42

5.1K 368 70
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_kina matuqar son El'mustapha, Pherty Ma tana son ki, Nagode da kulawa Mamman 4H tare da Ramlah Sokoto_❤

_Nafee Haixa Allah ya qaro lfy mai amfani_



42


Kuka suke babu mai rarrashin wani acikin su,

Da kyar jiddah ta dago tana kallonsa da jajjayen idanuwanta,

Ka saki Uwani, I mean ka fitar da ita daga prison...

El'mustapha ya dago da kyar yana mata kallon mamaki,

Ke wace irin mutum ce jiddah wace irin xuciya ce tare dake, don't you know that yarinyar nan ta nakasa ki, kin manta abinda tayi maki ne.

Nasani el'mustapha, Allah gafurun rahim ne, muka yi masa laifi muka roqesa ya yafe ballantana mu d'an Adam? 'Wannan abin da ya sameni yana cikin qaddarar rayuwata Allah ya rubuto uwani ce sila, ni na ya.... Shut up please ya katse ta cikin tsawa bayan ya tashi daga jikinta, ransa yayi matuqar baci, ta bude idanu sosai tana kallonsa, el'mustapha is shouting on her today, ta lumshe idanuwanta a hankali wasu hawaye suka soma xarya a fuskarta.

Idan kina tunanin rayuwarki bata da muhummanci a gurina tana da, haqqina ne na kare lafiyar ki kuma na hukunta duk wanda ya cutar dake, Uwani deserve to be in prison, in taqaice maki sai nayi Shari'a da uwani, look at you jiddah, just look at your leg har kike cewa abarta, something is wrong with you, you are so silly kada ki qara min wannan maganar, ya juya xai fice a fusacce.

Idan kayi fushi ka tafi ka barni Dame kake so naxo na rarrashe ka el'mustapha? Should I be waiting har lokacin da xaka huce ka dawo gare ni, ta fada tana kallon bayansa idanunta cike da hawaye.

Cak ya tsaya tare da juyowa da sauri yana kallonta cikin faduwar gaba, ya tuna yanxu fa ba irin da bane da xaiyi fushi ta bisa tana bashi haquri, suna hada ido jikinsa yayi matuqar sanyi, ya tako da sassarfa ya iso gareta, ya tsaya kyam a gabanta har lokacin xuciyarsa bata huce ba, jiddah ta fiye abin haushi da takaici taya xata ce wai a yafewa uwani kenan taci riba akan abinda tayi.

Ta dago a hankali tana kallonsa, kwarjininsa da kyawunsa ke qara wutar soyayyarsa a xuciyarta.

Ta soma share hawayenta a hankali da bayan tafin hannunta,

Kayi haquri El'mustapha, ya xauna batare da yayi magana ba, ta kwantar da kanta a kafadunsa batare da tayi magana ba.

Shiru har na tsawon wani lokaci banda sauke numfashi ba abinda ke tashi a dakin, ta dago a hankali tana kallonsa har lokacin bai saki fuskar saba,

Tasa hannuwanta ta juyo da fuskarsa tana kallonsa ido cikin ido,

Please El'mustapha, kayi haquri ka saki fuskar, jiddah baxata jure wannan fushin ba.

Ya sauke numfashi a hankali yana kallonta,

Xan hukunta uwani jiddah, xan sa acire mata qafar gabaki daya.

Da xaka bi yanda nake so da ka barta, daukar fansa ba naka bane, Allah yana gani kuma ya sani shi kadai yasan abinda ya tsara tsakanina da uwani, shi kadai yasan abinda yake shirin yi game da ita, bana so ka xama sanadi kamar yanda ta xama sanadi a qafana, ka fitar da ita daga prison ka barta taje duk inda xataje duniya xata gyara ta, kasan baxata xauna gidan mu ba kuma su hajiya baxa su karbeta ba, ina da tabbacin yan'uwanta Ma ba wanda xai xauna da ita saboda bata girmama su, allow her to go, duk inda xataje ita tasani.

El'mustapha Where stories live. Discover now