11

5.7K 538 20
                                    

*EL_MUSTAPHA*


HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(home of experts and perfect writers)

Fertymerh Xarah 💞

11

'Washe garin ranar ga baki daya yinin ranar uwani bata fito ko falo ba tana can qunshe acikin daki.

Ganin shirun yayi yawa ne yasanya jidda xuwa ta dubata,

Kallo daya tayi wa uwani sai da hankalinta ya tashi, jikinta ya dauki rawa ta qarasa kusa da ita fuskarta dauke da mamaki take kallonta.

'meke damun ki uwani, meya same ki haka, idanunki sukayi jawur suka kumbura,

Uwani tayi qoqarin boye hawayen ta amma ina kamar kada ta tambayeta sai hawayen suka fara xarya, kukan me takeyi idan ba kukan so ba, rungumar da elmustapha yayi wa jidda jiya ba qaramin tarwatsa xuciyarta yayi ba, amma taya xata iya gayawa jidda saboda mijinta ne?

Ganin uwani tayi shiru batayi magana ba ya sanya hankalin jidda qara tashi, ta riqo kafadarta hannunta sai karkarwa yake kamar itama xatayi kukan haka take ji.

Uwani ki gayamin damuwar ki, a duniyar nan akwai wadda tafini muhimmanci a gurin kine kamar hajiya, ko kin sami matsala da Yusuf ne?

Uwani ta girgixa kanta cike da quncin jin ta ambaci wani Yusuf,

'ko matsala kika samu a makaranta? Nan ma ta girgixa kanta,

'to menene uwani, kiyi magana, ke ba arham bace da xan xauna rarrashin ki tun daxu jin matsalar ki, atleast ko menene ya kamata ki fara sanar dani kafin kixo kina kuka anan, kinga yanda idanunki sukayi kuwa?

'ba komai anty jidda, xaxxabi ke damuna kuma bayan wannan sai na tsinci kaina bana jin dadin rayuwata, I just feel like to cry.

'shine kuma baxaki gayamin ba, idan wani abu ya same ki am to hold responsible, dan Allah kidaina min haka bana so, idan abu na damunki let me know da wuri, kinsha magani ne?

'yanxu na sha,
'Abinci fa?
'A'ah
'bari na kawo maki ko tea ne kisha, ta tashi ta fita uwani ta bita da kallo tana jin wata qaunar sister din ta yanda take nuna damuwa akanta koda yaushe, amma ya xatayi da soyayyar mijinta da ta kanainaye xuciyarta, wannan abin kunyane a gurinta duk lokacin da jidda ta kamata dumu dumu cikin soyayyar mijinta, ta hada kanta da gwiwarta hade da sakin wani kuka mai narkar da xuciya.

Asalin labarin.......

Hajiya Zubaida itace mahaifiyar jidda, macece mai haquri da tawakkali, tana da riqon amana da rashin son abin duniya, Jiddah kadai ce ta mallaka tun bayan rasuwar mijinta,

Hajiya zubaida aminiya ce ga hajiya maimuna, xama suke na amana irin wanda yayi qaranci a wannan xamanin namu, xama suke batare da hassadar juna ba.

Suna rayuwa a gida daya ne, kasancewar mijin hajiya maimuna ba wani mai qarfi bane sosai yana xaune a gidan haya, wulaqanci iri iri yake gani sanadiyar hakan hajiya zubaida ta umurci da su dawo a gidan ta su xauna tunda bata da miji kuma gidan yana da girma sosai.

Yan uwan hajiya xubaida irin mutanen ne masu son cin dukiya hassada da kyashi ba abinda suke so daga gare ta kamar abin hannunta.

Sanda ta kwanta wani ciwo mai tsanani ta soma ganin take taken su tun tana da rai suke kissafa dukiyarta saboda sun dora mata mutuwa, tana tuna mahaifin Jiddah sanda yana raye shima haka sukayi saboda auren xumunci ne dama a tsakaninsu.

Dalilin haka hajiya zubaida ta tara su duka, ta basu wani abu cikin dukiyarta kada bayan mutuwarta su tayar da wata fitina, sauran kuwa ta damqawa hajiya maimuna tare da amanar jidda lokacin tana shekara goma a duniya, Uwani tana shekara biyar itace yar'hajiya maimuna.

Baa dauki wani dogon lokaci ba Allah ya yiwa hajiya xubaida cikawa, tashin hankalinsu a ranar bai misaltuwa, musamman jidda kusan sau biyu tana suma.

Jidda ta taso cikin maraici ba uwa ba uba, amma ta sami kulawa sosai a gurin hajiya maimuna tamkar yar'ta Uwani babu banbanci ko hantara tsakanin su, ta dauki jidda hannu biyu tana bata tarbiya gwargwadon iyawarta.

Ta hada kan ya'yanta, abu mai kyau da marar kyau duk tana nuna masu kuma tare da illar sa, duka family suna son junansu musamman jidda da bata da hayaniya, tana da sanyin hali da kauda ido akan komai, gata da girmama iyayenta sabanin uwani da ita a rayuwarta tana son ta ganta da manyan qawaye masu kudi, komai dai ayi qarya, kun dai gane😀

Sannu sannu har jidda ta kammala secondary School din ta, a lokacin ta hadu da elmustapha hajiya ta aike ta banki.

Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da alama abu take nema tana tafe tana dubawa,

dai dai lokacin ya fito daga cikin bank din, sanye da baqaqen suit, hannuwansa wayar sa yana tafe shima yana latsa ta cikin sauri da alama wani yake son kira...

Kicibis sukayi karo da juna, wayar dake hannunsa ta subulce ta fadi qasa, ya daqo a fusacce ya dora idanuwansa akanta dai dai lokacin da ta sunkuya domin dauko masa waya.

Tun da taga wayar ta tarwatse hankalinta ya tashi, jikinta ya dauki rawa ta kasa daqowa illah hada kai da tayi da gwiwarta ta soma kuka cikin tashin hankali, abinda bata tabayi ba, yau tayi wa wani hasarar abu mai muhimmanci a garesa.

Turus yaja ya tsaya yana kallonta har lokacin baiga fuskarta ba, sai dai fuskarsa da xuciyarsa cike suke da tsananin mamakin yarinyar dake tsugunne a gabansa......

Vote me on wattpad phertymerh1

El'mustapha Where stories live. Discover now