54

4.6K 424 47
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

54


   Shiru dakin yayi, kowane da saqe saqen xuciyarsa.

Hajiya tayi sallama ta shigo da jaririyar a hannunta tana kuka, a tunanin ta jiddah barci take yanda taga ta lumshe idanuwanta.

Yarinyar nan sai kuka take tun daxu, dama jiddah ba wani abin kirki ta bata ta sha ba,

El'mustapha ya karbe ta, hajiya ta juya ta bar dakin, tsurawa yarinyar idanu yayi, shi kadai yasan tunanin me yake yi,

Ya dago yana kallon jiddah dai dai lokacin ta bude idanuwanta suka hada ido, turo baki tayi ta harare sa tana dauke kanta gefe,

Yace gata ki bata tasha, tayi masa banxa kamar bata ji ba, ya taso da jaririyar yana miqa mata,

Just feed the baby jiddah don't involve her  cikin baqin halin da kika kwaso tsakanin jiya da yau.

Ta bude idanu tana kallonsa, why should I feed her? Inaji kaima kana da shi a qirjinka, ka bata ta sha kada ta dauki baqin halin da na kwaso.

Wai meke damunki ne jiddah, har akwai ranar da xaki iya min rashin kunya, idan nace xanyi auren akwai wanda ya isa ya hana ne, ni ba mijin mace hudu bane ko anyi ni ne saboda jiddah kadai, ko kin manta sanda kike roqona akan nayi aure, You even cry for that, idan har xaki iya tilastamin auren wata yanxu banga abinda xai daga hankalin ki na kishi ba, gida nane I have the right nayi duk abinda nake so kuma nasa duk macen dana ga dama,kiyi abinda duk xakiyi.

Idan har kana tunanin ban isa na hana maka auren ba kaje kayi ni kuma xan nuna maka gida ba nawa bane amma na fika iko dashi dan ba shegiyar da xata xauna a wannan gidan wallahi sai dai na qona shi duka........ Kuka yaci qarfinta, Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un ta fada a hankali cikin kuka, bata taba tunanin akwai ranar da xata iya maidawa el'mustapha magana ba ballantana ta kai ta da yana fada tana fada,

Cike da bacin rai ya miqa mata baby, feed her jiddah.

Nace baxan bada ba, nawa ne ko shima xaa min iko akan shine, ka bata ta sha ko ka kaiwa banan din ta shayar da ita.

Xaiyi magana wayar sa ta dauki qara, yana ganin anty ikram ya dauka da sauri, jiddah ta kafe shi da idanu.

Autan mama yarinyar nan banan tace bata da lafiya na taba jikin nata naji xafi sosai shine nace ko a dawo da ita ne a duba ta tun da duk asibiti ce,

Ya dubi jiddah yanda ta kafe shi da idanu kusan Ma kamar tana jiyo abinda ikram din ke fada, ya tsinci kansa da tsoron jiddah,

Yace aa basai kun dawo ba idan kun sauka taje asibiti amma bari yanxu xan x....

Kaje ina?yaji muryar jiddah baisan sanda ya katse wayar yana kallon taba,

Xanje na duba yarinyar mutane...

Wallahi baxaka je ba, kaje ka duba yarinyar mutane You are not even ashamed of saying that, sai kace akan ka take bani ce na dauke ta aiki ba, wai me kake nufi el'mustapha?

Ke xan ma wannan tambayar jiddah, me kike nufi, sam wannan abin da kika dauko bai dace dake ba.

Baxai taba dacewa dani ba idan har baka cire wannan yarinyar a xuciyarka ba,

Don't you understand, so nawa xan gayamaki bana son yarinyar, ko sai na rubuta a goshina  na nunawa duniya bana son banan, saboda yarinyar nan kike min rashin kunya, telling me any word da yaxo bakin ki, abinda baki taba min ba shi kike min a yanxu, shikenan ki cigaba and don't feed the baby sai me, sai aka ce maki baxata rayu ba, mtsewwwww ya fice da yarinyar a hannunsa, ta bisa da kallo tana sharar kwallah,

El'mustapha Where stories live. Discover now