haka yasa ya sake ta ya d'ago ta yana kallon kumburarrun idanuwanta yace "Inajin ki meya faru?"

A hankali ta zayyane masa abinda Innah Jumah tayi musu itada Kubrah,ta qarasa da "Nifa kasani ina son kasancewa da mahaifina ina son zuwa gidan mu nima ace yau kamar kowacce d'iya nima naje gidan mu da sunan kwana ko wuni kai ko hutu ma amma qiri qiri yinin ma nema yake yafi qarfi na saboda Innah Jumah,na rasa mena tsare mata me kuma nake rage mata nida yarana idan munje gidan alhali gidan na ubana ne."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now