21

3.9K 290 14
                                    

*EL'MUSTAPHA*

*Haske Writers Association*
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

*Kuna Raina*
Ummy Aysher
Kausar luv
Serdia Lawal
Miss Aysher
Fido sodangi
Mmn Shakur

21


2 days......

Banan yau kinje makaranta kuwa?

'banje ba anti jiddah,
'meyasa baki je ba,

Ta soma inda inda cikin fargaba, dama.. dama anti uwani ce ta hanamin xuwa yau.

'akan wane dalili?
'ta bani kayanta ne na wanke bayan na shirya xanje makaranta, na roqi ta bari har na dawo na wanke shine taqi, makarantar ma tace baxan je ba.

'kira min uwani, banan ta tsorata ta xaro idanu,

'Anty jiddah kiyi haquri, xata ce nakawo karar tane gunki dukana xatayi.

Jiddah bata kula ta ba, ta daga murya tana kiran uwani kusan sau biyu kafin ta amsa,

Ta fito da sauri harda wani russunawa,
'Anty jiddah naji kina kirana,

'akan wane dalili xaki hana banan xuwa makaranta?

'aiki na sakata anty jiddah taqi tayi saboda ta raina ni.

'wannan ba hujja bace uwani, ban taba gayamiki kowacece banan bane, marainiya ce bata da iyaye, kakarta ta kawo amanar ta tayi aiki a gidan nan, kuma kina gani lokaci lokaci tana xuwa duba ta, kasancewar ta marainiya yasa na saka ta makaranta domin ta sami ilimi da xatayi alfahari dashi watarana, ina son maraya kuma bana so naga an takura maraya duk mai yin haka baxan xauna inuwa daya da shi ba, ba banan kadai ba duk masu aikin gidannan, babba da yaro har tsofaffin ina lura dake ba wanda kike ragawa, duk cikin su ba wanda ke qarqashinki ko kike ciyarwa game da takurasu da kikeyi kada ki sake, kuma daga yau kada ki sake baiwa banan wankin kayanki, akwai washing machine idan baxakiyi da kanki ba kibari.

Uwani ta hadiye wasu yawu da kyar yayin da wani qololon baqin ciki ya taso ya tokare xuciyarta, baa taba wulaqanta ta ba kamar yau kuma wai agaban shegiyar nan banan, idan ta xamo matar gidan ta hana mata iko dasu, wlhy ta ja masu, amma tunowa da tayi ita ke nema yasa ta qara russunawa hade da kwantar da muryarta,

'Allah ya huci xuciyarki anty jiddah insha Allah xan kiyaye, ta juya tana kallon banan kamar da gaske, banan kiyi haquri nima ina son maraya a xuciya na.

Jiddah ta dube ta tana fadin, xo ki cigaba da gyaramin salad din kafin abokan wasar naki su dawo,

Banan ta xauna cikin farin ciki, uwani kuwa ji take kamar ta shaqe ta ta huta, ta qara matsawa kadan yanda banan baxata ji taba.

'Anty tunda kika dawo nake xuba kunnuwa naji mesu hajiya suka ce game da mgnr amma kinyi shiru shiyasa har na kasa jurewa nake tambayar ki a yanxu.

Kallonta jiddah keyi cike da mamaki,

'Na tambayeki uwani, ta gyada kai tana kallonta.

'ki gayamin tun yaushe kika fara son el'mustapha,

'wlhy anty na fara sonsa tun ranar dana fara ganinsa, sonsa nake tsakani da Allah da xuciya daya ba dan na cutar dashi ba ko na cutar dake anty kinsani kuma nasan ke baxaki cutar dani ba kasancewar yar'uwa a gareni dan 'Allah ki taimakamin anty.

'taya xan taimakamiki bayan iyayen mu basu amince ba, Yusuf suke so ki aura ba el'mustapha ba.

'ashe har wadanda suka haifeka xasu iya Ma baqinciki a rayuwa? Ta fada a xuciyar ta batare da ta furta a fili ba.

'bayan wannan, ashe xaki iya xaman kishi dani, xaki iya auren mijina ina raye bawai mutuwa nayi ba, meyasa kike son mijina uwani, meyasa kike son rusa min farin cikina, kinsani da xuciya daya nake sonki, xaman ki da Yusuf xai fiye maki farin ciki akan auren ki da el'mustapha domin baya sonki kuma baxai taba qaunar kiba.

Uwani ta soma kuka haiqan, dan Allah kibar mgnr iyayen mu ko bada su ba xan iya aure, a yanxu ke kike riqo na kuma xaki iya auraddani, batun cutarwa kinsani baxan iya cutar dake ba nima da xuciya daya nake son ki, ni nasan yanda xanyi el'mustapha ya soni koda kwatar son da yake miki ne anty jiddah, kuma baxan taba jin haushin soyayyar da yake maki tunda na riga na jima da sanin ta tun kafin na aure sa, dan Allah ki aura min el'mustapha anti jiddah, 'shine farin cikina, shine rayuwata, ki ceci rayuwata xan iya mutuwa a kowane lokaci idan ban same sa ba, banyi niyar gaya maki ba saboda kada hankalinki ya tashi tun jiya da dare nake fuskantar wani irin tari dake sani xubar jini xuciyata tana min nauyi da kyar Ma nake numfashi.

Sosai hankalin jiddah ya tashi, ita dai a rayuwarta tana da tausayi da kawaici da hakan uwani kecin galaba akanta.

Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, dama likita yace kin kamu da ciwon xuciya, shine har kin fara aman jini, subhanallah meyasa uwani kike son rasa rayuwarki saboda abinda baki da iko akai, idan ni na amince ki auri el'mustapha shi kuna yaqi ya xakayi.

'Anty ke xaki sa ya amince, nidai ko shekara daya ne ya aureni dai dai lokacin xuciyata ta sami sauqi sosai akansa, wlhy anti na amince nayi auren shekara daya dashi kice ya sakeni baxan damu ba.

'mutumin da kike so kamar ki mutu har kina son a rabaki dashi auren shekara daya kacal uwani ina son da kika ce kina masa.

Uwani ta daburce ta soma inda.. Inda.. anty ko auren kwana biyu ne ina so ko ba komai burina ya cika na xama matar wanda nake so a rayuwata, wlhy baxan tabbata da mijinki ba kibani shi na shekara guda xan bar mikishi na nesan ta kaina dashi, ina so na sami sauqin ciwon xuciyata na warke daga cutar da ta kamani.

Jiddah taja numfashi, tana maimaita mgnr auren shekara daya uwani, idan kika aure sa bayan shekara daya mutane sukaji ya sake sa so kike a xargeni? Idan hakane ki haqura dashi.... Kafin ta qarasa uwani ta duqe gurin hade da dafe qirjinta tana Jan numfashi sosai tana daukewa, ta kakkafe idanuwanta kamar da gaske mutuwa xatayi wanda yayi matuqar ruda jiddah harda banan Ma dake saurarensu,

Jiddah ta soma jijjigata tana kiran sunan ta da qarfi wanda ya janyo hankalin mutanen gidan gare su harda securities din Ma,

Duk aka kewaye su tuni jikin jiddah ya fara rawa ta soma kuka sosai, banan taxo da ruwa ta kwarara mata, ta sauke wani numfashi da kyar tana fadin,

Wayyo qirjina, ku taimakeni mutuwa xanyi, anti jiddah xan mutu, wayyo anti jiddah.

Wani dan sanda a gurin yace, hajiya bari aje da ita asibiti xaifi tunda qirjin nata yana ciwo haka.

Jiddah ta share hawayen ta tana fadin to shikenan, ku kamata ku saka ta a mota kuje, duk abinda aka nema kai sai kayi ni baxan je ba.

Tana tsaye gurin aka fita da ita, ta tausayawa halin da uwani take ciki ciwon so bala'i ne hardai mai tare da ciwon qirji, allah ka baiwa yarinyar nan lafiya ka sassauta mata wannan ciwon, tasan ba laifin uwani bane na son mijinta, laifin sone da baya tunani sai dai kaji sa farat lokaci daya, idan har cutar uwani xata warke na tsawon shekara daya ta amince da auren ta da el'mustapha na tsawon shekara daya tare da yarjejeniya.

El'mustapha tare suka dawo da su arham yaje ya daukosu inda mama, rungume ya'yan tayi tana farin ciki, suma haka ne a gurin su sunyi missing mamin tasu sai faman surutu suke xuba mata.

'Angon jibi kaxo mu fara tattauna kan maganar mu fa,

Kallonta yayi yana xare safar qafafunsa,

'Uwargidan el'mustapha me kike so mu tattauna akai, idan nabila ta amince nima na amince dama xan dauki Hutu kuwa yanda xan angwance da kyau.

Murmushi jiddah tayi cikin qarfin hali tare da danne kishinta.

Tace Uwani bata da lafiya anje da ita asibiti, yanxu ta kai uwani har aman jini take yi, abinda uwani keso ina da iko akansa kuma ina son na inganta rayuwarta, ka taimakeni el'mustapha kada ka bani kunya,

'ina jinki jiddatulmusty kome kike so xaayi, me uwani ke so kudi ko me?

Kai... Kai.. take so el'mustapha, auren shekara daya ne, akwai yarjejeniya akai ku...... tayi shiru sakamakon wani kallo da el'mustapha ya jefe ta dashi sai da tayi suman xaune.


Pherty........ ✍🏻

El'mustapha Where stories live. Discover now