20

3.9K 324 6
                                    

*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

Mom of 12, I like your comment 👌🏻


20

'Washe garin ranar sama sama suka gaisa da Hajiya,

'hajiya kiyi haquri bana son fushin ki ko kadan, tunda na taso ban taba fuskantar wannan canjin daga gare ki ba, ki sassauta min fushin ki agareni ba alkhairi bane.

'baxaki taba ganin canjin fuskata har sai kin janye mgnr ki akan uwani ta auri el'mustapha, Sam ban amince ba shiyasa tun farko da ta gayamin daga ni har abbanku ba wanda ya goyi bayanta.

Kallon mamaki jiddah ke mata, ashe Ma tasan da mgnr kenan, tuntuni uwani keson el'mustapha aka boye mata meyiwuwa wannan dalilin ne ya saka har ta kamu da ciwon xuciya bata sani ba.

Kuka jiddah keyi sosai mai taba xuciya wanda kukan yayi matuqar daurewa hajiya kai,

Jiddah saboda na hana uwani ta auri el'mustapha ne kike wannan kukan?

'bana son na rasa uwani ne hajiya, tare muka taso muke rayuwa tare da ita, baxan so ta rasa rayuwarta saboda abinda take so ina da iko akan sa ba, meyiwuwa el'mustapha yana cikin qaddarar mu shi mijin mu ne.

Mijinki ne jiddah ke kadai bana son kibiye uwani Sam ban yarda da ita ba, mahaifinta Ma bai amince da auren ba, tunda kinji xaki iya kije gaki ga uwani ki aura mata abinda kike so a rayuwarki amma bada yawun bakin mu ba, ina roqon Allah ya albarkaci rayuwarki jiddah ya kuma kareki ga duk wanda ya nufeki da sharri, ke yar halaq ce.

Godiya jiddah tayi ita kadai tasan abinda take ji a xuciyarta game da wannan auren, tana tsoron uwani tabi wata hanyar da bata dace ba domin ta mallaki el'mustapha kamar yanda taji tana fada, tana tsoron uwani a yau da komai nata.

Kusan marece suka iso abuja, uwani taxo yi mata barka da dawowa da son jin bayanin iyayenta daga jiddah amma bataga wannan fuskar ba, babu alamar wasa a tare da jiddah tunda suka gaisa bata qara kallon uwani ba, toilet ta nufa domin ta watsa ruwa.

Jiddana ta tafi gida ta dawo amma na rasa gane kanta, bai jira cewarta ba ya fara making love da ita,

Duk abinnan da yake idanun jiddah a lumshe suke tana tunanin watarana fa haka xaiyiwa uwani,

El'mustapha kuwa sosai ya rungumeta wata qila inda hali da ya tsaga qirjinsa ya sanyata ciki saboda qaunarta, mai yiwuwa sannan ne xai xamo contented.

Sai da komai ya lafa ya fahimci jiddah kuka take, kukan da nayi matuqar daure masa kai,

Duk sai ya rikice, kukanta da hawayenta suna matuqar daga hankalinsa

Ya tarairayo ta ya dorata akan qirjinsa, cikin sassanyar murya yake tambayar _did I hurt you jiddah?_, ta girgixa kanta, batasan yanda xatayi masa mgnr ya auri uwani ba domin tana matuqar tsoron abinda xai biyo baya, sai dabara ta fado mata, cikin sheshshekar kuka tace,

Ni dai ka qara AURE...
Sai ya janye jikinsa da nata cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwowi, tare da tsananin mamakin jin wannan kalmar daga jiddansa, wani irin kallo yake jifanta dashi,

Kafin in baki amsa jiddah ko nabi umarnin ki ina so nasan dalilinki na son na qara aure?

Saboda el'mustapha ya cancanta ace yana da mata biyu, matsayinsa ya kai, shekaru kusan nawa rabona da haihuwa ya kamata ace su Aryan suna da qanni yanxu kuma nasan kaima kana buqatar hakan,

Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken farin wata daya keto shara sharan farin labulen dakin, kafin yayi murmushin takaici ya xauna sosai ya bata baya.

Hauwa'u haihuwa ce tasa na aure ki ko kuma tun bayan haihuwar twins kin taba ganin wata alama dana nuna maki ta ina son na qara haihuwa?

Ta girgixa kanta, idan Ma haihuwar ce ke kike baiwa kanki ne? Inaji ko haihuwar ce baki taba yi ba baxaki nemi na qara aure ba ballantana Ma kin haihu,

Ni ina son yarane a ynxu el'mustapha, ina so naga yara sun cika gidannan, shiyasa nake son ka qara aure dan Allah,

Ki gayamin idan twins ba yara bane, baligai ne, yaran dake nursery 2 yanxu sune ba yara ba, wai me kike nufi ne jiddah?

Xatayi magana ya daga mata hannu a fusacce, ya isa... Ya isa jiddah.... Sai ma ya rasa me xai ce mata saboda takaici, dogon tsaki yaja ya dauki wayoyinsa ya bar mata dakin.
Jiddah ta bisa da idanuwanta karo na farko a rayuwar auren su da el'mustapha yayi irin wannan fushin da ita, amma ya xatayi farin cikin su take so, bata son a sanyasu wata hanya da bata dace ba a ruguza masu farin cikinsu ta lura uwani komai xata iya a ynxu da take ganin take takenta,

El'mustapha yayi wannan fushin dan tace ya qara aure ina ga idan yaji uwani ce xai aura?

Dole ta dage ta nuna masa fa da gaske take har lokacin da xai sauko ya amince.

Kwanaki uku suna kan wannan taqaddamar, inyayi fushi sai kuma ya sauko yayi dariya wai jiddah ke son ya qara aure, baisan jiddah ita kanta qarfin hali kawai take ba, tana matuqar axabtuwa da rashinsa kamar yanda shima yake yi.

A rana ta hudu ya kasa jure wannan tsiri da take masa na shariya, dan bashi da wannan juriya ta wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan, sai ya cafki hannunta ya langabar da kai kamar qaramin yaro, idanuwansa sun juye sun rikide xuwa ja, idan Ma wasa take zai gwada ta shima ya gani ya nuna ko a jikinsa.

Jiddah na baki wuqa da nama, kece mijin kece matar, ki xabo min duk yarinyar da kike ganin ta dace dani don bani da idon kallon wata d'iya mace tun daga lokacin da Allah ya mallakamin ke....

A hankali take dubansa yayin da gabanta ya tsananta bugawa

Ganin yanayin ta, qiris ya rage ya saki dariya amma sai ya cije,

Yace ki nema min niko acikin manya manya qawayenki ne ko riqaqqun yan boko irin su Nabila Mohd,

Haushi ya kama jiddah sosai, ga kishi ga kuma ganin ya maida abin xolaya,

Ya rungumota ta baya ya dora kanshi a kafadunta, a sanyaye yace,

'ko kin daina sona ne jiddah kike neman kai dani? A da ko kallona wata tayi wanda bai maki ba sai kin kwana baki min magana, amma yanxu duk kin daga hankalinki wai inyi aure which means kin gaji dani, kin daina sona, kina neman mataimakiya a yanxu don ki huta, meyasa jiddah, me nayi maki, wane canji kika fuskanta daga gareni domin inyi gaggawar gyarawa?

In gayamiki gaskiya baxan iya sharing kaina ba, ina da kyankyami kin sani, ba kowace mace xan iya hada jiki da ita ba, babu, ban taba ba, kuma bana fata, baxan iya adalciba, ance kuma idan baxaku iya adalciba ku xauna da daya.

Amma inkin gwammace ranar qiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same sai na auri Nabila, kinga daganan sai ku qara danqon xumunci abotarku tayi qarfi ni kuma na sami yara da yawa shikenan?

Ta ture shi da sauri duk da jikinta yayi matuqar sanyi da kalamansa domin gaskiya yake fada mata, don shi baya fadin abinda ba haka bane a xuciyar shi don kaji dadi ko dan ya faranta maka, in hakane kenan el'mustapha da gaske xai iya auren Nabila?

Magana take yi a xucci bata san ta fito ba, ya sauka a gadon ya xauna dabas akan carpet, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi,

Ni *el'mustapha* na shigesu duk yanda nayi ban yi dai dai ba, to ki fadi yanda kike so ni mijin tace ne.

Idanunta fal da hawaye wai ana wata ga wata,

Yanxu el'mustapha son nabila kake?

Yayi murmushi yana lasar labbansa,

Yaya baxan so taba tunda aminiyar matata ce kuma itace xata riqa bani ya'ya a yanxu.

'ni ba wannan nake mgn ba,

Ya miqe tsaye yana fadin koma wane iri kike magana shine, yarinyar nan rikicinki ya isheni, son ta nake na soyayya wanda ake soyewa kiyi k'uli-k'ulin kubura dani ko kiyi ta kuka har hawayen ya qare....

Duk da kuka take batasan sanda tayi dariya ba, ganin ya dawo ya rungumeta yasa ta biye masa.

She have no choice banda ta rungumi mijinta mai sonta mai qaunarta, ta nuna masa sonsa kadai ne a xuciyarta.



My wattpad phertymerh1

El'mustapha Where stories live. Discover now