Sharhi

3.6K 217 13
                                    

*EL-MUSTAPHA*

17th Nov,2018

HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)


Fertymerh  Xarah💞



         *SHARHI*
                    daga
                         kungiyar

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*
( Home of perfect and expert writters)

     El'mustapha  labari ne daya qunshi abubuwa da dama way'anda suke faruwa awannan zamanin namu,
Abubuwa  ne da suke faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum."

El'mustapha ya kunshii jarumai irinsu JIDDAH  da kuma UWANI, dashi kanshi adon tafiyar EL'MUSTAPHA, sannan kuma aka sakayo mana BANAN aciki."

El'mustapha labari ne daya kunshi

#k'addara."
#cin amana."
#ilimantarwa."
#fad'akarwa."
#yadda zakayii tarbiyar yaranka."
#wa'zantarwa."
#Dakuma nishad'antarwa."
#hakurii."
#Tausayi."

  *El'mustapha*= hak'ik'a el'mustapha shine jigon wannan labari, El'mustapha ya kasance mutum mai sanin darajar iyalinsa, hankalii, hakurii, martaba dakuma mutunta iyalinsa, matashine mai ji da kud'i, Mulkii, dakuma ilimi, ga kuma uwa uba kuma mutum ne shi mai addini."
El'mustapha yakasance mutum mai kwarjini da shiga zuciya, ga kuma kyau, El'mustapha yana kula da matarsa sosaii, wanda hakan yajawo y'ar uwarta da kuma mai aikinta fad'awa soyayyarsa, dan suma sunason samun kwatan kwacin farincikin dayake baiwa matarsa."

     *JIDDAH* hakika samun mace mai zuciya dauriya hakurii, juriya, tausayii rigon amana yayi wuya awannan zamanin namu, Amma kuma Allah sai ya had'awa wannan duka abubuwan,  majidda mata awajen  El'mustapha."

JIDDA macecce mai matuqar son mijinta sosai, Tanayi masa biyayya bata d'aga muryarta akan mijinta, a kullum ba tada buri daya wuce taga y'ay'anta da mijinta cikin farinciki,

JIDDAH  tana da qoqari wajen farantawa duk wani wanda yake tare da ita.

" JIDDAH  marainiyace bata da uwa kuma bata da uba, Allah ya bata marik'anta wanda suka riketa tsakanii da Allah suka bata tarbiya, suka raineta kamar yanda sukayi wa y'arda suka haifa acikinsu, Allah ya dubii maraicin JIDDAH  ya bata miji mai mugun son ta da kuma kula da ita wanda ko wace mace zatayi sha'awar samu."

    *UWANI*" uwani itace musabbabin sanya y'ar uwarta jidda cikin wani hali, uwanii ta kasance maiciya amana, kuma cin amanar ma way'ar uwarta, kwata-kwata batad'auki tarbiyar da mahaifanta sukayi mata ba, kai halin uwani dai ba'acewa komai, sai dai Allah yaraba mu da hali irin nata."

*BANAN*" banan takasance y'ar aiki awajan JIDDAH  yayin da taraineta tun tana qarama bata kyamarta, ta sanyata a makaranta, amma kuma daga baya tazo ta nuna tanason mijinta."

*K'ADDARA* Hak'ika jiddah  taga  kaddori da dama, jiddah  ta kasance mace mai kishin  mijinta, tana son mijinta fiye da komai a fad'in duniya tana kishinsa sosai bata jin zata iya had'ashi da kowace irin mace a duniya amma kuma Da kaddara ta tashi fad'a mata sai ya juye ita da kanta take roqonsa yaqara aure, ya aurii y'ar uwarta dan batason rasa y'ar uwarta."

*CIN AMANA* mijin yar uwata nakeso, farin cikin dayake baiwa y'ar uwata nake son samu fiye da hakan, koda wannan kalamai da uwanii tayii ya kasance cin amana, tabbas uwani taci amanar y'ar uwarta, ta yaudare ta ta hanyoyi da dama domin ta cimma burin ta na ganin ta raba wadannan masoyan,  bayan wannan kuma take qoqarin kashe yar uwarta da yaronta duk saboda mijinta duk da tayi sanadiyar nakasa mata qafa. 

   BANAN" banan bata kyauta ba na son mijin jiddah duk da halacci da kyautatawar da tayi mata a rayuwa.

*ILIMANTARWA*" hakika wannan littafi ya ilimantar damu kuma ya nuna mana muhimmancin haquri da yarda da qaddarar da Allah ke dorawa bawansa domin ya jarabcesa.

El'mustapha Where stories live. Discover now