51

4.6K 400 58
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

51

  Sallama take ba kakkautawa kamar wace aka ma dole.

Abba na xaune a falo yana jinta, muryarta kawai da yaji sai da gabansa na fadi, baisan me ya dawo da ita gidan ba.

Yayi shiru yana cigaba da Jan carbinsa batare da ya kula ta ba,

Ta gaji da sallamar taji baa amsa ba taja dogon tsaki, sai ta fada falon kai tsaye tana qunquni, taxo gidan ubanta ana ji tana sallama an kyale ta saboda ana baqin cikin dawowar ta.

Tana ganin abba ta xube qasa, sai gaidashi take tana washe baki,

Kallo daya yayi mata ya dauke kansa, baiyi mamakin yanda yaga ta dawo ba yama so tafi hakan lalacewa yanda xata gane duniya ba komai bace, daga yanayinta ya gane Sam har yanxu batasan rayuwa ba, bata horu ba idan har wannan shegen bakin nata bai mutu ba.

Nayi sallama baa amsa ba, naxo ina gaisuwa an kyaleni, Allah yasa dai bayan rabuwar mu abba ba matsala ya samu a kunnuwan sa ba, ta matsa kadan tana kallonsa hade da yi masa nuni da hannu irin na kurame tana tambayar yana jin ta.

Abinda yaxo ransa uwani ta sami tabin hankali, no wander ya ganta hakan, sai yaji wani iri a jikinsa ko ba komai alhakinta na kansu.

Ke....! Ya daka mata tsawa ganin tana qoqarin tabashi da wannan dattin jikinta,

'au ashe Ma yana ji, ta xauna tana tunxure baki, mutum wata da watanni baya gida kuma ya dawo baxaa tarbesa ba,

Tashi ki bar min gidana cewar abba,

Ta dago tana kallonsa da sauri baki a bude,

'Abba ina kake so naje idan na bar gidan,

'inda kika fito, ko kin manta na gayamaki ba ni ba ke, kije ki xauna da rayuwar da kika xabarwa kanki.

Ta tsuke baki hade da bata fuska, ta gyara xama tana fadi, abba ba tonon asiri ba gidan nan fa nawa ne, gado nane, saboda ni kadai kuka haifa, nayi haquri na barku ku xauna ne tunda kuna raye amma ko mutuwa kuka yi ai gida nane, gado na to meyasa kake korata cikin sa.

Kibari idan na mutu kixo kici gadon ya fada a fusacce yana tashi daga inda yake xaune, tana ganin haka ta tashi da sauri tana kallonsa jikinta na rawa,

Wai abba da gaske kake yi korata kake, ina xanje, wallahi nayi nadama kowa yasan na shiryu, dan Allah kayi haquri ka tausayamin ka barni, ta soma kiran hajiya..... Hajiya... Kixo ga auta ta dawo abba yana Kore maki ita, tana leqen hanyar dakin hajiya.

Get out please, butulu macuciya, duniya yanxu kika fara gani tukunna Ma baki ga komai ba, haqqin jiddah kadai ya isheki.

'Abba wallahi *NAYI NADAMA* baxan qara cutar da kowa ba, jamcy ce ta sakani abba dan Allah kayi haquri ta soma kuka iya gaskiyarta tana bashi haquri, fafur ya murje ido akan lallai sai ta bar gidan.

Ganin da gaske yake kuma yana gab da dukan ta ya saka ta juya tana kuka ta fito gidan, bakin gate ta rakube ta xauna tana rera kuka.

Nida gidana a hana min xama a ciki, wai mai gadi ma ya fini gata a gidan, ita hajiya saboda baqin ciki kada na xauna ko ta fito ta bashi haquri ya barni amma tana jina ta kyaleni, ta cigaba da kukan iya gaskiyarta.

Kowa ma baya sona duk inda naje sai an cutar dani, yaran unguwa sai kallona suke, duk kyawuna da gayuna sun tafi a iska, na dawo kamar wata shegia a gari, wani maraya ma yafini gata a yanxu saboda kawai na cutar da jiddah, Allah ya ga xuciyata yanxu bani da wani mugun nufi a tare dani na shiryu baxan qara cutar da kowa ba ko daukar xugar qawa ama meyasa kowa baya yarda dani ne, ya suke so nayi da rayuwata duk gata na amma dubi yanda na koma a yau kuma anqi a tausayamin, ina suke son naje, ba inda xanje na sake fadawa halaka anan xan cigaba da xama har su yafe min, ta kwanta gurin tana kuka.

El'mustapha Where stories live. Discover now