25

4.1K 314 12
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

25

Zuru tayi tana kallon farar takardar, har lokacin jikinta rawa yake, kafin ta fara kuka.

Shikenan ta faru ta qare dama tasan el'mustapha baxai so ta ba, ya karbi auren ne domin ya wulaqantata, ai kuwa kansa yayi mawa saboda takardar jiddah xata bawa ita acewar ta tace, dan wlhy bai isa ya sakeni a farkon daren aure na ba.

Ta dauki takardar da sauri ta sakata cikin wardrobe din ta, baxan nuna masa na karanta takardar ba dan Ma karnaga sakin, jiddah xan bamawa ko saki nawa ne ya xamto itace yayi Ma bani ba, sai inga yanda xaiyi Allah yasa saki uku ne aciki ta tafi ta barmin shi har abada inga qarshen soyayya, ingani idan baxasu iya rayuwa ba kamar yanda suke fada.

Da wannan tunanin uwani ta kwanta barci, mafarkinta a ranar duk cike yake da el'mustapha, gani kawai take suna ta xuba soyayya ita dashi.

Jiddah kuwa a ranar ta kasa barci, tayi kuka harta gode Allah, once in life el'mustapha din ta kwance da wata macen ba ita ba, tunani iri iri, ganin bata da mafita ya sakata shiga toilet ta dauro alwallah taxo ta fara sallah.

El'mustapha kuwa bashi da damuwa illah ta kewar jiddah sa, rigar barcinta ya sakawa pillow ya rungume, barcinsa yake hankalinsa a kwance batare da tunanin komai ba.

'Washe gari jiddah ce a kitchen tare da banan suna hada breakfast suna hira abinsu.

'Anty kinga har yanxu kaka bata xo dubiya ta ba, ta dade sosai wannan karon kuma ina so na ganta.

'kibari idan kukayi hutu bata xo ba sai kije, ai ba abin damuwa bane banan, meyiwuwa wasu hidimomi suka yi mata yawa.

'hakane anty, amma a makaranta an fara mana maganar kudin waec da neco.

'eyyeh ashe Banan an xama yan mata, na manta ai wannan shekarar kike gamawa,  kice su arham sun kai ga babbar anti.

Murmushi banan tayi tana kallonta,
'Anty ai xaki sakani University nima kamar anti uwani.

Me xai hana banan, inaso kiyi karatu, kinga ni banyi ba iyakar secondary ne kawai dani, kuma bayan nayi aure banyi qoqarin shiga ba kasancewar el'mustapha baya so, Uwani kuma kinga saboda bata da aure ne har kika ga ta cigaba kuma yanxu xata cigaba tunda kinga tana kai ya aure ta, dan haka kema ina so kiyi karatu koda kin sami mijin aure ki cigaba, ilimi yana da matuqar muhimmanci ga 'ya mace, ina so watarana kaka tayi alfahari da bokon ki.

Banan tayi dariya tana kallon jiddah cikin tsananin qaunarta,

'Anty jiddah rayuwarki daban ce, halinki mai kyau ne kuma kina da kirki, shiyasa nake matuqar sonki, mutanen gidannan Ma basu da magana sai ta alherin ki, baxan iya cutar dake ko cutar da jinin ki ba shiyasa kika ga ina matuqar qaunar yan biyu saboda mamansu bata kyamace ni ta soni da xuciya daya.

Jiddah ta wanke hannuwanta a sink, kafin ta juyo tana kallon Banan,

Nagode da kulawar ki sosai akan twins, Allah xai saka miki, taimaka ki kwashe kayan ki jera a dining, ni xanje wanka.

Cikin shirinsa na uniform ya fito, suna hada ido da jiddah ya sakar mata murmushi,

'Uwargidan el'mustapha, amaryar el'mustapha, mata kadai a xuciyar el'mustapha da fatar kin tashi cikin qoshin lafiya,

Murmushi tayi tana kallonsa,
'Good morning my cwt, angon uwani.

Bai wara mgn ba ya qarasa dining yana duba abubuwan da ta hada masa,

El'mustapha Where stories live. Discover now