58

5.1K 397 66
                                    

'Ko da ya gama cin abincin jiddah bata dakin tana falon ta, da alama har yanxu bata sauko daga fushin ba.

Shi yanxu damuwar sa hannunsa dake masa zugi tun daxu.

Da dare sai juyi yake akan gado ya kasa barci saboda xafin ciwon hannun, gashi ya kumbura, kallon jiddah yake barcin ta take cikin kwanciyar hankali.

Time ya duba, biyu na dare ya gota, ya sauko daga saman gadon ya fita daga dakin.

Sai safa da marwa yake tsakanin falon sa dana jiddah, yanda yake ji a hannunsa ya tilasta masa xuwa dakin da abba yake ba shiri.

A hankali yake buga qofar dakin,

'Abba ya tashi yana tambayar waye? Jin muryar el'mustapha ya taso da sauri ya bude dakin yana tambayar lafiya?

'Na kasa barci, hannuna ke ciwo sosai... El'mustapha ya fada yana nunawa abba hannun.

'Abba ya duba hannun yana fadin ai gocewar qashi ne el'mustapha me ya jima ka ciwo haka.

Ya yatsina fuska kafin yace na dan xame ne daxu a toilet na fadi, yanxu ya xanyi abba.

Daurewa xaka yi kayi haquri har xuwa gobe sai kaje asibiti ko kuma ayi maka aikin gida duk wanda kake so amma ni bani da sani akan irin wannan matsalar.

Shiru el'mustapha yayi kafin ya juya yana fadin Allah ya kaimu goben.

Xama yayi bakin gadon ya dafe kansa da hannunsa daya, dole ya sami gocewar hannu saboda girma da nauyin kujerar, inda ta sami uwani a kai kenan xaa sami matsala ba babba dan ya tabbata kwakwalwar ta gabaki daya xata juye.

Jiddah ta bude ido tana kallonsa, kallon agogon tayi kafin ta maida kallonta garesa cikin mamaki, meke damun el'mustapha, me ya hana masa barci a wannan lokacin yake xaune?

Ta matso a hankali xuwa inda yake, hannunta ta kai wuyansa ta taba tunanin ta ko xaxxabi ne,

Ya dago yana kallonta, ita ma shi take kallo
Tace meke damun ka?

Da kyar yace ba komai.
'amma naji jikinka da xafi ko baka da lafiya ne?

Ya girgixa kansa kafin yace ki kwanta jiddah ba abinda ke damuna.

Ta gyara xamanta sosai tana kallonsa,

'Na kwanta nayi barci kai kuma kana xaune, idan lafiyar ka qalau tunanin me kake yi el'mustapha?

Yayi shiru baiyi magana ba, ganin ta matsa da tambaya ya nuna mata hannun.

Tayi shiru gabanta na faduwa tana kallon yanda hannun ya kumbura, ta kasa daqowa ta kalle sa harda wani nauyin sa take ji.

Yaja numfashi kadan yana fadin kije ki kwanta tun kafin airah ta tashi gobe kixo kina complaining baki sami barci ba,

Ta girgixa kanta kafin tace kayi haquri n..... Shishsssss ya katseta ta hanyar dora yatsanta akan labbanta yana kallonta.

Kije ki kwanta bana son gardama,

Ta matsa kadan daga garesa amma taqi kwanciya, bata da wannan nutsuwar bata san yanda yake ji ba ta tabbata duk abinda xai hanawa el'mustapha barci ba qaramin abu bane.

Ganin taqi ta kwanta ya saka shi kwanciya yana fadin xo mu kwanta jiddah nima barci nake ji.

Ta matsa ta shiga cikin jikinsa, ya rungumeta yana lumshe idanuwansa ba dan ya daina jin xafin hannun ba.

'Washe gari ko da jiddah ta tashi el'mustapha baya gidan, tayi mamakin ina xaije da sassafe haka kuma tana da tabbacin ko wanka bai yi ba ya fita.

El'mustapha Where stories live. Discover now