35

3.9K 369 72
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


35

Uwani ta shigo falon tana tauna cingam, yanayin fuskar el'mustapha yasa ta shiga taitayinta, ta tattaro nutsuwarta guri daya ta xauna tana gaida su.

Kallonta el'mustapha keyi da idanunsa da suka rikide, observing yake akan ta, yana son sanin wani abu a tare da ita,

Muryar ibrahim taji yana fadin, Jiddah bata sanar dake inda xata je ba kafin ta fita.

Uwani ta yatsina fuska tana kallonsa, idan xata fita bata gayamin ai, nima bana gaya mata kowa yana rayuwarshi ne shi kadai.

'Wannan rayuwar bata yi ba Sam uwani, cewar ibrahim yana kallonta fuskarsa ba walwala, keda bakinki kike fadar baki damu da rayuwar jiddah ba? Ke wace irin mace ce mai manta alheri? Ki tuna jiddah ta taimakeki ta tallafi rayuwarki, abinda take matuqar so fiye da komai a duniyar nan ta sadaukar maki uwani, ba kowace mace xata iya abinda jiddah tayi akan ki ba, tana xaune dake da xuciya daya ne, tana sonki tana son kyautata maki tana so ku xauna xama na amana ku hade kanku domin farin cikin mijinku, duk wanda yasan jiddah yasan mutuniyar kirkice bata da keta a rayuwarta ko niyar cutar da wani, kiji wata magana da kike fada yanxu ba dadin ji wai ba wanda ya damu da rayuwar wani kowa yana tasa rayuwar nan, na tabbata da jiddah ce baxakiji wannan kalma a bakin ta ba.

Jikin uwani yayi sanyi, tabbas gaskiya yake gayamata akan jiddah, sai tayi qoqarin fooling dinsu kada su xargi wani abu a tare da ita.

Nagode da nasihar da kake min a ynxu kuma insha Allah xan gyara, bari Ma naje na bata haquri.

Ibrahim ya qara tsaidata, kina nufin wai bakisan abinda ake ciki bane game da batan jiddah.

Kallonsa take baki a bude,

Wlhy ban sani ba, ina taje ne.

Banan da el'mustapha sai kallonta suke, kwata kwata banan bata xargin uwani akan batan jiddah ba kamar yanda el'mustapha ya kafe ta da idanuwa yana observing wasu abubuwa.

Yau na shiga uku, baa ga anti jiddah ba, ina taje da wannan cikin me ya same ta, sai ta soma hawaye.

Banan ma ta soma sharar kwallah,

Abinda uwani taji el'mustapha ya furta ne yayi kusan sumar da ita daga inda take xaune,

Jiddah ta gayamin kece kika kirata a waya ta fita, ina kika kai min matata ta?

Ni? Uwani ta tambaya tana fiddo idanuwa saboda tsananin tsoro da rudewa,

Wlhy ban kira ta, bana waya da jiddah, saboda me xan kirata ta fito?

Jiddah xata min qarya kenan ya qara tambayar ta bayan ya kafe ta da manyan idanuwansa yana son ya gasgasta xargin sa akanta.

Uwani ta qara rudewa ta fashe da kuka wanda ke nuna a tsorace take, amma tunani take har yaushe jiddah ta kira el'mustapha ta gayamasa, kodai so yake ya nuna mata halin su na yan sanda ya gani tunda haka suke bincike mai tsanani akan wanda suke xargi.

Wlhy bani na kirata ba, kowa yasani bana waya da jiddah, ban ma san sanda ta fita daga gidan ba ina daki a kwance, wlhy bani bace ban san komai a kai ba.

El'mustapha ya qara kallonta, Uwani idan nagane da sa hannunki a batan jiddah........ sai kuma yayi shiru ya barwa kansa sani, ya cigaba da fadin ke nake xargi kuma har yanxu xuciyata ke take xargi, xan iya shigar da qara kotu akan ina xargin ki da batan matata saboda nasan ba kyason jiddah baki da buri a duniya na ganin kin kawar da jiddah saboda ki mallaki xuciyar el'mustapha, kinsan nasan bakya qaunar jiddah itace din dai bata gano hakan ba, itace ta rasa gano illar uwani a tare da ita, ta dauki so da amana ta baki wanda ke baki da wani buri na ganin kin cutar da jiddah,

El'mustapha Where stories live. Discover now