19

3.6K 326 2
                                    

*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

19

Sum sum uwani tabar falon ta nufi dakin ta.

Daren ranar suna kwance da el'mustapha,

'ina so naje birnin kebbi gobe tunda xakaje xamfara, dama ina so na duba hajiya kwana biyu banje ba.

'meyasa baxaki bari idan nadawo muje tare ba, nima ina so naje na gaidata.

'A'ah, ina son naganta ne baxan iya jiran ka ba, please let me go,

'akwai abinda kike boyemin jiddah, my eyes are on you, kina ganin kamar hankalina ba guri daya yake ba, kina cikin damuwa kike boyemin, meyasa kika canxa min jiddah, ashe dama akwai lokacin da damuwar ki baxata xamo tawa ba, why did you change, kigayamin damuwar ki, ina so nasani a yanxu.

Tayi qoqarin saita numfashinta, jikinta ya dauki rawa, hawayen da take boyewa suka soma xarya,

'amma kasan ina son ka ko?

damuwar ki nake son ji, ba son da kike min ba, idan har ban cancanta nasan damuwar ki babu mgnr wata soyayya da kike min, you are deceiving yourself jiddah.

Ba yanxu take son sanar dashi ba har sai taji raayin iyayen su tukunna, tasan halin el'mustapha sarai xai iya hanata tafiyar idan batayi da gaske ba, hannunsa ta riqo tana kallonsa.

Uwani ce damuwa ta you know, ban gayama dalilin kwanciyarta asibiti ba, likitoci sunce tana cikin damuwa kuma ta kamu da ciwon xuciya a kowanne lokaci xata iya rasa rayuwarta, nayi juyin duniyar nan ta gayamin damuwar taqi shine nake so naje na sanar da hajiya kada wani abin yaxo ya sameta batare da sanin su ba.

Yaja numfashi yana kallonta, you are right jiddah na fahimce ki, amma tare da uwani xakije ne?

Aa bana son tasan da tafiyar Ma,

Allah ya tsare ya kaiki lafia, amma ni bana son kina damar da xuciyarki saboda uwani, kinsan dalili? Ta girgixa kanta tana kallonsa,

Saboda uwani bata taba damuwa dake hakan ba, akwai wani abu dana ke boye maki game da uwani wanda ke baki sani ba, tun daga lokacin nadaina ganin mutuncin ta.

Xuciyar jiddah ta tsananta bugawa to kodai el'mustapha ya san uwani na sonsa ne?

Sanda akace xaa yi maki c.s ga haihuwar twins wlhy uwani is happy, ina kallonta babu damuwa a tare da ita kamar iyayenku, hajiyarku harda kuka tayi, did you know that, jiddah ta girgixa kanta.

Duk wani movement din ta a hospital ina lura dashi, har sanda akace kin haihu da kanki, ol what uwani is asking a lokacin likita tana da rai ko ta mutu, kallon da nayi mata ya sanya mahaifinta bige mata baki yana salallami, bansan meyasa ba from that day nasaka idona akanta musamman saboda ke, amma ke saboda rashin lafiyarta kin rude kin shiga damuwa, kin tura ya'yanki inda mama saboda damuwar uwani ba lafiya, kin daina kulawa dani sai Ma nida ke qoqarin kulawa dake saboda uwani, You have to put eyes on her, kidaina yarda da ita cos ni ban yarda da ita ba again kuma bana qaunarta ko kadan, sorry to say idan kinji xafin kalamaina but am telling you the fact, kuma ban gaya maki mgnr saboda xumuncin ku ya lalace ba, rayuwar nan wanda ka yarda dashi shike cutar da kai sai a hada kai dashi a cutar da kai, ko ya xame ma sanadiyar rasa farin cikin ka, idan Ma bai xama makashin ka ba.

Shiru tayi tana saurarensa, maganar sa gaskiya ce, uwani tana son rusa farin cikinta saboda son el'mustapha, no it can be possible, uwani baxata mata haka ba tasan uwani tana son ta kuma tana nuna mata soyayya, gashi sanadiyar el'mustapha tana neman rasa rayuwarta, idan har mgnr el'mustapha gaskiya ce uwani ta cutar da ita Allah baxai barta ba kuma xai saka mata, duk wanda yayi niyar aikata alheri baxai taba tabewa a rayuwa ba, taimakon uwani xatayi saboda iyayenta kada ta rasa rayuwarta dalilinsa.

'Wannan tunanin yayi yawa jiddana kixo ki kwanta, el'mustapha need you today komai ina so daga jiddatulmusty,

Murmushi tayi tana kallonsa cikin so da qaunarsa, tau baban biyu bani minti biyar kacal na shirya,

Janyota yayi, ya kwantar da ita, a hakan nake son jiddana, bana son wani abu da xatayimin saboda ta birgeni, kome jiddah xatayi ina son ta, tana birgeni, kuma duk wanda baya son jiddah nima bana son shi.

Hannu tasa ta rungumosa sosai, yayin da ya hada fuskarsa da tata yana shaqar qamshin jikinta.

*

'Washe gari el'mustapha ya nufi xamfara, jiddah Ma ta shirya sai da xata tafi ne ta sanar da uwani xataje birnin kebbi kan maganar taji raayin iyayen idan sun amince.

Abu biyu ne ya hadewa uwani farin ciki jiddah ta amince xata bari ta auri el'mustapha da kuma yanda xata shige mata gaba a auren, sai fargabar abbanta wanda take ganin da kyar ne xai iya amincewa da auren da kuwa ta shiga uku.

Sai dai abinda jiddah ta jiyo uwani na fada a waya yayi matuqar bata tsoro da tada hankalinta matuqa wanda ya xama dole ta amince da auren el'mustapha da uwani idan ba so take ta ruguza mata farin cikinta ba.

'Walllahi baxan haqura da el'mustapha ba surry kidaina min mgnr bana so, da kinsan yanda numfashina ke bugawa tare da qaunarsa da baki nemi in barshi ba, ke idan fa ta kama ko nijar xan iya xuwa inda boka domin farin cikina.

Hankalin jiddah ba qaramin tashi yayi ba jin uwani ta ambaci boka, abin ya kai har haka, meyasa uwani keson ganin bayanta, bata nunawa uwani taji komai ba sai dai kallon da takewa uwani a yau daban ne da irin wanda ta saba yi mata a matsayinta na yar'uwa.

Babu kunya ta soma yiwa jiddah godiya ta rakata har harabar gida, inda mota ke jiranta, police biyu ne tare da ita wadanda xasuyi tafiyar, ta bude motar ta shiga tana adduar tsari a xuciyarta.

Tun da jiddah taje masu da mgnr da abinda ya sami uwani a asibiti iyayen suka soma kumfan baki, basu yarda da maganar ba kuma basu yarda uwani ta auri el'mustapha ba, domin ya xama cin amana garesu,

Duk iya qoqarin jiddah ta kasa shawo kansu sai Ma sabani da suka samu da hajiya wanda ta dauki fushi da ita mai tsanani,

Dalilin hakan yasa jiddah ta fasa komawa a ranar dole sai tayi convincing iyayen har su amince da auren bata son abinda xai taba mijinta da lafiyarta dan baxata iya  gayamasu abinda taji uwani ta fada a daxu ba.

My wattpad phertymerh1

El'mustapha Where stories live. Discover now