Labarin Zubaida

4.7K 449 39
                                    



'Exactly....

Rumaisa ta fada tana kallon Ammi,

Wallahi ammi sai da kika fada naga hakan,

Afiya tace yeah is true tana kama da Anty Zubaida, but ita wannan jiddah who is she?

Umman tace nima tun da na ganta naga tana kama da Zubaida, wannan kuma bamu santa ba.

El'mustapha ya dubi sarki,

Ranka ya dade, wacece zubaida da kuke magana, jiddah matata ce, mahaifiyar ta tabar duniya tun jiddah bata da wayo haka ma mahaifinta, iyayen dake riqon ta a yanxu suna da tabbacin cewa iyayen jiddah sun dade da mutuwa, wace Zubaida kuma ake magana?

Kwantar da hankalin ka yaro na, ya sunan ka? Merah ya tambaya yana kallon sa.

Sunana El'mustapha,

Sarki yace Zubaida 'ya ta ce, ma'ana d'iyar qanina ce itace babbar yar'sa.

Zubaida yarinya ce mai nutsuwa da haquri duk gurinnan kowa yasan da haka, duk suka jinjina kai cikin gamsuwa.

Kowa yasan zubaida bata da hayaniya kuma bata da son abin duniya kamar sauran qanninta maxa domin ita kadai ce mace.

Zubaida ta fara canxa hali daga ranar da ta hadu da wani saurayi a makaranta can London.

Ta dawo wata irin yarinya da bata jin maganar kowa saboda yaron, shi kadai xai gaya mata taji ko ta bari, ta dauki soyayyar yaron ta saka a xuciyarta wanda ta kai ko karatu ta daina maida hankalinta akan sa.

Duk mutunci irin na family din merah sai ga zubaida ta dawo da wata dabi'a ta marassa mutunci, tana shan wannan abin da naga kwanaki sultan yana sha har na hanasa, menene shi ya tambayi umma yana kallonta.

Tace ranka ya dade bansan da wannan maganar ba, qila hajiya ce,

Ammi tace wannan abin mai fitar da hayaqi kake nufi, kamar shisha naji suna cewa.

Yace yauwa, ita, zubaida da shan wannan abin, hankalin mahaifin ta ya tashi ranar da kanshi yaxo ya sanar dani halin da ya sami zubaida, tana mace ta lalace ina ga sauran maxan.

Nasa aka kira min ita taqi xuwa, sai na aika mata Maina saboda shi nasan tana tsoron sa baya sake mata fuska.

A tare suka xo, kallo daya nayi wa yarinyar na gane bata cikin nutsuwarta kwata kwata kamar ba zubaida ta mu ba,

Fada da nasiha ba wanda ban mata ba anan, ta kuma nuna ta daina sha.

'Ashe a boye tana sha, ta girmi Maina sosai yana matsayin qanin ta amma shi xai iya mata magana taji, tun daga lokacin da ya mata magana kuwa ta daina sha.

Bayan wani lokaci ta koma makaranta, Allah ya sa a lokacin naje London yin wani abu, sai na kai mata ziyarar baxata kamar yanda nake kaiwa Maina da Afiya sanda suna makaranta.

'Na same ta da wannan yaron cikin gidanta, banda gansu suna wani abin Allah wadarai ba amma alamu sun nuna hakan daga yanda na same ta da wasu kaya a jikin ta shi kuma da gajeren wando.

Duk mutunci da tarbiya irin na zubaida har tasan ta kawo wani namiji ta xauna dashi a gidan ta ba mijin auren ta ba,

Ban mata komai ba amma raina ya baci sosai, na saka ta hada kayanta na dawo da ita Nigeria.

Duk kukan ta da magiyar ta bai sa na barta acan ba kuma na saka maina ya dake ta da bulala kafin iyayenta suji me ta aikata.

Dalilin wannan mahaifinta ya fitar mata da mijin aure, a lokacin ta nuna masa bata son xabin da yayi mata lallai ita tana da wanda take so suka yi alqawarin aure.

El'mustapha Where stories live. Discover now